Editor

9513 Posts
Ƙalubalen da ke tattare da yaƙi da talauci a Nijeriya – Rahoton Bankin Duniya

Ƙalubalen da ke tattare da yaƙi da talauci a Nijeriya – Rahoton Bankin Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI Rahoton sakamakon binciken da bankin Duniya ya yi, ya bayyana cewa, akwai wasu jerin dalilai da suke kawo cikas ga yaqi da talauci da Nijeriya take ƙoƙarin yi. Waɗannan dalilai sun haɗa da tasirin annobar cutar COVID-19, karayar tattali. Arzikin ƙasa, sanan da dar-dar da ake fama da shi game da yaƙin da yake faruwa tsakanin Rasha da Yukiren su ne abubuwan da suke neman kawo cikas ga yunƙurin kawar da talauci a Nijeriya. Wasu masana a harkar tatalin arziki a Bankin Duniya, Jonathan Lain da Jakob Engel su ne suka gabatar da wannan rahoto a…
Read More
CBN ya umarci bankuna su dinga cazar masu ajiya ladan tura kuɗi ta yanar gizo daga miliyan zuwa sama

CBN ya umarci bankuna su dinga cazar masu ajiya ladan tura kuɗi ta yanar gizo daga miliyan zuwa sama

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN ya umarci bankunan Nijeriya da su dinga amsar ladan tura kuɗin da suka kai miliyan guda zuwa sama daga masu ajiya. Amma wannan hukunci ga masu asusun ajiya ne na ɗaiɗaikun. Yayin da su kuma asusun haɗaka na kamfanoni, za su dinga biyan kuɗin ne idan an tura kuɗin da ya kai miliyan 10. CBN ta bayyana haka ne a wata takardar sanarwar da ya wallafa na yin bitar NIBSS a game da hada-hadar kuɗi a yanar gizo. Hakazalika, bankin na CBN ya ƙayyade adadin iyakacin kuɗin da aka yarda a tura.…
Read More
Yadda biloniya Elon Musk da Aliko Ɗangote suka yi asarar fiye da Naira tiriliyon 6.25 a kwana guda

Yadda biloniya Elon Musk da Aliko Ɗangote suka yi asarar fiye da Naira tiriliyon 6.25 a kwana guda

Daga AMINA YUSUF ALI Mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, da kuma wanda ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, sun yi asara mai yawa daga duniyoyinsu abinda ya kai jimillar abinda suka rasa, Naira tiriliyon 6.25 ( Dalar Amurka biliyan $14.91). Al'amarin ya afku ne a ranar Juma'ar makon jiya. Sai dai abin mamakin shi ne, duk da wannan mummunar asarar da suka tafka hakan bai hana su cigaba da riqe matsayinsu na mafi arziki a Duniya da kuma mafi arziki a Afirka ba. Musk ya tafka asarar ne sakamakon faɗuwa a hannun jarin…
Read More
Tsaro: Harkar na kawo ruɗani a Nijeriya

Tsaro: Harkar na kawo ruɗani a Nijeriya

Assalamu alaikum, edita. Da fatan muna lafiya. Harkar tsaro, wani rukuni ne daga cikin manyan rukunan gudanar da gwamnatin. Wanda hakan ya sa ake ware wa harkar maƙudan kuɗi don wanzar da zaman lafiya. Ko wace ƙasa da ta ke ikirarin cewa ta cika ƙasa, dole ne sai da samar da tsaron, domin kuwa idan babu zaman lafiya to babu gwamnati. To irin hakan, wasu ƙungiyoyi da suka ɗaukar wa kansu tada zaune tsaye, sannan da hadafin cewa suna yaqi ne don nema yancinsu, ya sa matsalar tsaro ya haɗa dangi da siyasa. Duk da cewa, babban abinda ke haifar…
Read More
Abinda ya sa hukuma ta garƙame dukkan sassan Bankin Zenith a Owerri

Abinda ya sa hukuma ta garƙame dukkan sassan Bankin Zenith a Owerri

Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotu ta umarci a garƙame dukkan rassan ɗaya daga cikin manyan Bankuna Nijeriya wato Bankin Zenith. Kuma ta nemi bankin da ya warware harƙallar Naira biliyan 1.9 da take zargin su da yi. A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai aka wayi gari da ganin wasu jami'an tsaro sun rufe tare da kange dukkan rassan Bankin Zenith da suke a garin Owerri a jihar Imo. Hakan ya biyo bayan umarnin kotu da ta nemi jami'an da su aikata hakan don ladabtarwa ga bankin. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan rufe bankin umarnin kotun masana'antu…
Read More
Tinubu ya goge raini da Osinbajo

Tinubu ya goge raini da Osinbajo

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Zaven fidda gwanin jam'iyyar APC mai gwamnatin tsakiya ta Nijeriya ya fi tsanani a siyasance tsakanin waɗanda a ke ganin 'yan gida ɗaya ne wato uban APC Bola Ahmed Tinubu wanda ya lashe zaɓen da kuma mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo wanda ɗan gidan Tinubun ne. Yanda Tinubu ya lashe zaɓen da tura Osinbajo a matsayi na uku ya sa tamkar ƙarfin da, da uban gida daban ne. Tun a kamfen ɗin neman zaɓe, Tinubu ya furta cewa babu ɗan sa da ya yi ƙarfin da zai iya takarar shugaban ƙasa. A filin taron wanda dandalin…
Read More
Yayin da Shugaba Buhari ke cika shekarar ƙarshe na wa’adin mulkinsa…

Yayin da Shugaba Buhari ke cika shekarar ƙarshe na wa’adin mulkinsa…

A ranar 29 ga Mayu, 2022, Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekaru bakwai daga cikin shekaru takwas da aka zaɓe shi a karo na biyu. A daidai wannan lokacin ne a shekara mai zuwa zai kammala wa'adin mulkin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da shi na tsawon wa'adi biyu ga duk wanda zai yi aiki a wannan matsayi na siyasa a Nijeriya. Bisa la'akari da wannan muhimmin cigaba, fadar shugaban ƙasa, a ranar 28 ga Mayu, 2022, ta fitar da takardar da ta kira ‘Takardar Gaskiya: Manyan Nasarorin da aka cimmawa kan Cika Shekaru Bakwai na Gwamnatin Buhari’.…
Read More
Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: ‘Yan bindiga sun sako mutum 11 da ke hannusu

Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: ‘Yan bindiga sun sako mutum 11 da ke hannusu

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun sako fasinjojin da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a lokutan baya. Hakan ya biyo bayan sasantawar da aka yi ne tsakanin Gwamnatin Tarayya da 'yan bindigar. Ɗan jarida na kusa Sheikh Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu ya bayyana cewa, mutum 11 da lamarin ya shafa ne 'yan bindigar suka sako su a ranar Asabar. Ya ce, an kwashi waɗanda aka sakon baki ɗayansu zuwa Abuja don duba lafiyarsu a bisa umarnin Shugan Ƙasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a haɗa su da 'yan uwansu. Mamu ya ƙara…
Read More
Ranar Dimokuraɗiyya: Kada ku maida lamarin zaɓen 2023 na ‘a-yi-rai-ko-a-mutu’, Buhari ga ‘yan siyasa

Ranar Dimokuraɗiyya: Kada ku maida lamarin zaɓen 2023 na ‘a-yi-rai-ko-a-mutu’, Buhari ga ‘yan siyasa

*Ya ba da tabbacin gudanar da sahihin zaɓe Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga 'yan Nijeriya, musamman kuma 'yan siyasa da cewa, a lura a kuma kiyaye kada a maida sha'anin zaɓen 2023 ya koma na a-yi-rai-ko-a-mutu. Buhari ya yi wannan kira ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa ranar Lahadi kan bikin ranar Dimokuraɗiyya ta 2022. Yayin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Nijeriya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe a 2023, inda talakawan ƙasa su zaɓi wanda suke ganin ya fi cancanta ya zama magajinsa. Don haka, ya hori 'yan…
Read More
Sojoji sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta zaman lafiya a Kudancin Kaduna

Sojoji sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta zaman lafiya a Kudancin Kaduna

Daga WAKILINMU Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Zonkwa Selected da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta zaman lafiya da rundunar kiyaye zaman lafiya 'Operation Safe Haven' ta shirya a Kudancin Kaduna. Ƙungiyar dai ta lashe gasar ce bayan ta lallasa takwararta ta Golden Balley da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a da ci 3-1 a wasan ƙarshe da aka buga a sabon filin wasa na garin Kafanchan a da ke Jihar Kaduna. Da ya ke jawabi bayan kammala gasar, Kwamandan Rundunar ta OPSH mai hedkwata a Jos, babban birnin Jihar Filato, Manjo Janar Ibrahim Sallau…
Read More