Editor

9513 Posts
Rikicin APC: Ganduje ya lallasa Shekarau a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Rikicin APC: Ganduje ya lallasa Shekarau a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis da ta gabata Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta shure hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yanke na rushe zaɓen shugabannin jam'iyyar APC a matakin unguwanni da ƙananan hukumomi da jihar Kano ta gudanar kwanan baya. Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi na'am da duka ƙararraki guda ukun da ɓangaren Gwamna Ganduje ya ɗaukaka aa gabanta. Jim kaɗan bayan kammala zaɓen APC na Kano, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya shigar da ƙara gaban Babbar Kotun Abuja yana mai ƙalubalantar sahinhanci zaɓen tare da neman kotu ta rushe zaɓen sannan ta naɗa 'yan ɓangarensa a…
Read More
Shugaban IOC ya yaba da fasahar CMG

Shugaban IOC ya yaba da fasahar CMG

Daga CRI HAUSA Ranar 18 ga wata, shugaban kwamitin wasan Olympic na ƙasa da ƙasa wato IOC ya shirya taron manema labaru, inda shugaban kwamitin Thomas Bach ya ce, yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, an gwada fasahohi iri daban-daban, musamman ma mabambantan fasahohin zamani mallakar babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG, waɗanda suka ba shi mamaki sosai. Ya yi imanin cewa, fasahohin ƙasar Sin za su ƙara ba da gudummawa kan wasannin Olympics a nan gaba. Shugaban IOC ya ƙara da cewa, an samu nasara sosai a gasar…
Read More
Ƙasar Sin ta cimma manufar shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara

Ƙasar Sin ta cimma manufar shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara

Daga CRI HAUSA Yayin da ƙasar Sin ke neman baƙuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022, ta yi wa ƙasashen duniya alƙawarin shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin ƙanƙara. Bayan da ta samu nasarar karɓar baƙuncin shirya gasar a shekarar 2015 har zuwa yanzu, wasannin ƙanƙara sun zama wata hanyar jin daɗin zama a tsakanin al’ummar ƙasar Sin. Adadin ƙididdiga ya nuna cewa, tun bayan da ƙasar Sin ta samu damar karɓar baƙuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ya zuwa watan Oktoban shekarar 2021, yawan mutanen da suka shiga wasannin…
Read More
Hukumar NFC ta naɗa Shugaban MOPPAN, Dr. Sarari, jagoran kwamitin bajekolin finafinai na ƙasa

Hukumar NFC ta naɗa Shugaban MOPPAN, Dr. Sarari, jagoran kwamitin bajekolin finafinai na ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An naɗa Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN), Dr. Ahmad Muhammad Sarari, a matsayin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Shirya Bajekoli na Ƙasa (Zuma Film Festival) na bana, wato shekara ta 2022, mai kula da Shiyyar Kano da Kaduna a bajekolin da zai gudana a ranakun 2 zuwa 8 ga Afrilu, 2022. Naɗin na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da Daraktan Shirin Bajelkolin, Edmund Peters, ya aike wa Shugaban na MOPPAN mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Fabrairu, 2022, kuma Blueprint Manhaja ta samu kwafi. A cikin wasiƙar, hukumar da…
Read More
Xan wasan Nijeriya a gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

Xan wasan Nijeriya a gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

By CRI HAUSA Bisa labarin da kwamitin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ya bayar, an ce, Samuel Uduigowme Ikpefan mai shekaru 30 da haihuwa, ya kammala gasarsa a wasannin Olympics na bana, inda ya samu matsayi na 73, a gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji ta gajeren zango, kuma bai kammala wasanni ba cikin gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji mai nisan kilomita 15. Ikpefan ya zama ɗan wasa daya tak cikin tawagar Nijeriya a gasar ta Olympics na wannan karo, kuma shi ne ɗan wasan dusar ƙanƙara na farko a tarihin Nijeriya. An haifi…
Read More
Sudan ta kudu ta yaba ci gaban da aka samu a aikin talabijin da ƙasar Sin ke gudanarwa

Sudan ta kudu ta yaba ci gaban da aka samu a aikin talabijin da ƙasar Sin ke gudanarwa

Daga CRI HAUSA Wani jami’in ƙasar Sudan ta kudu ya yaba yadda ayyukan da kamfanonin gine-gine biyu na ƙasar Sin ke gudanarwa suke gudana ciki sauri a babban gidan radiyo da talabijin na ƙasar. Ramadan Kamil Abulangi, daraktan sashen injiniya na babban gidan radiyon ƙasar Sudan ta kudu (SSBC), ya ce, aikin wanda aka fara gudanarwa a shekarar 2019 zai kawo gagarumin sauyi ga ayyukan yaɗa labarai na gidan radiyo da talabijin na ƙasar idan aikin ya kammala a watan Agusta. Kamfanonin China Dalian International Economic da Technological Cooperation Group Co. Ltd da Beijing Yutian Suocheng Technology Co. Ltd ke…
Read More
UNICEF ta koka da ƙaruwar yi wa mata kaciya a Nijar

UNICEF ta koka da ƙaruwar yi wa mata kaciya a Nijar

Yi wa mata kaciya na ci gaba da zama babbar matsala a fanin kiyon lafiyar al’umma, ɗiyaucinsu da kuma take haƙƙoƙinsu da ake yi ta wannan mummnar al’ada, lura da irin aika aikar da a hakan ke haifarwa ga ƙoshin lafiyarsu, sai dai abin baƙin ciki a Jamhuriyar Nijer wannan ɗabi’a maimakon raguwa sai ci gaba da ƙaruwa a cewar UNICEF. Haka dai abin yake, idan ba a ɗau matakan da suka dace ba 'yan mata miliyan 68 ne za su fuskanci kaciyar nan da shekara ta 2030 a duniya, kamar yadda wani bincike da hukumar yara ta Majalisar Dinkin…
Read More
Ban yi garkuwa da Hanifa ko kashe ta ba – Abdulmalik Tanko

Ban yi garkuwa da Hanifa ko kashe ta ba – Abdulmalik Tanko

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da da farko ya amsa cewa ya kashe ɗalibarsa 'yar shekara 5, Hanifa Abubakar, ya yi mi'ara-koma-baya, inda ya ce sam bai yi garkuwa da ita ba, ballantana ma ya kashe ta. Manhaja ta rawaito cewa gwamnatin Kano ce ta maka Tanko da abokan aikata laifin sa biyu, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, a Babbar Kotun Kano mai lamba 5, inda ta ke tuhumar su da laifuka biyar. Duk su ukun ana tuhumar su da haɗin baki, garkuwa da mutum, ɓoye wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kisan…
Read More
Ana barazana da rayuwata saboda ƙin goyon bayan tsige Mahdi, cewar ɗan majalisar Zamfara

Ana barazana da rayuwata saboda ƙin goyon bayan tsige Mahdi, cewar ɗan majalisar Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Salisu Usman, wanda shi kaɗai ne ba ya goyon bayan a tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara, ya ce ya yi gudun hijira daga Zamfara, saboda yunƙurin da “gwamnatin jihar ke yi domin ta cim min don na ƙi goyon bayan a tsige mataimakin gwamna.” Usman dai shi kaɗai ne ba ya goyon bayan tsigewar, kuma shi kaɗai ne ɗan majalisar da ya rage a PDP, sauran duk sun bi Gwamna Bello Matawalle zuwa jam'iyyar APC. Ya ƙi halartar zaman majalisa na makon jiya, inda mambobi 18 daga cikin 22 su…
Read More
Aston Villa ta shirya sayen ɗan wasan Nijeriya, Ndidi

Aston Villa ta shirya sayen ɗan wasan Nijeriya, Ndidi

Ɗan wasan tsakiyar Nijeriya da Leicester City, Wilfred Ndidi, ya ce, ba shi da sha'awar barin Leicester City a yanzu, duk da shirin Ƙungiyar Aston Villa ke yi na miƙa tayin Fam miliyan 50 kan shi. Jaridar Daily Star ta Burtaniya ta ruwaito cewa, Villa ta kammala shirye-shiryen taya Ndidi, kuma idan har ciniki ya faɗa a ƙarshen kaka zai zama ɗan wasan mafi tsada da ƙungiyar ta tava saye a tarihi. Ndidi ya buga wa Leicester wasanni 23 a bana, inda ya ci wa Foxes ɗin ƙwallo ɗaya. To, sai dai tsohon ɗan wasan Genk din ya ce, "ina…
Read More