Editor

9513 Posts
Safarar Ƙwayoyi: NDLEA ta kama ƙosai da aka yi da wiwi a oyo

Safarar Ƙwayoyi: NDLEA ta kama ƙosai da aka yi da wiwi a oyo

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Yaƙi da Tu'ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen jihar Oyo, ta kama tabar wiwi da aka sarrafa shi kamar ƙosai don ɓadda kama a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da ke jihar. Shugabar NDLEA a jihar Oyo, Mrs Josephine Obi, ita ce ta bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Ibadan a Talatar da ta gabata. Haka nan, shugabar ta ce sun cafke wani ɗan aike ɗauke da kek ɗin bikin ranar haihuwa wanda aka cusa tabar wiwi mai nauyin 1.2kg a cikinsa. Ta ce hanyoyi da dabarun da masu…
Read More
HOTO: Buhari da wasu sun yi tsayuwar ‘WAZOBIA’

HOTO: Buhari da wasu sun yi tsayuwar ‘WAZOBIA’

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugabar Cibiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka (AFDB), Akinwumi Adesina, sun yi tsayuwar ɗaukar hoto mai zubin 'WAZOBIA' yayin babban taron da suka halarta a Farisa babban birnin Faransa inda aka tattauna batun da ya shafi Afirka. Duk da dai wataƙila shugabannin ba su kawo haka a zukatansu ba yayin ɗaukar hoton, amma tsayuwar da suka yi ta fassara manyan ƙabilun nan uku da Nijeriya ke da su, wato WAZOBIA, ma'ana Yoruba, Hausa da Kuma Igbo. Idan aka kalli hoton daga hagu, Adesina shi ne na farko inda…
Read More
Zambar kuɗaɗe: Nijeriya ta karɓi milyan £4.2 na kuɗaɗen da Ibori ya wawushe – Malami

Zambar kuɗaɗe: Nijeriya ta karɓi milyan £4.2 na kuɗaɗen da Ibori ya wawushe – Malami

Daga BASHIR ISAH Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya tabbatar cewa Gwamnatin Tarayya ta karɓi maƙudan kuɗaɗe Fan milyan £4,214,017.66 na kuɗaɗen sata da aka danganta su da iyalan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori. Mai taimaka wa ministan kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Umar Gwandu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Talata. Bayanan Gwandu sun nuna an rigaya an saka kuɗaɗen a kwatankwacin Naira cikin asusun Gwamnantin Tarayya tun a 10 ga Mayu, 2021. Haka nan cewa Minista Malami ya rattaba hannu a takardar yarjejeniyar karɓar kuɗaɗen…
Read More
INEC: Mu na ci gaba da aiki da lokutan da mu ka tsara na rajistar masu zaɓe

INEC: Mu na ci gaba da aiki da lokutan da mu ka tsara na rajistar masu zaɓe

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan kan bakan ta na yin aiki da jadawalin da ta tsara na ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe daga ranar 28 ga Yuni a duk faɗin ƙasar nan. Mista Festus Okoye, wanda shi ne Babban Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai, shi ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja ran Lahadi. Okoye ya ce hukumar na nan kan bakan ta, musamman da yake ta samu gidan yana…
Read More
Zaɓen 2023: Ban bayyana ƙudirina na takarar shugaban ƙasa ba – Osinbajo

Zaɓen 2023: Ban bayyana ƙudirina na takarar shugaban ƙasa ba – Osinbajo

Daga FATUHU MUSTAPHA Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, ya ce shi dai bai bayyana ra'ayinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023. Yana mai cewa ɗaga wanna zance a yanzu neman karkatar da hankali ne kawai. Sanarwa da mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya fitar a Litinin da ta gabata, ta nuna ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba shi da alaƙa da  wani gangamin goyon bayan tsayawa takara da aka shirya ta intanet. Sanarwar ta ce, "Hankalin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya kai ga wani shafin intanet 'supportosinbajo.ng' wanda ke kira ga 'yan Nijeriya da su zo a haɗa…
Read More
Zabtare Ma’aikata: Ba gudu ba ja da baya, cewar El-Rufai

Zabtare Ma’aikata: Ba gudu ba ja da baya, cewar El-Rufai

Sufeto Janar ya bada umarnin tura ƙarin dakaru zuwa Kaduna Daga AISHA ASAS Sakamakon zanga-zangar lumana da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta gudanar a Litinin da ta gabata da kuma soma yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar, ya sa harkokin kasuwanci sun tsaya cak a jihar. NLC ta ɗauki wannan mataki ne domin ƙalubalantar korar ma'aikata su 4,000 da Gwamna Nasir el-Rufai ya yi kwanan nan. Gwmna El-Rufai ya ce game da matakin rage yawan ma'aikata da ya ɗauka ba gudu ba ja da baya, tare da cewa matakin yajin aikin NLC ba zai sanya gwamnatin…
Read More
NFF ta taya Okala murnar cika shekara 70 da haihuwa

NFF ta taya Okala murnar cika shekara 70 da haihuwa

Daga FATUHU MUSTAPHA Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta aika da saƙon taya murna ga tsohon mai tsaron ragar Nijeriya, Emmanuel Okala, wanda ya cika shekara 70 da haihuwa a ranar Litinin 17, Mayu, 2021. Babban Sakataren NFF, Dr Mohammed Sanusi, ya yaba wa tsohon ɗan wasan bisa irin rawar da ya taka wa Nijeriya a fagen wasan ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa da kuma a matakin ƙungiyar Rangers ta Enugu. Ya ce, "Ba mu mance irin ƙoƙarin da Emmanuel Okala ya yi ba a zamaninsa inda ya yi wa Nijeriya hidima gwargwadon hali. Muna yi masa fatan alheri,…
Read More
APC ta musanta fitar da jadawalin babban taronta

APC ta musanta fitar da jadawalin babban taronta

Daga UMAR M. GOMBE Jam'iyyar APC ta ce ba ta shirya gudanar da babban taronta ba kamar yadda ta ga wasu kafofin yaɗa labarai sun yaɗa. Jam'iyyar ta ce rahoton taron nata da aka yaɗa shiryayyen al'amari ne wanda  aka tsara domin kitsa bahaguwar fahimta a cikin al'umma. Sanarwar da ta fito daga hannun sakataren tsare-tsren babban taron jam'iyyar, John James Akpanudoedehe, ta nuna rahoton shiri ne kawai na masu neman ci da siyasa. Sanarwar ta ce, "An ja hankalinmu kan wani shiryayyen labari da aka yi ta yaɗawa a wasu kafafen yaɗa labarai dangane da cewa APC ta shirya…
Read More