Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a ya rasu

Daga ABUBAKAR LABARAN KAFANCAN

Babban Limamin Ƙaramar Hukumar Jema’a da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sheik Adam Tahir ya rasu yana da shekaru 130 a duniya.

Jaridar Manhaja ta samu bayanin cewa Sheikh Tahir ya rasu ne ranar Laraba a garin Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan rufe limamin a maƙabartar musulmai da ke Kafanchan, Mataimakin Limami na masarautar Kafanchan, Alhaji Muhammad D. Kassim ya ce babban limamin ya shafe fiye da shakara 35 yana gabatar da sallah a babban masallacin Kafanchan, ya bayyana cewa shi mutum ne na kowa, wanda kowa ke so, kuma musulmi nagari.

Daga cikin ɗumbin musulman da suka halarci jana’izar babban limamin, akwai Shugaban Ƙaramar Hukumar Jema’a Mista Yunana Markus Barde da Sarkin Jema’a Alhaji Muhammad Isah Muhammadu.

A saqon ta’aziyyarsa, Sarkin Jema’a Alhaji Muhammad Isah Muhammad ya bayyana rasuwar limamin a matsayin babban rashi ga jama’ar masarauta da kafatanin jama’ar Kudancin Kaduna.

A takardar ta’aziyyar wacce Sakataren masarautar Alhaji Yakubu Isah (Dakajen Jema’a) ya sanya wa hannu, ya nuna alhinin sa na rashin babban limamin da kuma ɗaya daga cikin masu naɗa sarki, sa’annan ya yi wa mamatan addu’ar samun rahamar Ubangiji da sakamako mai kyau a ranar gobe kiyama.

Ibrahim Adam Tahir, ɗa ga marigayin, ya bayyana wa Manhaja cewa mahaifin su ya haifi ‘ya’ya 50, inda ya rayu da ‘ya’ya 26 da jikoki 290 da kuma jikan-jikoki fiye da 200.