Editor

9513 Posts
Ƙarancin fetur: Gunagunin ’yan Nijeriya ya sa NNPC kwana rabon mai

Ƙarancin fetur: Gunagunin ’yan Nijeriya ya sa NNPC kwana rabon mai

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin dillancin man Fetur a Nijeriya, NNPC, ya bayyana cewa, sashensu na rarraba man fetir ga 'yan kasuwa masu sari ya fara kwana yana aiki domin tabbatar da an sallami dukkan motocin dakon man da suka zo ɗaukar man. Daraktan Zartaswa na ɓangaren rarraba man na Kamfanin NNPC ɗin, Adetunji Adeyemi shi ya bayyana wa 'yan jarida hakan a Abuja. Inda ya ƙara da cewa, a yanzu haka kusan lita biliyan biyu da kusan rabi na man fetur za a shigo da shi ƙasar nan kafin nan da ƙarshen…
Read More
An jigbe gawargawaki tsawon shekara huɗu a Cibiyar Lafiya da ke Keffi

An jigbe gawargawaki tsawon shekara huɗu a Cibiyar Lafiya da ke Keffi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar gudanarwar babbar Cibiyar Lafiya ya Tarayya, wato Federal Medical Centre, da ke garin Keffi, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, ta ce, a yanzu haka akwai kimanin gawarwakin mutane 10 da suke ɗakin adana gawarwaki a cibiyar, waɗanda suka shafe shekaru huɗu a ajiye.  Babban jami’in hulɗa da jama’a na cibiyar Mohammed Adamu ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da Wakilin Blueprint Manhaja dangane da lamarin a ofishinsa da ke cibiyar ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairun da ake ciki.  Ya ce, waɗannan gawarwarki waɗanda ba a san…
Read More
Ruɗani kan shigo da gurɓataccen fetur a Nijeriya

Ruɗani kan shigo da gurɓataccen fetur a Nijeriya

A Nijeriya masu ababan hawa sun shiga tsaka mai wuya sakamakon ƙarancin man fetur a gidajen mai da kuma samun gurɓataccen man da wasu ke sayarwa, abin da ya sa kasuwar bayan fage tashi. Ruɗani a kan shigo da gurɓataccen man fetur ɗin dai ya jefa ’yan Nijeriya a hali na rashin tabbas a kan man da aka kwashe makwanni ana fuskantar ƙarancinsa, wanda dama aka danganta da alamu na sake fuskantar ƙari. A ranar Talata ne sabuwar Hukumar kula da harkokin Sarrafa man fetur da tacewa da sufuri ta Nijeriya wato ‘Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority’ ta…
Read More
Vision FM: BON ta buƙaci NBC ta sassauta hukuncinta

Vision FM: BON ta buƙaci NBC ta sassauta hukuncinta

Daga BASHIR ISAH Hukumar gidajen rediyo da talabijin ta ƙasa (BON) ta ce, matakin da NBC ta ɗauka a kan tashar Vision FM, na ƙaƙaba mata harajin Naira miliyan biyar tare da dakatar mata da shirin 'Idon Mikiya' na tsawon wata shida ya yi tsauri da yawa. BON ta bayyana haka ne cikin wasiƙar da ta aike wa NBC game da matakin nata a kan Vision FM mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2022 da kuma sa hannun sakatarenta, Dr. Yemisi Bamgbose. BON na mai ra'ayin cewa ɗaukar irin wannan tsattsauran mataki kan wata tasha ka iya zama…
Read More
Namiji mai tsafta

Namiji mai tsafta

Daga AISHA ASAS A lokacin da mace ta zama ƙazama, za ka ji ana tsorata ta da cewar, ba za ta samu mijin aure ba. Amma duk ƙazantar namiji sai ka ji ana cewa, ya dai nemi kuɗi, ba zai rasa matar aure ba. Abin tambaya, shin su matan ba sa duba tsafta a cikin rukunan zaɓinsu ga aure? Ko ita mace ba ta buƙatar namiji mai tsafta wurin samun nutsuwa a zaman aure? Shafin iyali na wannan sati zai tattauna kan wannan matsala tare da jin ra’ayoyin wasu mata akan wannan maudu'i. Kasancewar mata na da mabanbantan ra’ayi kan…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Shugaban Hukumar Kwastom), Kanar Hamid Ali

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Shugaban Hukumar Kwastom), Kanar Hamid Ali

Daga NAFI'U SALISU Yin kyakkyawan bincike ta hanyar da ta dace da kuma gani da ido, su ne abubuwan da suke tabbatar da abinda yake wakana a cikin al’umma, ko sun yi ƙorafi ko ba su yi ba. Tun bayan ɗarewar s'Shugaba Muhammadu Buhari kan ƙaragar mulkin ƙasar Nijeriya, an ga yadda jami’an hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastom) suka yawaita a manya da ƙananan titunan ƙasar. Abinda  a zahirance ke nuna manufar barbaza su a ko’ina shi ne, don su daƙile ayyukan fasa-ƙwauri na kayayyakin da Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari ta hana shigowa da su cikin ƙasar nan ko…
Read More
Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance

Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance

Sharhi daga LUBABATU LEI Jama’a, shin me za ku ce game da ma’anar gudanar da gasar wasanni ta Olympics? Yin takara don neman cin lambobi ne? Babu shakka, wannan wani ɓangare ne na gasar, amma ba shi ke nan ba. ‘Yan kwanaki suka rage za a kawo ƙarshen gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ke gudana a nan birnin Beijing. A cikin kwanakin da suka gabata, yadda ‘yan wasan daga ƙasa da ƙasa suka ƙoƙarta matuƙa, don cimma ƙarin nasarori a yayin gasar ya burge mu ainun, sai dai baya ga haka, yadda ‘yan wasan suke cuɗanya da juna…
Read More
Yawan jarin wajen da aka zuba a ƙasar Sin ya ƙaru da kaso 11.6 a Janairu

Yawan jarin wajen da aka zuba a ƙasar Sin ya ƙaru da kaso 11.6 a Janairu

Daga CRI HAUSA Ƙididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar Sin ta fitar ya yi nuni da cewa, a watan Janairun shekarar 2022, yawan jarin waje da aka zuba a ƙasar Sin ya kai kuɗin Sin yuan biliyan 102.28 kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 15.84, adadin da ya ƙaru da kashi 11.6 bisa na makamancin lokacin bara. Idan kuma an yi nazari, za a gane cewa, jarin da ƙasashen da suka amsa shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya da ma ƙasashen ƙungiyar ASEAN suka zuba ya ƙaru da kimanin kashi 30 cikin ɗari. A game da wannan, Mista Zhang Jianping, darektan cibiyar…
Read More
Babban masanin aikin jaridar Nijeriya ya buƙaci ƙasarsa ta yi koyi da Sin

Babban masanin aikin jaridar Nijeriya ya buƙaci ƙasarsa ta yi koyi da Sin

Daga CRI HAUSA A ranar 15 ga watan Fabrairun 2022, jaridar Leadership ta Nijeriya ta wallafa wani sharhi da sanannen mai sharhi na Nijeriya Ray Morphy, ya rubuta, mai taken, “Ƙasar Sin darasi ne da ya kamata Nijeriya ta yi koyi", inda ya bayyana cewa, ƙasar Sin ta yi nasarar fita daga ƙangin talauci da koma bayan ci gaba a cikin wasu gwamman shekaru ‘yan kaɗan. A cikin ƙanƙanin lokaci Sin ta cimma gagaruman nasarori na ban mamaki. Nasarorin da ƙasar Sin ta samu ya nuna cewa, muddin shugabanni suna da burika masu tasiri, tabbas ne za a samu gagarumin…
Read More
Yunƙurin siyasantar da sha’anin wasanni ba zai taɓa yin nasara ba

Yunƙurin siyasantar da sha’anin wasanni ba zai taɓa yin nasara ba

Daga SAMINU HASSAN Kafin buɗe gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing dake gudana yanzu haka, gwamnatin Amurka ta shafe tsawon lokaci tana yi wa Sin matsin lamba, tare da ƙoƙarin amfani da lokacin gudanar gasar ta Olympics, a matsayin wani makami na siyasa, don sarrafa akalar ƙawayenta su juya wa ƙasar Sin baya, inda Amurka ta sha fakewa da batun kare haƙƙin bil adama, a yunƙurinta na cimma wannan mummunar manufa. Bisa hakan ne ma, ’yan siyasar Amurka suka ayyana ƙaurace wa gasar ta birnin Beijing, a matsayin wani mataki na matsin lambar diflomasiyya. To sai dai…
Read More