Editor

9513 Posts
Ƙungiyar matasan APC ta yaba wa Adamu bisa nasarar shirya ingantaccen zaɓen fidda gwani

Ƙungiyar matasan APC ta yaba wa Adamu bisa nasarar shirya ingantaccen zaɓen fidda gwani

*Ta yi watsi da barazana gare shi ‘Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Gamayyar Ƙungiyoyin Cigaban Matasa a Nijeriya da ’yan ƙasashen waje (COPY-ND), ta yi watsi da duk wasu zarge-zargen barazana da ake yi wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, kan tsarin da ya dace wanda a ƙarshe ya samar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, cikin kyakkyawar nasara. A cikin wata sanarwa da babban daraktan ƙungiyar ta COPY-ND, Dakta Aminu Abdullahi Isyaku ya fitar, ya ce, nasarar da kuma sakamakon taron na musamman da aka kammala kwanan nan, wata hujja ce da Sanata…
Read More
EFCC ta kama mutane 19 da ake zargi da damfara ta intanet a Kogi

EFCC ta kama mutane 19 da ake zargi da damfara ta intanet a Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Hukum Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa EFCC, shiyyar Ilorin ta kama wasu mutane 19 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da ta kai a Lokoja, jihar Kogi. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin hukumar Wilson Uwujaren, kuma aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Ilorin. Ya ce jami’an hukumar EFCC masu sa ido ne suka fito da waɗanda ake zargin daga maɓoyarsu a ƙarshen mako, biyo bayan samun sahihin bayanan sirrin da suka yi na…
Read More
Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa – IPMAN

Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa – IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta ɗora alhakin ƙarancin dakon man fetur da ake samu daga defo na Legas a dalilin da ya haifar da wahalar man da ake fuskanta a Abuja da sauran sassan ƙasar. Shugaban ƙungiyar ta IPMAN, Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Litinin a Legas. Okoronkwo ya yi magana kan yadda layukan mai ke sake dawowa a wasu sassan ƙasar nan, musamman a Abuja. Ya ce yaƙin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga…
Read More
Rahoton ƙarya da Adrian Zenz ya watsa ya tona asirin Amurka

Rahoton ƙarya da Adrian Zenz ya watsa ya tona asirin Amurka

Daga CMG HAUSA Wata doka mai suna wai hana tilastawa ‘yan Uygur aiki ta Amurka za ta fara aiki nan bada jimawa ba. Kwanan nan, Adrian Zenz, wanda ya sha kitsa ƙarairayi ya sake fitar da wani rahoton dake nuna cewa, wai ƙasar Sin na ƙara tilasta wa mutane aiki. Irin wannan doka tana cike da ƙarairayi, wadda ta tona asirin kasar Amurka, na kawar da Xinjiang daga cikin yankuna masu samar da kayayyaki ga duniya. Haƙiƙa, kafofin watsa labarai sun ruwaito maganganun tsoffin ‘yan diflomasiyyar Amurka a ƙasar Sin dake cewa, babu wata matsala a Xinjiang, dukkanmu mun sani,…
Read More
Ƙasar Sin ta nuna adawa da ƙudurin Majalisar Turai kan Xinjiang

Ƙasar Sin ta nuna adawa da ƙudurin Majalisar Turai kan Xinjiang

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun majalisar dokokin ƙasar Sin ya bayyana adawa da kakkausar murya kan wani sabon ƙuduri da majalisar Turai ta amince da shi, kan halin da ake ciki game da batun kare haƙƙin dan-Adam a jihar Xinjiang. Kakakin kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar Ƙasar Sin You Wenze ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana adawa da magudin siyasa da tsoma baki a harkokin cikin gidan ta da majalisar Turai ke yi, ta hanyar fakewa da batun kare haƙƙin bil-Adama Manufar yunƙurin da wasu makiya ƙasar Sin dake cikin majalisar dokokin Turai ke…
Read More
Sin: Kimiyya da fasaha sun taimakawa wajen bunƙasar kamfanoni da horas da ƙwararru

Sin: Kimiyya da fasaha sun taimakawa wajen bunƙasar kamfanoni da horas da ƙwararru

Daga CMG HAUSA A shekaru 10 da suka wuce, kamfanoni da sauran masu dandalin kasuwanci suna ta kara ƙarfin zuba jari a fannin kimiyya da fasaha, lamarin da ya taimaka wajen horas da dimbin ƙwararru. Alƙaluma sun nuna cewa, yanzu yawan kuɗin da kamfanoni suke zubawa a fannin nazari ya wuce kashi 76 bisa 100 na jimillar kuɗin da zamantakewar al’ummar ƙasar Sin suke zubawa. Kana gwamnatin tsakiyar ƙasar Sin ta fito da manufofi da matakai da dama don ƙarfafa gwiwar kamfanoni da su ƙara zuba kuɗi kan aikin nazari, a ƙoƙarin kyautata ƙwarewarsu ta fannin yin ƙirƙire-ƙirƙire. Yanzu haka…
Read More
Gwamnati ta ba da hutu don bikin Ranar Dimokuraɗiyya

Gwamnati ta ba da hutu don bikin Ranar Dimokuraɗiyya

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta bayyana Litinin, 13 ga Yunin 2022 a matsayin ranar hutun gama-gari don Bikin Ranar Dimokuraɗiyya. Sanarwar haka ta fito ne ta ofishin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola a ranar Alhamis a madadin Gwamnatin Tarayya. Aregbesola ya taya ‘yan Nijeriya murna game da bikin wannan rana, tare da yin kira ga ‘yan ƙasa da a ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen ganin ta inganta ayyukanta a fannoni daban-daban. Ya ce, “Yayin da muke bikin Ranar Dimokuraɗiyya, ya kamata mu waiwaya mu dubi ƙoƙarin magabatanmu sannan mu tabbatar da Najeriya ta ci gaba da…
Read More
Albashin alƙalai: Lauyoyi 54 sun kai ƙarar m’Majalisar Dokokin Nijeriya da wasu mutane

Albashin alƙalai: Lauyoyi 54 sun kai ƙarar m’Majalisar Dokokin Nijeriya da wasu mutane

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Cif Sebastien Tar, SAN, ya maka majalisar dokokin Nijeriya da wasu mutane uku a gaban kotun masana’antu ta ƙasa kan rashin albashin alƙalai. Tar, wanda ya shigar da ƙarar, a yayin da ake ci gaba da shari’ar a ranar Litinin a cikin tawagarsa, SAN 32 da ake magana da su a matsayin qwararren siliki da kuma 22 masu ba da shawara. SAN Awomolo ya jagoranci sauran SAN a cikin lamarin da aka shirya gabatar da shi a gaban mai Shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae. Sauran lauyoyin sun haɗa da Kanu Agabi, JB Daudu, EC Ukala, Emeka…
Read More
Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Jihar Nasarawa ta yaye ɗalibai 35,000, cewar Umar Idris

Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Jihar Nasarawa ta yaye ɗalibai 35,000, cewar Umar Idris

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Kimanin ɗalibai 35,000 ne cibiyar koyon sana’oi da dabarun aiki da aka fi sani da Vocational and Relevant Technology Board a Turance na gwamnatin Jihar Nasarawa da ke Lafiya babbar birnin jihar ta yaye kawo yanzu. Janar Manajan cibiyar, Dokta Idris Umar Idris ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilin mu dangane da harkokin cibiyar a ofishin sa dake cibiyar a Lafiya ranar Litinin, 6 ga Yuni, 2022. Ya ce cibiyar ta yaye ɗaliban ne daga fannonin karatun ta guda biyu a cibiyar wato fannin koyon sana’o'in da na…
Read More
Harin Abuja-Kaduna: ‘Yan uwa sun ƙaryata sako waɗanda aka yi garkuwa da su

Harin Abuja-Kaduna: ‘Yan uwa sun ƙaryata sako waɗanda aka yi garkuwa da su

Daga BASHIR ISAH ‘Yan uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun ƙaryata labarin cewa, an sako musu ‘yan uwa da ke hannun ‘yan bindiga. Sun ƙaryata labarin ne cikin wata sanarwa da suka fitar ta ƙungiyarsu ta “Relatives of AK9”, ƙarƙashin jagorancin Dokta Abdulfatai Jimoh da Dokta Ba’aba Muhammad. Sashen sanarwar ya ce, “Labarin sako waɗanda aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja-Kaduna wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ba gaskiya ba ne, jama’a su yi watsi da labarin.” Idan dai ba a manta ba, a ranar 28 ga Maris ɗin da…
Read More