Editor

9513 Posts
ACF ta yi Allah-wadai da kisan kiyashi a Owo

ACF ta yi Allah-wadai da kisan kiyashi a Owo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar tuntuva ta Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Church Owo da ke Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin ɗabi'un dabbanci da mutane ke yi. A yayin da ya ke kokawa kan yadda masallatai a Arewa suka sha fama da irin waɗannan hare-hare a baya, babban sakataren ƙungiyar ACF, Murtala Aliyu, ya ce, hare-haren na da nufin sanya ’yan Nijeriya gaba da juna, tare da yin kira ga ’yan ƙasar da su haɗa…
Read More
Masu sayar da GSM na Zamfara sun tabbatar da sace mutanensu 30 da ‘yan bindiga suka yi

Masu sayar da GSM na Zamfara sun tabbatar da sace mutanensu 30 da ‘yan bindiga suka yi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinsu kimanin 30. Shugaban ƙungiyar, Comrade Kabir Garba Muktar ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Lahadi. A cewarsa, an yi garkuwa da mambobinsu ne a tsakanin Turata zuwa Lambar Bakura a hanyarsu ta komawa Gusau yayin da suka halarci bikin auren abokinsu a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato ranar Asabar. "‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinmu sama da 50 da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar…
Read More
Za mu kashe Naira biliyan biyu kan tantance ma’aikatan makarantu – UBEC

Za mu kashe Naira biliyan biyu kan tantance ma’aikatan makarantu – UBEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Makarantu a Matakin Farko (UBEC) ta ce, za ta kashe Naira biliyan biyu wajen tantance malaman makarantu a cikin kwana 10. Babban Sakataren Hukumar UBEC, Hamid Bobboyi, ya ce, an ware kuɗaɗen ne domin tantance ma’aikatan makarantun a faɗin Nijeriya a shekarar 2022 da muke ciki. Ya ce, hukumar za ta tantance makarantu a jihoi 17 na yankin Kudu da yankin Arewa mai jihohi 19 da kuma Birnin Tarayya, Abuja, daga ranar 4 zuwa 23 ga watan Yuli mai mkamawa. Bobboyi ya shaida wa taron tantance ma’aikata da ya gudana a Abuja, inda…
Read More
Rundunar ’yan sandan Katsina ta bai wa iyalan jami’anta tallafin kuɗi

Rundunar ’yan sandan Katsina ta bai wa iyalan jami’anta tallafin kuɗi

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina ta raba wa iyalai da magadan jami'anta da suka rasa rayukansu lokacin gudanar da ayyukansu cakin kuɗi na Naira Milyan 53 da dubu ɗari tara. Da ya ke miƙa cakin kuɗin ga iyalai da  magadan 'yan sandan su 25  a hedikwatar rundunar kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina Idris Dauda Dabban ya bayyana cewar bada cakin kuɗin wata Inshora ce da babban sufeto janar na 'yan sanda Alƙali Baba ya ƙirƙiro da shi don tallafawa iyalan jami'an da su ka rasu lokacin gudanar da aiyukansu. Ya ci gaba da cewa, an…
Read More
Ministan tsaron ƙasar Sin ya gabatar wa Amurka buƙatar Sin a fannoni 4

Ministan tsaron ƙasar Sin ya gabatar wa Amurka buƙatar Sin a fannoni 4

Daga CMG HAUSA Yau ne, ministan tsaron ƙasar Sin Wei Fenghe, ya gabatar da jawabi kan ra'ayin ƙasarsa, game da odar yankin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 19 da aka gudanar a ƙasar Singapore. Dangane da hulɗar da ke tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Amurka, ministan tsaron ƙasar Sin din ya ce, yanzu hulɗar da ke tsakanin ƙasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci. A ganin ƙasar Sin, kyakkyawar hulɗar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki ɗayan. A matsayinsu na muhimman ƙasashe 2 a duniya, ba za a iya raba…
Read More
Sin ta gudanar da ayyukan nazarin kayan tarihi fiye da 8800 a cikin shekaru 10 da suka gabata

Sin ta gudanar da ayyukan nazarin kayan tarihi fiye da 8800 a cikin shekaru 10 da suka gabata

Daga CMG HAUSA Ranar Asabar ta biyu ta watan Yuni na kowace shekara, rana ce ta kayayyakin al’adu da halittu da aka gada daga kaka da kakanni ta ƙasar Sin. A jiya ne, aka buɗe bikin ranar kayayyakin al’adu da halittu da aka gada daga kaka da kakanni ta ƙasar Sin ta shekarar 2022 a lardin Gansu, a yayin bikin buɗewar, hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin ta bayyana cewa, Sin ta gudanar da ayyukan nazarin kayan tarihi fiye da 8800 a cikin shekaru 10 da suka gabata. Taken ranar ta wannan shekara, shi ne tabbatar da tsaron…
Read More
Yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama a ƙasar Sin ya kai 33.1% bisa adadin dukkan sufuri a ƙasar

Yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama a ƙasar Sin ya kai 33.1% bisa adadin dukkan sufuri a ƙasar

Daga CMG HAUSA A cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu bunkasuwar sha’anin sufurin jiragen sama na ƙasar Sin sosai, yawan fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen sama ya kai kashi 33.1 cikin ɗari bisa adadin dukkan sufurin ƙasar. Sin ta daddale yarjejeniyoyin jigilar jiragen sama tare da ƙasashe da yankuna 128, da buɗe hanyoyin jiragen sama 895 a tsakaninta da ƙasashen waje. A cikin shekaru 10 da suka gabata, an gina sabbin filayen jiragen sama ko canja wurin filayen jiragen sama 82 a ƙasar Sin, a halin yanzu yawan filayen saman ƙasar Sin ya kai 250,…
Read More
Ranar dimokuraɗiyya: Buhari ya sha alwashin gudanar da ingantaccen zaɓen shugaban ƙasa a 2023

Ranar dimokuraɗiyya: Buhari ya sha alwashin gudanar da ingantaccen zaɓen shugaban ƙasa a 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, a yau Lahadi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, zai jajirce tare da ƙudurar aniyar ganin an zaɓi sabon shugaban ƙasa ta hanyar lumana da gaskiya. Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a faɗin ƙasar domin murnar zagayowar ranar dimokuraɗiyya ta bana domin karrama wanda ake kyautata zaton ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, Cif Moshood Kashimawo Abiola. Ya ce, a cikin shekaru bakwai da suka wuce, gwamnatin da ke kan mulki ta ba da jari sosai…
Read More
2023: INEC ta ba wa Atiku da Tinubu mako guda su fitar da mataimaka

2023: INEC ta ba wa Atiku da Tinubu mako guda su fitar da mataimaka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ba dukkan ’yan takarar Shugaban Ƙasa da na Gwamnoni daga jam’iyyu 18 wa’adin mako ɗaya su gabatar ma ta da sunan mataimakansu. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taronsa da Kwamishinonin hukumar na Jihohi. Hakan dai na nufin ɗan takarar PDP (Atiku Abubakar) da na APC (Bola Tinubu) da na NNPP, (Rabi’u Musa Kwankwaso) da sauran ’yan takarar dole su naɗa mataimakansu nan da mako zaya mai zuwa. A cewar Shugaban na INEC, yayin da…
Read More
Sarkin Kwatarkwashi Alhaji Ahmad Umar, Basarake mafi daɗewa a Zamfara ya rasu

Sarkin Kwatarkwashi Alhaji Ahmad Umar, Basarake mafi daɗewa a Zamfara ya rasu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sarkin gargajiya mafi daɗewa a Jihar Zamfara, Sarkin Kwatarkwashi, Alhaji Ahmad Umar, ya rasu Alhamis da ta gabata. A cewar sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Danisa, ga manema labarai cewa, sarkin ya rasu ne bayan gajeriwar jinya yana da shekaru 93 a duniya. Marigayi Alhaji Ahmad Umar ya kasance basaraken gargajiya mafi daɗewa kuma babba akan karagar mulki ba a Zamfara kaɗai ba, har ma a faɗin Nijeriya bakiɗaya, inda ya kwashe shekaru 61 a matsayin Sarkin Kwatarkwashi. Sarkin mai shekaru 93, an fara naɗa shi hakimin ƙauye a…
Read More