Editor

9513 Posts
Tashin gwauron zabin Dala

Tashin gwauron zabin Dala

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ko yaya gauro a zabi ke tashi sama?, masu zabi za su iya ba mu amsa, amma a nan zan ce akan yi amfani da furucin in ana son kwatanta yadda wata haja kan zama in ta yi ɗan karen tsada. Za a fi gane batun in kai tsaye kawai a ka ce kaya sun yi matuƙar tsada. Ita dai dala takardar kuɗin Amurka ce da kuma a ke amfani da ita wajen harkokin cinikayya a duniya. A ɗan tsakanin nan a Nijeriya dala ta yi matuqar tsada in an kwatanta ta da naira ta Nijeriya.…
Read More
Mahdi Shehu ya nemi afuwar Gwamna Masari kan yaɗa bayanan bogi

Mahdi Shehu ya nemi afuwar Gwamna Masari kan yaɗa bayanan bogi

Daga BASHIR ISAH Shugaban kamfanin Dialogue Group, Muhammad Mahdi Shehu, ya miƙa ƙoƙon neman afuwa ga Gwamnan Katsina, Bello Masari kan cewa ya dubi Allah sannan ya yi masa afuwa dangane da bayanan ƙarya da ya ce ya yi ta yaɗawa a kan gwamnan da gwamnatinsa wanda suka taɓa mutunci da martabar gwamnan da ma gwamnatinsa. Shehu ya nemi afuwar Masari ne cikin wata wasiƙa da ya fitar mai ɗauke da kwanan wata, 23 ga Satumban 2021. Afuwar da Shehu ya nema ta haɗa har da ta al'ummar Jihar Katsina baki ɗaya bisa yadda ya yi ta yaɗa bayanan bogin…
Read More
Babu wani fim da ba za a iya yi a Kannywood ba’, inji Aminu Saira

Babu wani fim da ba za a iya yi a Kannywood ba’, inji Aminu Saira

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A lokacin da Darakta Aminu Saira ya ke gudanar da aikin fim din 'Labarina' a shekarun baya, mutane da dama suna xaukar vata lokacin sa kawai ya ke yi saboda yadda a ke ganin fim mai dogon zango abu ne da ba ya cikin tsarin masana'antar finafinai ta Kannywood, shi kuma ya zo ya ke yi don haka wasu ke yi masa dariya saboda ya na zuba kuxin sa ne a wajen da ba zai dawo ba. To sai bayan tsawon lokaci da shigar masana'antar wani yanayi ne a ke ganin hanyar da Daraktan ya…
Read More
Jan kunnen da NYSC ta yi wa masu digiri kan runguma sana’a

Jan kunnen da NYSC ta yi wa masu digiri kan runguma sana’a

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Hidimar Ƙasa ta Nijeriya (NYSC) a kwanakin baya ta shawarci matasa mambobinta masu aikin hikidmar ƙasa bayan kammala digirinsu na farko da su rungumi shirye-shiryen fara kasuwanci da sana’o’i daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu, don bunƙasa fasaha da ninka hanyoyin samun kuɗin shiga a gare su tare da kauce wa tsintar kai a halin zaman kashe wando bayan kammala hidimar ƙasar. Haƙiƙa wannan kira yana da matuƙar muhimmanci, idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki da kuma alƙiblar da ya ke tunkara. A wani lokacin ana alaƙanta muhimmancin…
Read More
Gwamna Matawalle ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya don taimakawa a kan sha’anin tsaro da lafiya

Gwamna Matawalle ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya don taimakawa a kan sha’anin tsaro da lafiya

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jahar Zamfara, Hon Bello Muhammad Mutawalle, ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J Mohammed a garin New York don tattaunawa a kan hanyoyin samar da agaji na gaggawa ga jahar Zamfara, mussaman a kan lamarin tsaro da bunƙasa sha'anin lafiya da ciniki a jaharsa. Gwamnan jahar Zamfara wanda tun farko ya amsa gayyatar Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya don zuwa ƙasar Amurka ya tattauna da ita a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana yanzu haka a garin New York, inda ya samu isa ofishinta tare da kwashe…
Read More
Mun gano waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin Boko Haram – Malami

Mun gano waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin Boko Haram – Malami

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta gano masu ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram da suka addabi yankin Arews-maso-gabashin ƙasar. Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da 'yan jarida a birnin New York a wajen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 76. Hadimin Malami kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata. Malami ya ce Gwamnatin Tarayya na yin bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da Nijeriya ta ci gaba da kasancewa cikin…
Read More
Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta tsame hannun ministoci daga sabuwar dokar mai

Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta tsame hannun ministoci daga sabuwar dokar mai

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aike wa da Majalisar Dattawa da wasiƙa inda ya nemi su yi wa wata sabuwar doka da suka yi ta man fetur (PIA) kwaswarima. Wadda ta ƙunshi cire ministan kuɗi da na albarkatun man fetur. A cikin ɗaya daga cikin wasiƙun wacce Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisar, Buhari ya buƙaci a yi garambawul ga dokar ta PIA, sannan kuma a cire ministan kuɗi da na albarkatun man fetur daga kwamitin na Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPC). Inda shugaban shi…
Read More
Buhari da Badaru sun jajanta kan rasuwar Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir

Buhari da Badaru sun jajanta kan rasuwar Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulƙadir

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, sun nuna alhininsu da kuma jajantawa dangane da rasuwar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir. Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya fitar Buhari ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin nagartattun sarakunan gargajiya da ake da su a faɗin Nijeriya, waɗanda suka janyo wa harkar sarauta martaba. Buhari ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ya yi wa talakawansa hidima da gaskiya ba tare da nuna son-kai ba, wanda kuma masarautarsa ba za ta taɓa mancewa da shi ba. Haka nan, Shugaban…
Read More
Shirin N-Power: Gwamnati ta fara biyan bashi ga mutum 14,021 ‘yan kashi na ‘A’ da ‘B’

Shirin N-Power: Gwamnati ta fara biyan bashi ga mutum 14,021 ‘yan kashi na ‘A’ da ‘B’

Daga WAKILIN MU Ma'aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana cewa a yanzu ta fara yin biyan ƙarshe na bashin da ya rage ga masu cin moriyar shirin tallafi na N-Power kashi na 'A' da 'B' su 14,021. Hakan ya biyo bayan kammala warware 'yar mishkilar da aka samu a tsarin da ake amfani da shi wajen tattara bayanan biyan kuɗin. Babban Sakataren ma'aikatar, Alhaji Bashir Nura Alƙali, shi ne ya bayyana haka a cikin wata takarda ga manema labarai da ya saki a Abuja a madadin ministar ma'aikatar, wato Hajiya Sadiya Umar Farouq. Alƙali ya…
Read More
An dakatar da rajistar masu zaɓe a Jihar Bauchi

An dakatar da rajistar masu zaɓe a Jihar Bauchi

Daga WAKILIN MU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ɗage aikin rajistar masu zaɓe da ake yi a Jihar Bauchi. Wannan bayanin ya ba ƙunshe ne a sanarwar da shugaban wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai na INEC a jihar, Alhaji Adamu Gujungu, ya bayar a ranar Litinin a Bauchi. Gujungu ya ce dakatar da aikin, wanda na wani taƙaitaccen lokaci ne, zai fara aiki daga ranar 21 ga Satumba, domin a samu damar kafe rajistar masu zaɓe da aka fara yi. Ya ce ita wannan rajista da aka yiza a kafe ta ne a hedikwatar hukumar da…
Read More