Editor

9513 Posts
Abinci shi ne tushen rayuwa

Abinci shi ne tushen rayuwa

Daga IBRAHIM YAYA MƊD da hukumomin ƙasa da ƙasa su kan fito da jerin tsare-tsare da manufofi, baya ga wasu ranaku da ake keɓewa a duk shekara, don nazartar irin nasarori da ma akasin haka da ɓangaren aikin samar da abinci a duniya ke fuskanta. Sai dai annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta haifar da illoli da sauran matsaloli ga ɓangaren samar da abinci a duniya, inda alkaluma ke nuna cewa, kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa. Sai dai yayin da wasu ƙasashe ke nuna halin ko’in kula kan wannan lamari,…
Read More
Ta yaya ‘yan siyasan Amurka za su yi ƙarin bayani kan ƙaryarsu kan Xinjiang?

Ta yaya ‘yan siyasan Amurka za su yi ƙarin bayani kan ƙaryarsu kan Xinjiang?

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, jawabin wata tsohuwar jakadar ƙasar Amurka a ƙasar Sin da kafofin yada labaru suka gabatar, ya sake sanya mutane sun ƙara sanin halayyar wasu Amurkawa. An ruwaito cewa, Sheila Carey, ƙaramar jakadar Amurka mai kula da tattalin arziki da siyasa a birnin Guangzhou da Andrew Chira, sun yi karin bayani kan maƙarƙashiyar Amurka kan batun Xinjiang a wata liyafa a asirce a shekarar 2021, a yunƙurin neman samun goyon bayan kamfanonin Amurka, inda suka ce, “Lallai ba matsala a jihar Xinjiang. Mun san haka, amma muna ƙara gishiri kan batun wai tilastawa a yi aiki…
Read More
Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari ya roƙi ‘yan jam’iyya su zama masu haɗin kai

Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari ya roƙi ‘yan jam’iyya su zama masu haɗin kai

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da jam'iyyar APC take cigaba da zaɓen fidda gwani na takarar shugabancin ƙasar nan, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan jam'iyya da kuma daliget. Inda ya roƙi 'yan Jam'iyyar APC da su kasance masu haɗin kai, su kuma daliget ya roƙe su a kan su tabbatar da sun zaɓo ɗan takara wanda zai ba wa jam'iyya dama ta kai bantenta a babban zaɓe. Muhammadu Buhari ya bayyana haka a jawabinsa a safiyar yau Laraba a Abuja, a yayin da zaɓen fidda gwani na 'yan takarar shugabancin ƙasar Nijeriya a jam'iyyar APC yake…
Read More
Gobara ta yi ajalin mutum 2 a Abia

Gobara ta yi ajalin mutum 2 a Abia

Daga BASHIR ISAH Mutum biyu aka ruwaito sun riga mu gidan gaskiya a safiyar Laraba sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan mai da ke kusa da Alaoji a hanyar Ikot-Ekpene, cikin ƙaramar hukumar Obingwa, Jihar Abia. Kwamandan Hukumar Kwana-kwana na Shiyyar Aba, Mr Belenta Belenta, ya tabbatar da faruwan hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba. Belenta ya ce, yana zargin waɗanda lamarin ya rutsa da su suna ƙoƙari satar mai ne wanda hakan ya yi sanadiyar zubewar fetur ɗin da ya yi sanadin ta da gobarar. Ya ci gaba da cewa, gobarar ta…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC

Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwamanan Jihar Legas kuma jigo a Jam'iyyar APC, Cif Asiwaju Bola Aahmed Tinubu, ya zama dan takarar da zai nemi shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar APC a babban zaben 2023.Tinubu ya taki wannan nasarar ce bayan kammala zaben fidda gwanin da Jam'iyyar APC ta gudanar a Abuja.Jigon jami'yyar ya yi nasarar a kan abokan hamayyarsa ne bayan da ya yi musu fintinkau da kuri' 1,271.Tun farko, 'yan takara 23 ne aka tantance don shiga zaben fidda gwani, amma daga bisani an samu wadanda suka janye don goya wa sauran baya.Yayin zaben fidda gwanin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi…
Read More
An damƙe na hannun daman A.A Zaura da ya jagoranci garkuwa da mahaifiyarsa

An damƙe na hannun daman A.A Zaura da ya jagoranci garkuwa da mahaifiyarsa

Daga BASHIR ISAH An kama wani mai suna Maiwada Dakata bisa zarginsa da hannu a garkuwar da aka yi da mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano, A.A Zaura. Mai magana da yawun Zaura, Al-Amin Ciroma, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na facebook a ranar Laraba. Ciroma ya ce Maiwada Dakata amini ne mai kama da dan’uwa ga A.A Zaura saboda yadda suka taso tare, amma ana zarginsa da jagorancin garkuwar da aka yi da Hajiya Laure Mai Kunu, mahaifiyar A.A Zaura. “Jami’an tsaro sun damke wanda ake zargin ne otel a lokacin da yake hutawa tare da budurwarsa yayin…
Read More
Zaɓen APC: Amosun da Fayemi sun janye wa Tinubu

Zaɓen APC: Amosun da Fayemi sun janye wa Tinubu

Daga BASHIR ISAH A ci gaba da fafatawa da ake yi tsakanin 'yan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar APC don tsayar da ɗan takara ɗaya da zai wakilci jam'iyyar a Babban Zaɓen 2023, an samu wasu daga cikin 'yan takarar sun janye aniyar takararsu. Tsohon Gwmanan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun da Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, sun bayyana janyewarsu daga zaɓen fidda gwanin don mara wa tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu baya. Amosun da Fayemi sun bayyan janyewarsu ne a wajen Babban Taron APC da ke gudana a dandalin Eagle Square, Abuja. Su biyun sun yi kira ga ɗaukacin…
Read More
Sai mun kimtsa kanmu kafin mu iya ci gaba da riƙe madafun iko – Adamu ga mambobin APC

Sai mun kimtsa kanmu kafin mu iya ci gaba da riƙe madafun iko – Adamu ga mambobin APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, yaya nunar wa mambobin APC cewa dole su kimtsa cikin gida muddin ana da buƙatar jam'iyyar ta ci gaba da riƙe madafun iko gaba da 2023, yana mai cewa buƙatar jam'iyyar na gaba da ta kowane mamba ko ƙungiya. Adamu ya ce sakamakon taron APC da ya gudana ranar Talata shi zai tantance nasarar da jam'iyyar za ta samu a 2023. Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne a wajen Babban Taron APC a Talatar da ta gabata a dandalin Eagle Square da ke Anuja. Haka nan, Adamu ya yi…
Read More
Sin: An ƙaddamar da jarrabawar shiga jami’a

Sin: An ƙaddamar da jarrabawar shiga jami’a

Daga CMG HAUSA Yau Talata ne aka fara gudanar da jarrabawar shiga jami’a a sassa daban daban na ƙasar Sin. Alƙaluman ma’aikatar ilmi ta ƙasar Sin sun nuna cewa, yawan waɗanda suka yi rajistar rubuta jarrabawar a bana ya kafa tarihi, inda ya kai miliyan 11.93 baki ɗaya, wanda ya ƙaru da miliyan 1 da dubu 150 bisa na shekarar 2021. Akwai wuraren gudanar da jarrabawar guda dubu 330 a duk fadin ƙasar Sin, tare da masu sa ido kimanin miliyan 1 da dubu 20. Fassarawa: Tasallah Yuan
Read More