Ban yi garkuwa da Hanifa ko kashe ta ba – Abdulmalik Tanko

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da da farko ya amsa cewa ya kashe ɗalibarsa ‘yar shekara 5, Hanifa Abubakar, ya yi mi’ara-koma-baya, inda ya ce sam bai yi garkuwa da ita ba, ballantana ma ya kashe ta.

Manhaja ta rawaito cewa gwamnatin Kano ce ta maka Tanko da abokan aikata laifin sa biyu, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, a Babbar Kotun Kano mai lamba 5, inda ta ke tuhumar su da laifuka biyar.

Duk su ukun ana tuhumar su da haɗin baki, garkuwa da mutum, ɓoye wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kisan kai, laifukan da su ka saɓa wa sassa na 97, 274, 277 da kuma 221 na dokar ‘Penal Code’ ta jihar.

A zaman kotun na ranar Litinin, bayan da a ka karanto musu laifukan su, Tanko, a matsayin wanda a ke zargi na 1, da Isyaku, wanda a ke zargi na 2 sun musanta laifukan nasu, ban da tuhuma ta farko.

Ita kuwa Fatima, wacce ake zargi ta 3, ta musanta dukka tuhumomin da a ka yi mata.

A nashi ɓangaren, lauyan waɗanda ake ƙara, M.L. Usman, a bisa dogaro da sashi na 36 (6b), ya nemi gwamnati da ta ba shi dukkanin takardun shari’ar domin ya yi nazari sannan a hanzarta shari’ar, inda ya nemi da a ba shi takardun a ƙasa da mako ɗaya.

Bayan wannan roƙo nasa, sai alƙalin kotun, Mai Shari’a Usman Na-Abba ya yarje masa.

Ya kuma ɗage zaman zuwa 2 da kuma 3 ga watan Maris domin sauraren ƙarar.

Sannan Na-Abba ya bada umarnin aikewa da waɗanda ake zargin gidan yari domin cigaba da tsare su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *