09
Jun
Daga FATUHU MUSTAFA A yanzu dai saura 'yan watanni suka rage a yi zaɓen shugaban ƙasa. Wanda zai zo a watan Fabrairu na shekarar baɗi. Tuni dai jam'iyya mai ci a Jihar Kano wato APC, ta tsayar da dan takararta, wato Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna. Inda kuma ake kyautata zaton babbar jam'iyyar adawa ta NNPP mai kayan daɗi za ta ƙara tsai da zakaran gwajin dafinta, wato Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida. A wannan nazari da na yi, ina son na kalli ƙalubalen dake gaban ɗan takarar jam'iyya mai ci, wato Nasiru…
