03
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙaramin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya shirya zaman addu'o'i na musamman domin neman nasarar Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027 da ke tafe da zaman lafiya da kuma ci-gaban ƙasa. An gudanar da taron addu'o'in ne a babban Masallacin Maradun da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara, wanda ya haɗa sarakunan gargajiya, malamai da dubban al'ummar Musulmi. A yayin jagorantar addu'ar, Sarkin Maradun, Muhammad Garba Tambari ya ce addu'a wajibi ce ga shugabanni da ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada cewa babu wani alheri da ke tabbata ba tare da taimakon…
