Editor

9513 Posts
Kisan gillar matar aure a Kano: Ganduje ya bada umurnin gaggauta bincike

Kisan gillar matar aure a Kano: Ganduje ya bada umurnin gaggauta bincike

Daga IBRaHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta bincike da kamo waɗanda su ka kashe wata matar aure mai suna Rukayya Mustapha a cikin gidanta da ke unguwar Danbare, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Kano. Gwamnan ya bada umarnin ne a Litinin da ta gabata lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan marigayiyar a unguwar Ɗorayi dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar. Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge ya fitar, Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf…
Read More
Jaridar The Guardian: Amurka na da tarihin cin zarafin lafiyar fursunoni masu launin fata

Jaridar The Guardian: Amurka na da tarihin cin zarafin lafiyar fursunoni masu launin fata

Daga CRI HAUSA Jaridar The Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa, gwajin maganin ivermectin a gidan yarin Arkansas, ya haska daɗaɗɗen tarihin cin zarafin lafiya da Amurka ke yi wa al’ummomi masu launin fata. Rahoton jaridar ya bayyana cewa, a watan Augustan bara, an yi wa fursunoni 4 dake gidan yarin gundumar Washington dake Arewa maso yammacin Arkansas amfani da ivermectin wajen maganin COVID-19 ba tare da saninsu ba, wanda magani ne da ake amfani da shi ga dabbobin da ake kiwonsu a gida. Cibiyar kandagarki da taƙaita yaduwar cututtuka ta Amurka da hukumar tantance ingancin abinci da magunguna…
Read More
Kafofin watsa labaran Amurka: Masu zuba jari na ƙasa da ƙasa suna ƙara zuba jari ga kasuwar hada-hadar kuɗin Sin

Kafofin watsa labaran Amurka: Masu zuba jari na ƙasa da ƙasa suna ƙara zuba jari ga kasuwar hada-hadar kuɗin Sin

Daga CRI HAUSA Tashar yanar gizo dake ba da labaran sayayya da kasuwanci ta Amurka ta wallafa wani rahoto a ranar 17 ga wata dake cewa, duk da cewa, masu zuba jari dake cikin gidan ƙasar Sin ba su nuna kuzari sosai ga kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar ba, masu zuba jari na ƙasa da ƙasa na ƙara zuba jarinsu ga kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar Sin. Alƙaluma sun nuna cewa, a watan Janairun bana, adadin kuɗin da aka zuba kan kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 16.6, wannan kuma shi ne karo na huɗu da adadin ya…
Read More
Bacci a jikin ɗan’adam (2)

Bacci a jikin ɗan’adam (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Idan kun shirya, bismillah! A makon da ya gabata,  na fara bayani ne a kan yadda bacci ya ke a jikin ɗan adam. Inda na fara somin taɓin manyan al'amura da sula shafi bacci. Na faɗa cewa bacci maudu'i ne mai faɗin gaske, wanda ya ke da alaƙa da rayuwar ɗan adam ta fuskoki da dama irinsu: nutusuwa,…
Read More
Buhari zai rattaɓa hannu kan sabuwar dokar zaɓe, inji mashawarcinsa

Buhari zai rattaɓa hannu kan sabuwar dokar zaɓe, inji mashawarcinsa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A cikin taraddadin ƙila-wa-ƙala ko Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba zai rattaɓa hannu akan dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima ba cikin wa’adin kwanaki 30 na yin hakan, mai ba shi shawarwari a kan lamuran Majalisar Dattawa, Sanata Babajide Omoworare ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewar, Shugaba Buhari zai rattaɓa hannu akan dokar ta zaɓe. Hadimin na Shugaban Ƙasa ya bayar da wannan tabbaci ne yayin wata tattaunawar jin ra’ayi da Cibiyar Lamuran Majalisa da Nazarin Siyasa ta shirya a birnin tarayya ta Abuja a satin da ya gabata. Tattaunawar ta neman cimma…
Read More
2023: Jonathan ya ɗabbaƙa takarar shugabancin ƙasa ta Gwamna Bala

2023: Jonathan ya ɗabbaƙa takarar shugabancin ƙasa ta Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya amince da shaidar takarancin neman shugabancin ƙasar nan da Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yake yi, yana mai bayyana Gwamna Bala da cewar, mutum ne mai tsantsar haƙuri, tawali’u da kuma sauraron kasancewar Nijeriya kyakkyawar ƙasa da inganci. A wani jawabi da mataimaki ga gwamnan kan hulɗa da kafofin yaɗa labarai ta intanet, Lawal Muazu Bauchi, ya ce Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis da ta gabata, yayin da yake yi wa Gwamna Bala marhabun a gidan sa…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta buɗe kasuwar gwal a Kano

Gwamnatin Tarayya za ta buɗe kasuwar gwal a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin cewa, nan da watanni 10 masu zuwa za ta kammala gini sannan kuma ta buɗe kasuwar gwal ɗin da take ginawa a Jihar Kano.  Ministan tama da ƙarafa na tarayyar Nijeriya, Arc Olamilekan Adegbite, shi ya tabbatar da haka a yayin wata ziyarar rangadi da ya kai ga kasuwar da ake ginawa a halin yanzu a jihar Kano.  Waɗannan jawabai suna ƙunshe ne a cikin wata takarda da kakakin Ma'aikatar tama da ƙarafa, Idowu Jokpeyibo ya wallafa. A cikin jawabin, an bayyana cewa, Shugaba Buhari na Nijeriya ya yi alƙawarin cewa,…
Read More
Ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwar mutane 94 a Brazil

Ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwar mutane 94 a Brazil

Aqalla mutane 94 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zabtarerwar ƙasa a Brazil bayan an shafe tsawon lokaci ana shatata ruwan sama kamar da bakin-kwarya. Lamarin ya auku ne a birnin Petropolis mai cike da wuraren ƙayatarwa da yawon buɗe ido kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana. Bayanai na cewa, akwai yiwuwar samun ƙarin mamata, ganin yadda alƙalumansu ke ci gaba da ƙaruwa sannu a hankali a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ta ƙoƙarin nemo masu sauran numfashi. Dimbin mutane ne dai ke ci gaba da makalewa a cikin laka da kuma tarin buraguzai. Da…
Read More
Majalisar Wakilai za ta hana aikin jarida ga marasa digiri

Majalisar Wakilai za ta hana aikin jarida ga marasa digiri

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na neman tsaftace aikin jarida a Nijeriya, Majalisar Wakilai ta soma nazarin ɗaga shaidar zama ɗan jarida zuwa digiri na ɗaya ko HND ko makamancin haka a aikin jarida. Buƙatar hakan ta taso ne biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ado/Ogbadigbo/Okpokwu, Francis Agbo ya gabatar a gaban majalisar na neman yi wa dokar aikin jarida kwaskwarima, wato Nigerian Press Council Amendment Bill 2019. Tuni dai wannan ƙuduri ya tsallake matakin nazari na ɗaya ake kuma shirin nazarinsa a mataki na biyu inda ake buƙatar yi wa dokar aikin jaridar, wato…
Read More
Ganduje ya naɗa Khalid Musa hadiminsa kan sha’anin Kannywood

Ganduje ya naɗa Khalid Musa hadiminsa kan sha’anin Kannywood

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya naɗa Khalid Musa a matsayin Babban Hadimi na Musamman (SSA) kan sha'anin masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, naɗin da ya soma aiki daga ranar 8 ga Fabrairun 2022. Sanarwar naɗin na ƙushe ne cikin wasiƙar da sashen REPA da ke ƙarƙashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, wadda Babbar Sakatariyar REPA, Bilkisu Shehu Maimota ta sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar. A cewar wasiƙar, an naɗa Musa a matsayin SSA ne duba da jajircewarsa, sadaukarwa a bakin aiki, sanin makamar aiki, ƙwazo da kuma biyayyar da yake da su, wanda…
Read More