29
Sep
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ministan harkokin yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio sun zagi junansu a kan siyasar jam’iyya a wani taron da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya halarta. An gudanar da taron ne don bikin ƙaddamar da sashin kare ‘yan sandan Nijeriya na Muhammadu Buhari a hukumance wanda ya ƙunshi gidaje 68 da sauran kayayyakin aiki da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) ta gina a Fatakwal, jihar Ribas. Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osibanjo ne ya wakilci Buhari a wurin taron da mahalartansa suka haɗa da Wike, Akpabio, ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Maigari…
