Editor

9513 Posts
Tsaro: Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku

Tsaro: Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku ga Rundunar Sojan Sama (NAF). Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Alhamis Buhari ya miƙa jiragen ga rundunar a sansanin sojojin da ke Makurɗi a jihar Binuwai, yayin bikin cikar rundunar shekaru 57 da kafuwa. Buhari wanda Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya wakilce shi wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki ya ce, jiragen yaƙin samfurin JF-17 da aka miƙa wa rundunar hakan zai ƙarfafa wa NAF matuƙa wajen ci gaba da fatattakar 'yan ta'adda da ta'addanci haɗa da manyan laifukan da ƙasa ke…
Read More
An gano gawar ɗan shekara uku a cikin rijiya a Kano

An gano gawar ɗan shekara uku a cikin rijiya a Kano

Daga AISHA ASAS Jami'an kwana-kwana a jihar Kano sun gano gawar wani yaro ɗan shekara uku wanda ya faɗa a rijiya a garin Gaida da ke yankin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar. Kamfani Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa, Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kwana-kwana na Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan a Kano. Abdullahi ya ce wannan al'amari ya auku ne da yammacin Larabar da ta gabata. A cewarsa, da misalin ƙarfe 4 na yamma suka samu labari kan faɗawa rijiya da yaron ya yi, inda cikin gaggawa suka tura jami'ansu…
Read More
An yi jana’izar mahaifin Sanata Sani Musa a Minna

An yi jana’izar mahaifin Sanata Sani Musa a Minna

Daga BASHIR ISAH Jama'a daga sassan Nijeriya suka haɗu a Minna, babban birnin jihar Neja domin jana'izar mahaifin Sanata Mohammed Sani Musa. An gudanar da sallar jana'izar marigayi Alhaji Musa Tanko (Iyan Minna) ne a fadar Sarkin Minna, Dr Umar Farouq Bahago a Larabar da ta gabata. Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar har da Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsallami A. Abubakar, wanda ya bayyana marigayin a matsayin tsayayyen mutum wanda rasuwarsa babban rashi ne ga al'umma. A nasa ɓangaren Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, wanda ya jagoranci manyan baƙin da suka halarci jana'izar, ya ce marigayi…
Read More
NLC ta dakatar da yajin aikin da ta soma a Kaduna

NLC ta dakatar da yajin aikin da ta soma a Kaduna

Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna, ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwana biyar da ta soma a Litinin da ta gabata. NLC ta ɗauki matakin dakatar da yajin aikin ne domin amsa gayyatar da Gwamnatin Tarayya ta yi mata ya zuwa Alhamis. Shugaban NLC na ƙasa, Comrade Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani taron gaggawa da suka yi a Kaduna a Laraba.
Read More
Zanga-zangar Kaduna: Matan da El-Rufai ya ɗauko haya sun yi ƙorafin rashin biyan su haƙƙinsu, cewar NLC

Zanga-zangar Kaduna: Matan da El-Rufai ya ɗauko haya sun yi ƙorafin rashin biyan su haƙƙinsu, cewar NLC

A ranar Laraba Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna, ta shiga yini na uku a ci gaba da zanga-zanga da kuma yajin aikin kwanaki biyar da ta soma a jihar don nuna rashin yardarta kan matakin korar wasu ma'aikatan jihar da Gwamna Nasir El-Rufai ya ɗauka. Kamar yadda ta wallafa a shafinta na twita, NLC ta ce ta gano cewa Gwamna El-Rufai ya yi hayar wasu mata na musamman domin su shigo su lalata wa NLC tsarinta wanda a ƙarshe haƙarsa ta kasa cim ma ruwa. Sannan kuma matan, sun yi ƙorafin an bar su a yashe ba…
Read More
Bagudu ya karɓi baƙuncin jakadiyar Amurka a Nijeriya

Bagudu ya karɓi baƙuncin jakadiyar Amurka a Nijeriya

A ranar Laraba, Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Sanata A.A Bagudu, ya karɓi baƙuncin jakadiyar Amurka a Nijeriya, Ambasada Mary Beth Leonard, yayin ziyarar aiki da ta kai jihar. Bagudu ya karɓi baƙuwarsa ce a Fadar Gwamnantin Jihar da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Read More
Gwamna Bello ya yi rigakafin korona kashi na biyu

Gwamna Bello ya yi rigakafin korona kashi na biyu

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi allurar rigakafin korona na Oxford Astrazeneca karo na biyu. Bello ya yi rigakafin ne yayin ƙaddamar da shirin rigakafin karona karo na biyu a jiharsa. A lokacin ƙaddamar da shirin wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, an ga mataimakin gwamnan da sauran mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar su ma sun yi tasu allurar karo na biyu-biyu. Da yake jawabi jim kaɗan bayan da ya yi allurar, Gwamna Sani Bello ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama'ar jiharsa suka bada haɗin kai yayin rigakafin zubin farko.…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sa baki kan rikicin El-Rufai da NLC

Gwamnatin Tarayya ta sa baki kan rikicin El-Rufai da NLC

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta sa baki cikin rashin jituwan da ke gudana tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa. Ƙungiyar Ƙwadagon ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduns da takwararta TUC sun shiga yajin aiki ne na kwanaki biyar da kuma zanga-zanga kan sallamar ma'aikata 7,000 da gwamnatin Kaduna ta yi. A jawabin da ya yi a madadin Gwamnatin Tarayya a Talatar da ta gabata, Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, ya yi kira ga ɓangarori biyu da su yi sulhu da juna. A cewar Ngige, "Mun san abin da ke faruwa a jihar Kaduna. Matsalar ƙwadago ne kuma…
Read More
Jami’an EFCC sun sabunta rantsuwar aiki

Jami’an EFCC sun sabunta rantsuwar aiki

Daga FATUHU MUSTAPHA A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi wajen gyara zamanta, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta bai wa jami'anta damar sabunta rantsuwar aiki a Abuja a Talatar da ta gabata. Yayin shan rantsuwar, jami'an su yi alƙawarin za su yi aiki da gaskiya ba tare da ha'inci ba. Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, shi ne wanda ya jagoranci shan rantsuwar da ma'aikatan suka yi daidai da dokar aiki ta hukumar. Bawa Bayanan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na hukumar suna nuna taron shan rantsuwar ya gudana…
Read More