Sudan ta kudu ta yaba ci gaban da aka samu a aikin talabijin da ƙasar Sin ke gudanarwa

Daga CRI HAUSA

Wani jami’in ƙasar Sudan ta kudu ya yaba yadda ayyukan da kamfanonin gine-gine biyu na ƙasar Sin ke gudanarwa suke gudana ciki sauri a babban gidan radiyo da talabijin na ƙasar.

Ramadan Kamil Abulangi, daraktan sashen injiniya na babban gidan radiyon ƙasar Sudan ta kudu (SSBC), ya ce, aikin wanda aka fara gudanarwa a shekarar 2019 zai kawo gagarumin sauyi ga ayyukan yaɗa labarai na gidan radiyo da talabijin na ƙasar idan aikin ya kammala a watan Agusta.

Kamfanonin China Dalian International Economic da Technological Cooperation Group Co. Ltd da Beijing Yutian Suocheng Technology Co. Ltd ke gudanar da aikin bisa haɗin gwiwa.

Kamil ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan aiki ne mafi muhimmanci ga Sudan ta kudu saboda za a samar da na’urar yaɗa shirye-shirye mai tsawon mita 120, kuma za a samar da yanayin sadarwa wanda zai haɗa fadar shugaban ƙasar yayin da ake watsa shiri na kai tsaye, sannan za a samar da wani yanayin sadarwar wanda zai kewaye birnin Juba don watsa dukkan shirye-shiryen da ake gabatarwa kai tsaye.