26
Sep
Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu haka dai wani ɗan damfara wanda ya wanke wani mutum mai neman ku]i har zunzurutun Naira miliyan 16 ya fa]a komar hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC. Hukumar EFCC ɗin ta yankin garin Maiduguri ta samu nasarar damƙe wani wanda ya yi ikirarin shi boka ne, Mohammed Ibrahim, da kuma abokin aikinsa, a kan zargin wankiyar Naira miliyan sha shida ga Mohammed Gaji. Muhammad Ibrahim da Ibrahim Abubakar ana zargin su ne da amsar waɗancan maƙudan kuɗaɗe daga Muhammad a matsayin sadaka don a…
