Editor

9513 Posts
Zaɓen mace ko namijin aure (II)

Zaɓen mace ko namijin aure (II)

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah da ya sake ba ni damar rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja. Kamar dai yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa za mu cigaba da bada shawarwari ga matasa maza da mata kan zaɓar abokin/abokiyar zamantakewar aure. A yau za mu cigaba daga inda muka tsaya. 3- Rashin yalwa, talauci da tsadar aure: waɗannan suna daga cikin abin da kan kawo jinkirin aure ga samari, don haka bai kamata ba a bi al'ada da ƙuntatawa da tsanantawa ga kuɗin aure da za ta…
Read More
Duk da dokar taɓaci kan ilimi a Sakkwato, firamare ta Ruggar Giwa na cikin wani hali

Duk da dokar taɓaci kan ilimi a Sakkwato, firamare ta Ruggar Giwa na cikin wani hali

Daga AMINU ALHUSSAIN AMANAWA a Sakkwato Makarantar firamaren Ruggar Giwa dai na a ƙauyen Tuntube ne dake yamma da garin Shuni na ƙaramar hukumar mulkin Dange-shuni dake jihar Sakkwato, tafiyar aƙalla mintuna 15 zuwa 20 daga ƙauyen zuwa ƙwaryar birnin Sakkwato. Makarantar wacce aka kafa sama da shekaru 40 da suka gabata, na cigaba da kasancewa cikin halin ka’ka’ni kayi, na lalacewar ajijuwa, da ofishin shugaban makaranta, da ma na malamai, uwa uba rashin kayan rubutu da na karatu da makarantar firamaren ke fama da shi. A cewar ɗaya daga mazauni ƙauyen Malam Muhammad Naira Tuntube, yanayin da makarantar ke…
Read More
Red Cross ta bada tallafin kuɗi don rage raɗaɗin talauci

Red Cross ta bada tallafin kuɗi don rage raɗaɗin talauci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya (NRCS) ta ce, za ta fara shirin raba kuɗaɗe ga mutane miliyan 2.5 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Nijeriya a ƙoƙarinta na magance yunwa da rashin abinci mai gina jiki. Mista Anthony Abah, Sakataren Reshen NRCS Benuwai, ya ba da wannan umarni a Makurdi yayin wani taron horar da ma’aikata da masu sa kai kan yadda za a raba kuɗaɗen shirin na CTP. Ya ƙara da cewa, “a shekarar 2022, al’umma na son fara shirinta na daƙile ko ma kauce wa illar yunwa…
Read More
Tir da kashe ’yan sintiri 63 a Kebbi – Buhari

Tir da kashe ’yan sintiri 63 a Kebbi – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matuqar baƙin cikinsa kan kisan ’yan sintiri su guda 63 da ’yan ta’adda suka yi a garin Zuru na Jihar Kebbi, ya kuma yi kira ga jami’an tsaron mu da su tashi tsaye wajen ganin an shawo kan lamarin. Ya kuma bayyana kisan gillar da wasu ’yan bindiga suka yi wa gomman ’yan sintiri a jihar Kebbi inda suka musu ƙwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Sakaba/Wassagu a matsayin abin takaici da ban tausayi. A cewarsa, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, “wannan…
Read More
Buhari ya umarci Buni ya jagoranci taron APC bisa sharuɗɗa

Buhari ya umarci Buni ya jagoranci taron APC bisa sharuɗɗa

Daga SANI AHMAD GIWA Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa gwamnan Jihar Yobe, kuma Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwaryar Jam'iyyar APC, Mai Mala Buni shi zai jagoranci gudanar da babban taron ƙasa da jam'iyyar ta tsayar a ranar 26 ga Maris, 2022. Jaridar Punch ta jiyo cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Buni ɗin da ya jagoranci taron, amma ya yi masa kashedin cewa ba za a ƙara ɗage ranar yin babban taron jam'iyar na ƙasa ba. Majiyoyi sun shaida wa Punch cewa Buhari ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da ya yi da wasu jiga-jigan jam'iyar a…
Read More
Osinbanjo ya bayyana wa Buhari aniyarsa ta tsayawa takara 2023

Osinbanjo ya bayyana wa Buhari aniyarsa ta tsayawa takara 2023

Daga SANI AHMAD GIWA Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari shirinsa na neman kujerar shugabancin ƙasar a zaven 2023. Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa bayan wata da watanni ana raɗe-raɗi, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa yana sha’awar shugabancin ƙasa. Farfesa Yemi Osinbajo ya faɗa wa mai gidansa cewa idan so samu ne, ya karvi ragamar shugabancin ƙasar nan daga hannunsa a Mayun 2023. Osinbajo yana ganin hakan zai bada damar cigaba da samun nasarorin da aka gani daga lokacin da gwamnatin APC ta karɓi mulki a hannun jam’iyyar PDP.…
Read More
ASUU ta ƙara mako takwas a kan yajin aikin da take yi

ASUU ta ƙara mako takwas a kan yajin aikin da take yi

Daga SANI AHMAD GIWA Yayin da a yau Litinin wa'adin yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) take yi, ƙungiyar ta kuma sanar da tsawaita yajin aikin da makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan buƙatunsu. ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka ƙulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a a ƙasar. Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau, jami’i ne a ƙungiyar ta ASUU, ya ce sun ɗauki matakin ƙara wa’adin…
Read More
Bayan shekara 28, Buhari ya cika alƙawarin bai wa ‘yan wasan Super Eagles gidaje

Bayan shekara 28, Buhari ya cika alƙawarin bai wa ‘yan wasan Super Eagles gidaje

Daga WAKILINMU Shekaru 28 bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi wa 'yan wasan Super Eagles alƙawarin gidaje kyauta, sai a wannan karon Shugaba Muhammadu Buhari ya cika wannan alƙawari da gwamnatocin baya suka kasa cikawa. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaba Buhari da kansa a lokacin da ya ke ƙaddamar da sababbin gidaje da gwamnatinsa ta gina a Lafiya, Babban Birnin Jihar Nasarawa a ƙarshen makon jiya, yana mai cewa, gwamnatinsa a shirye ta ke wajen saka wa duk ɗan ƙasar da ya yi aiki tuƙuru wajen gina Nijeriya. Idan dai za a iya tunawa, a 1994 Gwamnatin…
Read More
Mataimakiyar firaministan Sin ta buƙaci a ɗauki matakan daƙile cutar COVID-19 cikin ƙanƙanin lokaci

Mataimakiyar firaministan Sin ta buƙaci a ɗauki matakan daƙile cutar COVID-19 cikin ƙanƙanin lokaci

Daga CMG HAUSA Mataimakiyar firaministan ƙasar Sin, Sun Chunlan, ta buƙaci yankunan dake fama da tsananin yaduwar annobar COVID-19 su yi ƙoƙarin daƙile cutar a cikin ƙanƙanin lokaci. Sun, ta yi wannan tsokaci ne a wajen taron majalisar gudanarwar ƙasar ta wayar tarho game da matakan yaƙi da annobar COVID-19. Sun ta ce, ya kamata a ƙara ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan gwaje-gwajen cutar, da faɗaɗa ayyukan tantance yanayin lafiyar jama’a, da aikin jigilar marasa lafiyar da kuma aikin killacewa. Ta ƙara da cewa, ya kamata a bayar da fifiko wajen kandagarkin hana shigo da cutar daga ƙetare, inda bangaren tashoshin ruwa…
Read More
Gwmantin ƙasar Sin tana ƙoƙarin gabatar da nagartattun manufofi dake ba da tabbaci ga ayyukan gona

Gwmantin ƙasar Sin tana ƙoƙarin gabatar da nagartattun manufofi dake ba da tabbaci ga ayyukan gona

Daga AMINA XU Manyan taruka biyu na wannan shekara, wato taron majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin NPC da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar CPPCC, sun fitar da sakwanni na bunƙasa sana’o’i na musamman a yankunan da suka fita daga ƙangin talauci, da ƙara ƙarfin raya ƙauyuka. Gwmantin ƙasar Sin tana ƙoƙarin gabatar da nagartattun manufofi dake ba da tabbaci ga ayyukan gona, da ƙara kuɗin shigar manoma, ta yadda za a inganta nasarorin da aka samu wajen sauƙaƙa fatara. Abu mafi muhimmanci ga gwamnati shi ne biyan buƙatun jama’a, da ba da tabbaci ga zaman…
Read More