12
Jun
Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano An bayyana cewa duk wani shugaba da zai zo nan gaba a Nijeriya koma na yanzu da ya ce zai inganta tsaro da tattalin arziƙi da duk wani cigaba ba tare da ya samar da wadataccen hasken wutar lantarki ba a Nijeriya to abu ne da ba zai yiwu ba kuma almara ce ko kuma yaudara. Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Ashiru Ali Muhammad Yammusa Gezawa, Shatiman Sardaunan Alagwado a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis ɗin makon jiya. Har wa yau, Yammusa Gezawa ya ƙara…
