Editor

9513 Posts
Dokar hana ci da safarar jakai babbar illa ce gare mu, cewar dilolin jakai

Dokar hana ci da safarar jakai babbar illa ce gare mu, cewar dilolin jakai

Daga AMINA YUSUF ALI Diloli masu safarar jakuna a faɗin Nijeriya sun koka matuƙa a kan dokar da gwamnatin tarayya ta riga ta zartar a kan hana ci da safarar jakunan.  Shugaban ƙugiyar dilolin jakuna ta Nijeriya, Mista Dike Ifeanyi shi ya bayyana haka a yayin zantawar sa da manema labarai a game da dokar hana safara da cin jakunan da sayar da abinda ya shafe su da gwamnatin Nijeriya ta sanya a 'yan kwanankin nan. Inda ya bayyana wasu daga cikin alfanun kiwatawa da cinikin jakunan a ƙasar nan.  Daga cikin falalar jakunan a cewar sa, sun haɗa da,…
Read More
Shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata Jihar Kebbi ta sha alwashin haɗa kan mata

Shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata Jihar Kebbi ta sha alwashin haɗa kan mata

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sabuwar shugabar gamayyar ƙungiyoyin mata ta ƙasa reshen jihar Kebbi, Hajiya Halima Hassan, ta ƙuduri aniyar haɗa kan matan Jihar Kebbi, domin bunƙasa tattalin arzikinsu. Ta yi wannan bayani ne jiya Alhamis a garin Argungu lokacin da ta ke zantawa da wakilin jaridar Blueprint Manhaja. Ta ce ya zama wajibi ga mata da su tashi tsaye wajen haɗa kai ta hanyar ɗabbaƙa ƙungiyoyin mata ta yadda za su samu nasarar samun duk wani shiri na tallafi tun kama daga na sana'o'i ya zuwa neman haƙƙinsu.  Hajiya Halima Hassan ta ce an kafa wannan ƙungiyar tun…
Read More
Gwamnatin Katsina ta haramta aikace-aikacen ’yan sa-kai

Gwamnatin Katsina ta haramta aikace-aikacen ’yan sa-kai

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari ta haramta ayyukan 'yan  sa kai a duk faɗin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba wa gwamnan jihar shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina. Kamar yadda takardar ta bayyana dakatar da aikace-aikacen 'yan sa kai ɗin ya biyo bayan kashe-kashen mutane da ake yi ba gaira babu dalili a jihar. Sanarwar ta ƙara da cewar dokar ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu na wannan shekarar da muke ciki.…
Read More
Sojojin Nijeriya sun kashe alƙalin alƙalan ‘yan ta’adda

Sojojin Nijeriya sun kashe alƙalin alƙalan ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH A cigba da yaƙi da 'yan ta'adda da suke yi a faɗin ƙasar nan, sojojin Nijeriya sun taki nasara a wani samame da suka kai wa mayaƙan ISWAP inda suka kashe wasu kwamandojinsu ciki har da alƙalin alƙalan 'yan ta'addan. Kwamandojin da suka rasa rayukan a wannan karon sun haɗa da Musa Amir Jaish da Mahd Maluma (alƙalin alƙalan ISWAP) Abu-Ubaida da Abu-Hamza da kuma Abu-Nura Umarun Leni. Bayanan da MANHAJA ta tattaro sun nuna matse ƙaimin da sujojin suka yi a bakin aiki ne ke ci gaba da bai wa sojojin damar samun nasara a kan…
Read More
USAID ta bada tallafi ga manoman rogo 100 a Kwara

USAID ta bada tallafi ga manoman rogo 100 a Kwara

Daga AMINA YUSUF ALI Kimanin ƙananan manoman rogo guda 100 ne dai 'yan asalin jihar Kwara suka samu tagomashin tallafi daga ƙungiyar tallafi ta Amurka (USAID) don bunƙasa harkar noma.  An zavo waɗannan manoman rogo ne daga ƙananan hukumomin jihar Kwara. Inda aka fara da ba su kayan aiki da kuma horaswa a fannin noman zamani domin ingantawa da bunƙasa sana'arsu.  Mashiryin shirin ba da tallafin jarin ga manoman rogon, Mista Banjo Famuyiwa, ya bayyana cewa, wannan shirin USAID a Nijeriya ce ta ɗauki nauyinsa tare da haɗin gwiwar AYOSIFAM da ma'aikatar faɗaɗa aikin noma da raya karkara ta jihar…
Read More
Matsalar garkuwa da mutane laifin gwamnonin Arewa ne, inji Miyetti Allah

Matsalar garkuwa da mutane laifin gwamnonin Arewa ne, inji Miyetti Allah

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Matsalar da ake fama da ita a arewacin Nijeria ta fuskar garkuwa da mutane da satar dabbobi da rashin zaman lafiya laifin gwamnonin Arewa ne, inji shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Muhammed Baɗejo a lokacin da ya je ziyarar aiki ta kwana ɗaya a cikin wannan makon. Baɗejo ya ci gaba da cewar gwamnonin Arewa su ne suka gaza wajen inganta rayuwar Fulani makiyaya ta fuskar samar masu da kayan more rayuwa da tsunduma su cikin harkokin Fulani makiyaya. Ya ce rashin kulawar gwamnonin Arewa a kan Fulani makiyaya shi ne…
Read More
Nijeriya 2023: Birnin Daura ya tumbatsa da fastocin takarar Amaechi

Nijeriya 2023: Birnin Daura ya tumbatsa da fastocin takarar Amaechi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi A Kwanakin baya ne Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ya yi addu’ar Ministan sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaechi, wanda ya bayyana shi da mai nasara kan dukkan abinda ya sanya a gaba, Allah ya ba shi wani matsayi fiye da wanda yake a kai. Shahararren sarkin dai ya yi wannan addu’a ce yayin da yake karrama Minista Amaechi da sarautar gargajiya ta Ɗan Amanar Daura, wanda yake nufin amintaccen ɗan Daura. Bikin naɗin na Ɗan Amanar Daura ya samu halartar fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan, haɗi da waɗanda suke…
Read More
Shugaba Xi Jinping ya halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing

Shugaba Xi Jinping ya halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing

Daga CRI HAUSA An yi bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu karo na 24 a Beijing a daren yau Lahadi, inda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa Thomas Bach suka halarci bikin. A jawabin da shugaban kwamitin wasannin Olympic ta ƙasa da ƙasa IOC, Thomas Bach, ya gabatar a bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing da cewa “ta musamman ne." A gun bikin rufe gasar, an kuma damqa tutar Olympic ga magajin garin Milan da na Cortina d'Ampezzo, biranen da…
Read More
Afirka ta nuna damuwa ko Turai za ta iya cika alƙawurran da ta ɗauka a wajen taron ƙolin Turai da Afirka

Afirka ta nuna damuwa ko Turai za ta iya cika alƙawurran da ta ɗauka a wajen taron ƙolin Turai da Afirka

Daga CRI HAUSA A ranar 18 ga wata, aka kammala taron ƙoli tsakanin ƙungiyar tarayyar Turai EU da ƙungiyar tarayyar Afirka wato AU a birnin Brussels na ƙasar Belgium, inda aka cimma wasu nasarori a ɓangarorin da suka shafi sake tsugunar da al’umma, da kiwon lafiya, ciki har da wani shirin zuba jari ga ƙasashen Afirka da EU ta sanar, wanda ke ƙunshe da kuɗin EURO biliyan 150. Masanin dangantakar ƙasa da ƙasa daga ƙasar Kenya, Cavins Adhill ya yi tsokaci kan nasarorin taron ƙolin, inda a cewarsa, duba da yadda nahiyar Afirka ke matuƙar buƙatar zuba jari a fannin…
Read More
Sin tana maraba da ziyarar Jami’ar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Xinjiang

Sin tana maraba da ziyarar Jami’ar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Xinjiang

Daga CRI HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya ce, ƙasar Sin tana maraba da zuwan babbar jami’ar kare haƙƙin ɗan adam ta MDD Michelle Bachelet, wacce za ta ziyarci ƙasar, ciki har da yankin Xinjiang. Wang, yayin da ya halarci taron ƙolin al’amurran tsaro na Munich karo na 58 ta kafar bidiyo, ya yi furucin ne a yayin da ya mayar da martani dangane da batun dake shafar yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na Uygur na ƙasar Sin. Ya bayyana cewa, Xinjiang wani yankin ne dake kan iyakar wurare masu fuskantar…
Read More