15
Mar
Daga CMG HAUSA Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin ɗaukar ƙwararan matakai domin haye wahalhalu don tabbatar da samun bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasa mai ɗorewa, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci taron tattaunawar majalisar gudanarwa ta ƙasa a ranar Litinin. Taron ya gabatar da muhimman ɓangarorin da za a mayar da hankali a cikin rahoton ayyukan gwamnati na wannan shekara ga hukumomin da abin ya shafa na majalisar gudanarwar ƙasa da ta kananan hukumomi, kana ya buƙaci a aiwatar da kudurorin yadda ya kamata. Ya bayyana cewa, tattalin arziki yana fuskantar sabbin matsin lamba da…
