Babaji

5684 Posts

Kano: Matan APC sun kimtsa tunkarar zaɓen 2027 a Bichi

A bayan ƙaddamar da jiga-jigan 'yan takarar wakilan al'umma ƙarƙashin tutar Jam'yyar APC a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, Shugabar Matan Jam'iyyar APCn ta yankin, Hajiya Rahana Idris ta jaddada alƙibla da ɗaukacin matan yankin suka dosa a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027. Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito, Shugabar matan, ta ƙarfafa aniyarsu ta hanyar ci gaba da bada haɗin kai da goyon bayan dukkan 'yan takarar jam'iyyar tasu na yankin, domin cigaba da inganta rayuwar al'ummar garin Bichi ta fanni lafiya, ilimi, sana'a da kuma ayyukan raya ƙasa domin haɓaka…
Read More

Kano: Bichi za ta rabauta da ginin zamani na makarantu huɗu

A fannin cigaba da ɗora ayyukan alheri na raya ƙasa da gina al'umma dake ta wanzuwa a Ƙaramar Hukumar Bichi ƙarƙashin wakilcin Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar yankin, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya saka ɗambar sabunta ginin wasu makarantu huɗu a garin Bichi. Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito, marakarantun sun haɗa da; GASS Sabon Layi, Ciranci Science and Mathematics Primary School, Makarantar Firamare ta Ɗanzabuwa da Makarantar Firamare ta Saye, kuma dukkan waɗannan makarantu tuni aka fara gudanar da aikin. Makarantun za su samu ingantaccen ginin zamani mai kyau da ƙarko da kuma…
Read More

‘Yan bindiga sun sace makamai bayan harin ofishin jami’an shige da fice a Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Oyo, ta ce ta fara bincike akan wani kutse da aka yi wa ofishin Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da ke garin Ogbomoso a daren ranar Talata wayewar Laraba, inda aka yi awon-gaba da makaman jami'an da ke bakin aiki. Binciken manema labarai ya nuna cewa al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ofishin hukumar da ke kan hanyar Ogbomoso zuwa Ilorin kusa da gidan man NNPC. Wata majiya ta ce, "Maharan sun farmaki ofishin ne yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin…
Read More

Gwamnatin Zamfara ta tallafa wa mata da marasa galihu miliyan ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tallafa wa sama da mata miliyan guda, 'yan mata da sauran masu ƙaramin ƙarfi a faɗin jihar. Wannan wani ɓangare ne na shirinta na tallafa wa mata na WEE da nufin inganta lamuran rayukansu na yau da kullum. Kwamishinar Harkokin Mata ta jihar, Dakta Aisha M.Z. Anka ta bayyana hakan a yayin wani taron ƙara wa juna sani na kwana uku akan shirin Inganta Rayuwar Mata a Gida na Ƙasa a Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a Karma Guest Inn, Sakkwato, ranar Talata. Dakta Aisha, wadda ta samu wakilcin…
Read More

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗaliban Polytechnic a Zamfara yayin da ɗaya ya tsira

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a Jihar Zamfara, sun yi garkuwa da ɗalibai guda bakwai na makarantar Polytechnic ta Tarayya da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda bayan sun kai hari gidansu da ke kusa da unguwar Low-Cost a cikin garin Ƙauran Namoda. Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Ƙaura ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawowar ɗaliban cikin ƙoshin lafiya. Wani dalibi mai suna Ibrahim Ahmad ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya tsere daga hannun masu garkuwar, yayin da dalibai shida…
Read More

Kotu ta ɗage sauraron ƙarar ƙalubalantar shugabancin David Mark a ADC zuwa 8 ga Yuni

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ɗage sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar akan shugabannin tsagi na jam'iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark zuwa ranar 8 ga watan Yuni. Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yi hukuncin bayan lauyan mai ƙara ya nemi ƙarin lokaci sakamakon rashin halartar lauyoyin ɓangarorin da ke neman shiga cikin shari’ar. A zaman kotun, wakilan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Independent National Electoral Commission, da kuma masu neman shiga cikin ƙarar ba su halarta ba, duk da cewa an tabbatar da cewa an aika wa INEC takardar sanarwar zaman kotun. Lauyoyin…
Read More

Tinubu zai yi jawabin Ranar Dimukraɗiyya a 12 ga Yuni

Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabi a zaman haɗin-gwiwar na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 12 ga watan Yuni, a wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 27 da dawo da mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne ya faɗi hakan yayin ƙaddamar da kwamitin ministoci da aka ɗora wa alhakin shirya bukukuwan a Abuja, inda ya a ce jawabin shugaban ƙasar zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su gudana a ranar. Ya bayyana cewa Ranar Dimukraɗiyya wata dama ce ta tunawa da sadaukarwar waɗanda suka yi gwagwarmayar dawo da mulkin dimukraɗiyya musamman…
Read More

Kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa kan harin Cocin Owo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane huɗu na ƙungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa hannu a laifin farmakin Cocin St. Francis Catholic Church da kaa ƙaddamar a ranar 5 ga watan Yunin 2022, wanda ya yi ajalin mutane 40 da raunata sama da wasu guda 100. Mai Shari'a Emeka Nwite ya gabatar da hukuncin akan Idris Abdulmalik Omeiza mai shekaru 25; Al Qasim Idris, mai 20; Jamiu Abdulmalik mai 26; da kuma Abdulhaleem Idris ɗan shekara 25, bisa laifuka tara masu alaƙa da…
Read More

Oyo: ‘Yan bindiga sun sace ‘yar uwar tsohon Ministan Lantarki Adelabu da ‘yan biyunta a Ibadan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace 'yar uwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo. Iyalan tsohon ministan kuma jigo a jam'iyyar APC ne suka tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce an yi awon-gaba da Misis Olaide John-Paul da 'yan biyunta maza masu shekara 12 ne a yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026. A cewar sanarwar da ya aike wa manema labarai, mai taimaka wa Adelabu kan harkokin yaɗa labarai, Femi Awogboro, al'amarin ya faru ne da misalinàq ƙarfe 7:30 na safe, yayin da…
Read More

Gwamnatin Tarayya na shirin gaggauta samar da gidaje yayin da Minista Darma ya ziyarci na rukunin 1,500 a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sabunta muradinta na hanzarta samar da gidaje a sassan ƙasar nan domin inganta walwalar al'ummar ƙasa a fannin zamantakewa. Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayyar Nijeriya, Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya bayyana haka yayin da ya ziyarci wani aikin gina gidaje na Renewed Hope City a Jihar Kano don samar da gidaje masu rahusa ga 'yan ƙasa ta alaƙar ɗaiɗaikun mutane da gwamnati. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara wani rukunin gidaje guda 1,500 da ake ginawa a Kano, wanda ake sa ran zai ɗauki…
Read More