Editor

9513 Posts
Kafa dokar hana kiwo barkatai da cikas da ke ciki

Kafa dokar hana kiwo barkatai da cikas da ke ciki

Kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi gargaɗi game da siyasantar da rigimar hana kiwo a fili, inda ya mayar da martini kan wannan doka da cewa, ba kafa dokar ba ne abu mai muhimmanci, aiwatar da dokar ne ba zai yiwu ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Talata bayan wata ganawa da jami’an jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, Gwamna El-Rufai ya ce, duk da cewa akwai buƙatar makiyaya su daina yawo da dabbobi kamar yadda suka saba, mafita ba shi ba ne kafa dokokin…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yunwa a Keffi

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yunwa a Keffi

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin Ma'aikatar Agaji, Jinƙai da Kyautata Rayuwar 'Yan Ƙasa, ta ƙaddamar da shiri na musamman kan yaƙi da yunwa mai taken 'Project Zero Hunger' a ƙaramar hukumar Keffi, jihar Nasarawa. Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a ƙofar fadar masarautar Keffi a ranar Alhamis, tare da raba kayayyakin masarufi ga mutum sama da ɗari, maza da mata. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da;shinkafa, wake man girki, magi, tocila, omo, atampa, sabulai da sauransu, wanda aka kimtsa su cikin wani akwatin roba na musamman. Da yake jawabi a madadin Hon. Kwamishina Iman Sulaiman Ibrahim wadda…
Read More
Janar Yahaya ya buƙaci kyautata hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula

Janar Yahaya ya buƙaci kyautata hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula

Babban Hafsan Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yi kira da a samar da faɗaɗɗen tsari na hulɗa tsakanin soji da fararen hula domin inganta kundin tsarin hulɗa tsakanin sojoji da fararen hula da masu ruwa da tsaki a Najeriya. Yahaya ya yi wannan kira ne yayin gabatar da lacca ga mahalarta darasi na 43 na cibiyar koyar da dabaru da siyasa na tarayya da ke Kuru, Jos babban birnin jihar Filato. Jami'in ya bayyana cewa, rundunonin sojin ƙasa na aikin ƙirƙiro dangantaka mai ƙarfi domin ƙara kyautata hulɗa domin samun nasara wajen yaƙi da ta'addanci. Daga nan,…
Read More
Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda

Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda

Daga AMINA YUSUF ALI Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana 'yan fashi da ɓata-garin dake daji da suka addabi yankin arewacin ƙasar a matsayin 'yan ta'adda, tare da ƙaddamar da yaƙi a kansu. 'Yan majalisar sun bayyana haka ne a yayin zaman majalisar a ranar Larabar nan da ta gabata. Sannan sun ƙara da cewa, ya kamata kuma a ba da umarni jami'an tsaro su kama su, a gurfanar da su, tare da gaggauta yi musu hukuncin da ya dace da su. Wannan batu yana ƙunshe ne a cikin wani wani ƙudiri da ɗaya daga cikin…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta fara ba wa maza hutun jego na kwanaki 14

Gwamnatin Tarayya za ta fara ba wa maza hutun jego na kwanaki 14

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Larabar nan a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ƙarƙashin shugabancin Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Yemi Osinbajo, sun amince da dokar da ta ba da dama ga iyaye maza waɗanda iyalansu suka haihu, hutun jego domin su ma su samu su ƙara shaƙuwa da jaririn da aka haifa ko ɗan goyon da aka ɗauko. Shugabar Ma'aikata na Tarayya, Dakta Folasade Yemi - Esan ce ta bayyana hakan a ƙarshen zaman majalisar zartarwar wanda ake gudanar da shi a ƙarshen kowane mako. Wanda aka gudanar da shi a ɗakin taro na Matar Shugaban Ƙasa…
Read More
‘Yan bindiga sun sace tsohon Ministan Abuja

‘Yan bindiga sun sace tsohon Ministan Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Sanata Solomon Ewuga, a jihar Filato. Sace shi na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yi wa Dakta Chike Akunyili, mijin tsohon Ministar Yaɗa Labarai kuma Babbar Daraktar NAFDAG, Farfesa Dora Akunyili.
Read More
Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da rufe hanyoyin sadarwa

Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da rufe hanyoyin sadarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da rufe ayyukan sadarwa a wasu sassan jihar saboda ayyukan sojoji na fatattakar ‘yan bindiga a yankunan. Kwamishinan ya kuma ba da sanarwar haramta amfani da baburan haya na tsawon wata uku daga ranar Alhamis 30 ga Satumba 2021. A yanzu adaidaita sahu za su fara aiki daga ƙarfe 6 na safe zuwa 7 na yamma yayin da duk motocin haya da ke aiki a jihar za a yi musu fenti da launin rawaya da kore. Waɗannan da sauran su…
Read More
`Yan bindiga sun kashe mijin Marigayiya Dora Akunyili

`Yan bindiga sun kashe mijin Marigayiya Dora Akunyili

Daga SANI AHMAD GIWA Wasu `yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yaɗa Labarai, Farfesa Dora Akunyili. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun far masa ne a yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba a Jihar Anambara. Kodayake zuwa haɗa wannan labari babu wani cikakken bayani daga ɓangaren jami'an tsaro game da al'amarin. Amma wani rahoton Jaridar The Nation ya ce an kashe marigayin ne a Umuoji da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambara da yammacin ranar Talata. Wata majiya ta kusa da iyalan Marigayin…
Read More
‘Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara

‘Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara

Sarkin Kagara, Alh. Ahmad Garba Gunna Daga BASHIR ISAH Bayanan da MANHAJA ta kalato daga Jihar Neja sun nuna 'yan bindiga sun kai hari a garin Kagara, hedikwatar ƙaramar hukumar Rafi inda suka shiga har fadar masarautar Kagara. A jiya Talata wannan al'amari ya faru, inda bayanai suka tabbatar da 'yan bindigar sun kai harin ne a kan babura da yawansu ya kai 20 inda kowane babur ke ɗauke da mutum uku. Majiyar jaridar Thisday ta bayyana cewa, an yi sa'a lokacin da aka kai harin Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba Gunna, ba ya gari, ya tafi Minna halartar wani…
Read More
Rashin sha’awar iyali da dalilansu

Rashin sha’awar iyali da dalilansu

Daga BILKISU YUSUF ALI Tambaya:Malama Ina da tambaya. Wai shin me yake hana sha’awar iyali shekararmu biyar da matata amma daga baya sai na ji sam ba na sha’awarta. Amsa:Wannan matsale ce da abu biyu yake kawo ta. Na farko dai akwai yanayin zamantakewa inda kuma na biyun zai iya kasancewa rashin lafiya ce ke haifarwa. Katsewar sha’awar miji ga matarsa ko mace da mijinta yana hana zama lafiya a zamantakewar aure sannan ya hana al’amuran rayuwa na yau da gobe gudana, saboda al’amuran aure kaso ma fi rinjaye ya ta’allaƙa ne a kan sha’awa tsakanin iyali. Amma kafin mu…
Read More