Editor

9513 Posts
Kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya ya bai wa al’ummar ƙasar Sin kofin Olympic

Kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya ya bai wa al’ummar ƙasar Sin kofin Olympic

Daga CRI HAUSA A wajen cikakken zama na 139 da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa wato IOC ya shirya a jiya Asabar a Beijing, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya karrama al’ummar ƙasar Sin da kofin Olympics, da nufin gode musu saboda goyon-bayansu ga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana. Bach ya ce, ba don goyon-bayan mutanen Sin ba, da ba za a iya shirya gasar bana tare da samun cikakkiyar nasara ba. Duk da cewa an shirya gasar bana cikin wani yanayi na kulle don hana yaɗuwar cutar COVID-19, amma Bach ya ji dadin…
Read More
Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa ya sake hira da ‘yan jaridun CMG

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa ya sake hira da ‘yan jaridun CMG

Daga CRI HAUSA Kafin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana a Beijing, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa wato IOC, Thomas Bach ya sake zantawa da ‘yan jaridun CMG, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin. Bach ya bayyana cewa, ‘yan wasannin ƙasa da ƙasa sun shaida wa duniya kyawawan halayensu, da bayyana ma’anar zumunci da samun fahimtar juna da zaman lafiya. Alal misali, ‘yan wasannin Ukraine da Rasha sun rungumi juna, kana, ‘yan wasan ƙasar Sin sun goyi bayan ‘yan wasan Amurka, har sun ba su tambarin Olympics kyauta don…
Read More
Cutar korona: Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta harbu

Cutar korona: Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta harbu

Rahotanni daga ƙasar Ingila na nuni da cewa Sarauniya Elizabeth ta kamu da cutar korona. Fadar Buckingham ce ta bada sanarwar faruwar hakan. Bayanan fadar sun nuna sarauniyar na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa. Fadar ta bayyana a cikin sanarwar tata cewa, "Za a ci gaba da duba sarauniyar kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace." BBC ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta haɗu da babban ɗanta kuma magajinta, wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu…
Read More
Gwamna Ganduje: Shin dankali sha kushe ne..?

Gwamna Ganduje: Shin dankali sha kushe ne..?

Daga NASIR S. GWANGWAZO Gwamnan Jihar Kano, Injiniya (Dr.) Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake yi wa laƙabi da Khadimul Islam, ya kasance gwamnan da ya ke jagorantar jiha mafi yawan jama’a a Nijeriya kawo yanzu kusan tsawon shekara bakwai kuma a yanayin tafiyar siyasar da ake yi zai shekara takwas yana jan ragamar mulkin jihar, idan da rai, lafiya da nisan kwana. Tabbas ko da ba a faɗa ba, jiha kamar Kano za ta iya yin wahalar tafiyarwa, saboda yanayin yawan al’ummar da ta ke da shi da kuma zafin siyasa ta aƙida da aka san Kanawa da ita. Kusan…
Read More
Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya

Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya

Daga CRI HAUSA Ma’aikatar kuɗi ta ƙasar Sin, ta yi kira ga ƙasashen duniya su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tafiyar da dabarun da suka shafi tattalin arziki, a matsayin wata hanya ta samun ci gaba na bai ɗaya. Ministan kuɗi na ƙasar Sin, Liu Kun ne ya bayyana haka, yayin wani taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashen G20 da ya gudana ta kafar bidiyo. A cewar Liu Kun, cikin ƙasashen ƙungiyar G20, ƙasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudunmuwa ga shirin sauƙaƙa basussuka ga ƙasashe masu fama da talauci. Ya ce ƙasar Sin tana kira ga…
Read More
Jakadan ƙasar Sin: Sin na ingiza tattaunawa kan batun kwance ɗamarar soji

Jakadan ƙasar Sin: Sin na ingiza tattaunawa kan batun kwance ɗamarar soji

Daga CRI HAUSA Shugaban karɓa-karɓa na farko na shekarar 2022 na taron tattauna batun kwance ɗamarar soji na birnin Geneva, kuma jakadan ƙasar Sin kan wannan batu, Li Song ya kira cikakken taro yayin da ya yi nasarar kammala wa’adin shugabaci na ƙasar Sin a jiya Juma’a. Bayan taron, Li Song, ya tattauna da kafofin watsa labarai na birnin Geneva, inda ya bayyana cewa, taron ya kasance dandali ɗaya tilo dake tattauna batun kwance damara tsakanin bangarori daban-daban, inda ƙasashe mambobi 65 ke karɓar shugabanci ɗaya bayan ɗaya. Ya ce ƙasar Sin ta sake zama shugaba ne bayan shekaru 11…
Read More
’Yan sandan Bauchi sun cafke soja da tabar wiwi

’Yan sandan Bauchi sun cafke soja da tabar wiwi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Wani da aka ayyana a matsayin jami’in soja mai suna Yusuf Gongpolai Adams, da aka cafke da pasul-pasul guda 81 na tabar wiwi yanzu haka yana tsare a kurkukun ‘yan sanda na jihar Bauchi. Gongpolai, wanda yake jami’in soja ne na rundunar soji dake bataliya ta 145 a jihar Abiya, an damƙe shi ne a ranar 6 ga wannan wata na Fabrairu, 2022 akan hanyar Bauchi zuwa Darazo cikin wata mota ‘Toyota Highlander’. Da yake nuna shi wa manema labarai a garin Bauchi a ranar Talata da ta gabata, kwamishinan ‘yan sanda na jihar,…
Read More
Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a ya rasu

Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a ya rasu

Daga ABUBAKAR LABARAN KAFANCAN Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema'a da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sheik Adam Tahir ya rasu yana da shekaru 130 a duniya. Jaridar Manhaja ta samu bayanin cewa Sheikh Tahir ya rasu ne ranar Laraba a garin Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Da yake yi wa manema labarai bayani bayan rufe limamin a maƙabartar musulmai da ke Kafanchan, Mataimakin Limami na masarautar Kafanchan, Alhaji Muhammad D. Kassim ya ce babban limamin ya shafe fiye da shakara 35 yana gabatar da sallah a babban masallacin Kafanchan, ya bayyana cewa shi mutum ne na kowa, wanda kowa…
Read More
An halaka ɗan binidgar da ya kashe DPO

An halaka ɗan binidgar da ya kashe DPO

*Jiragen sojoji ya sheƙa Dogo Umaru da ’yan ta’adda 41 barzahu Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta samu gagarumar nasarar sheƙa wasu gungun ƙasurguman ’yan bindiga zuwa barzahu, waɗanda suka kitsa kashe Babban Jami’in ’Yan Sanda na Yanki (DPO) a Jihar Katsina. Hare-haren da jiragen NAF ya kai a jiya Alhamis ya samu nasarar halaka Dogo Umaru, wanda ƙusa ne a tafiyar babban ɗan bindigar nan, Bello Turji, wanda ake zargi da addabar yankin Arewa maso Yamma da ayyukan garkuwa da mutane da kuma kisan kiyashi. A tare da Umaru akwai ’yan bindiga…
Read More
Ƙarancin fetur ya jagwalgwala rayuwar ’yan Nijeriya

Ƙarancin fetur ya jagwalgwala rayuwar ’yan Nijeriya

*Za a warware matsalar ba jimawa – Gwamnati Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja ’Yan Nijeriya na cigaba da fuskantar azabar ƙarancin man fetur a ƙasar yayin da hukumomi suka ce su na yin aiki a wani yunƙuri na magance matsalar ƙarancin man da ya janyo raguwar kuɗaɗen shiga a kowane fanni. Birnin Abuja da manyan jihohin Nijeriya sun afka cikin matsanacin ƙarancin man fetur duk da alƙawarin da mahukunta suka yi na samar da shi. Wannan ya kawo cikas a harkokin yau da kullum, saboda ana sayar da shi da tsada, sannan kuma ga wuyar samu. A lokuta da…
Read More