Editor

9513 Posts
‘Yan sanda sun damƙe masu safarar sassan jikin mutum a Kwara

‘Yan sanda sun damƙe masu safarar sassan jikin mutum a Kwara

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta ce, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da safarar sassan jikin mutum a jihar. Rundunar ta ce, sakamakon matsawa da ta yi da bincike kan ɓacewar wasu 'yan mata, a nan ta gano Femi Adeniji da Shittu Abdulmalik a matsayin masu safarar sassan jikin mutum ta kuma kama su. Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a, SP Okasanmi Ajayi (anipr), runduna ta ce ba za ta lamunci ci gaba da aukuwar miyagun ayyuka ba a jihar Kwara, don haka ta shawarci maɓarnata a…
Read More
Jiki da jini (2)

Jiki da jini (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa na Jikin Ɗan Adam, wanda ya ke zayyano muku bayanai game da duniyar gangar jikin bil adama, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda jikinku ya ke aiki, don kula da lafiyarku da rayuwarku ta yadda za ku iya sarrafa shi gwargwadon yadda ya halitta mu. Kamar yadda na faɗa, shi jiki koyaushe cikin aiki ya ke. Hatta lokacin da muke zaune muna hutawa, da lokacinda muke bacci, kiki baya daina aiki. Sai…
Read More
Ƙarya ita ce musabbabin yawan mutuwar aure (1)

Ƙarya ita ce musabbabin yawan mutuwar aure (1)

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Ƙarya fure take… Wannan karin maganar dai ta daɗe tana yawo, Kuma gaskiya ne komai daren daɗewar ƙarya, gaskiya na tafe.Ƙarya ce yanzu ta yi yawa cikin duniyar nan. Babu yara, babu manya, kowa so yake ya yi gwaninta ga ɗanuwan zamansa. Zawarci:Idan an ambaci wannan kalmar an san me take nufi. Saboda yawan mutuwar aure yanzu da ya yi yawa. zawarawa sun cika gari, ga auren suna so amma ƙarya ta yi wa masu neman auren yawa. Sai sun ƙyalla sun ga mai maiƙo, kuma an tabbata daga inda ta fito akwai maiƙo, sai su…
Read More
Da yawan magidanta a Nijeriya ba su ne mahaifan ‘ya’yansu ba – Masanin DNA

Da yawan magidanta a Nijeriya ba su ne mahaifan ‘ya’yansu ba – Masanin DNA

Daga BASHIR ISAH Binciken masana kimiyyar ƙwayar halitta (DNA) a Nijeriya ya nuna cewa, magidanta da dama a ƙasar ba su ne mahaifa na asali na 'ya'yan da ke gabansu ba alhali ba su san da haka ba. Alƙaluman masanan sun nuna daga gwajin DNA da ake gudanarwa, akan tarar 6 daga cikin kowane yara 10 daga aka bincike su mahaifin da suke ƙarƙashinsa ba shi ne ya haife su ba, wato dai 'ya'yan wani ne ko wasu ne can daban. Abiodun Salami ƙwararre ne a fagen sanin kimiyyar halitta daga jihar Legas, ya bayyana cewa kusan kashi 60 cikin…
Read More
Martabar aikin jarida da ƙalubalensa a yau

Martabar aikin jarida da ƙalubalensa a yau

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wata muhawara ta tashi a makon da ya gabata dangane da wani batu da ya harzuƙa wasu ‘yan jarida na Arewa, sakamakon yadda shirin wasan kwaikwayo na talabijin mai dogon zango na LABARINA zango na 3 fitowa ta goma sha ɗaya, ya nuna yadda aka bai wa wani ɗan jarida abin hasafi don ya yi kuɗin mota, bayan wata hira da ya yi da wani a cikin shirin. Wannan fita da aka nuna ta hassala mutane da dama, musamman ‘yan jarida, da suka riƙa bayyana mabambantan ra'ayoyi kan dacewa ko rashin dacewar abin da aka nuna…
Read More
Dalilin da ya sa muke yi wa Gwamnatin Filato zanga-zanga – Ƙungiyar Ɗalibai

Dalilin da ya sa muke yi wa Gwamnatin Filato zanga-zanga – Ƙungiyar Ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne, ɗaliban jihar Filato na Kwalejin Fasaha ta Barkin- Ladi suka gudanar da wata zanga- zangar lumana don nuna ƙin jininsu a kan yadda hukumar gudanarwar makarantar take yin watsi da shakulatin ɓangaro a kan al'amuran ilimi abin da suka ce yana kawo musu tasgaro a harkar karatunsu. A cewar ɗaliban saboda sakacin hukumar gudanarwar a yanzu haka sun biya kuɗin shekara uku cur, a matsayin kuɗin zangon karatu guda kacal! A cewar wani shaidar gani da ido, kuma wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, ya bayyana cewa, a yayin…
Read More
Masarutar Kontagora ta yi sabon sarki

Masarutar Kontagora ta yi sabon sarki

Daga BASHIR ISAH Kawo yanzu, Masarautar Kontagora a jihar Neja ta samu sabon sarki da zai ci gaba da jan ragamar harkokinta. Muhammadu Barau Mu’azu shi ne wanda aka zaɓa daga jerin waɗanda suka nuna sha'awarsu ta zama sarki a matsayin magajin marigayi Alhaji Sa'idu Namaska. MANHAJA ta kalato cewa Muhammadu Barau Muazu babban ɗan kasuwa ne kuma jikan Sarkin Sudan na 5, wato Alhaji Muazu Ibrahim, wanda ya yi mulki daga 1961 zuwa 1974. An zaɓi Muhammadu Barau Muazu a matsayin sabon Sarkin Kontagora ne biyo bayan rasuwar tsohon sarki Sa'idu Namaska bayan da ya shafe shekara 47 kan…
Read More
Ko kun san jihar Kano tana nan fiye da shekara 2000?

Ko kun san jihar Kano tana nan fiye da shekara 2000?

Daga MAHD M. MUHAMMAD Kano, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, garin da a wannan shekara (2021) ya kai kimanin shekaru dubu biyu da goma sha bakwai (999 zuwa 2021). Gari ne da ya fara daga sansanin mafarauta a mafi shaharar ruwayoyi, har ya zama katafaren birni sannan ya rikiɗe ya koma masaurauta, sannan ya koma lardi, daga bisani kuma ya zama Jiha mafi yawan jama’a a duk faɗin Ƙasar Nijeriya. Wannan Jiha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha shida daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2021. Akwai gurare masu daɗaɗɗen tarihi a…
Read More
Kwalara ta halaka mutane 100 a Neja

Kwalara ta halaka mutane 100 a Neja

Daga IBRAHIM HAMISU Gwamnatin Jihar Neja ta ce fiye da mutane 100 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar annobar amai da gudawa cikin watanni huɗu. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Muhammad Makunsidi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar da ta gabata a Minna babban birnin jihar, yayin buɗe wani taron bada horo ga 'yan jarida. Kazalika ya ce, an samu ɓarkewar annobar ne a ƙananan hukumomin jihar 25. Kwamishinan ya kuma ce, an samu wannan adadi ne tun lokacin da annobar ta ɓarke daga  watan Afrilun da ya gabata zuwa yanzu ne. Haka kuma ya bayyana yawan yin…
Read More