Babaji

5684 Posts

Matatar Ɗangote ta ƙara adadin samar da fetur zuwa ganga 700,000 a kullum

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin matatar man Fetur ta Ɗangote ta sanar da ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai daga ganga 650,000 zuwa ganga 700,000 a kowace rana. Rahotanni sun bayyana cewa matatar ta riga ta gudanar da gwajin aiki inda ta tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a rana, abin da ya zarce ƙarfin da aka tsara mata tun farko na ganga 650,000 a kullum. A cewar matatar, hakan na nuna ingancin tsarin injiniyoyinta da kuma yadda take aiki yadda ya kamata domin wadatar da masu amfani da fetur a Nijeriya. A baya ne Mataimakin Shugaban kamfanin mai…
Read More

Borno: Sojoji sun ceto mai shayarwa, jariri da wasu daga cikin ‘yan Ngoshe da aka sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na ƙarƙashin Atisayen HAƊIN KAI (OPHK) sun ƙara kaimi wajen murƙushe ayyukan ta'addanci a shiyyar Arewa maso Gabas, bayan aun wasu nasarori da suka haɗa da ceto mutanen da aka sace gami da kuma tilasta wa 'yan ta'adda miƙa wuya. An ƙaddamar da atisayen ne a yankin Amuda, inda dakarunmu suka yi nasarar ceto wata mata mai suna Maryam Muhammad (shekara 20) da ɗanta ƙarami, Bello Muhammad, waɗanda aka yi garkuwa da su tun a ranar 3 ga watan Maris, 2026 a garin Ngoshe. Bayan tserewar da suka yi daga maboyar ta'addancin…
Read More

Tsauraran sharuɗɗan beli sun saɓa wa doka – NBA ga kotuna

Ƙungiyar Lauyoyin Ƙasa (NBA) ta nuna damuwa akan yadda wasu kotuna da jami’an tsaro ke sanya tsauraran sharuɗɗan beli da ke hana mutane da dama cin gajiyar ‘yancin da doka ta tanada a gare su. NBA ta yi kira ga kotuna da hukumomin tsaro da su sake duba tsarin bayar da beli domin tabbatar da adalci da kare haƙƙin waɗanda ake tuhuma. Shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe ya bayyana cewa yawan sanya sharuɗɗan da suka haɗa da buƙatar manyan ma’aikatan gwamnati ko masu kadarori masu tsada a matsayin masu tsaya wa wanda ake tuhuma na hana mutane da dama samun beli…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ci alwashin ceto ɗaliban Oyo da Borno da aka sace yayin da Tinubu ya tura jami’ai na musamman

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa tana ƙoƙarin ganin cewa an ceto ɗalibai da malaman da aka sace a jihohin Oyo da Borno, tana mai bayyana cewa manufarta ita ce ceto su cikin ƙoshin lafiya da kuma kawo ƙarshen ta'addanci a sassan ƙasar. A cewarta, hukumomin tsaro suna ɗaukar halastattun matakai wajen ceto waɗanda suke hannun 'yan ta'adda da tabbatar da kama masu hannu a ciki. Haka na zuwa ne yayin da al'ummar ƙasa suke cigaba da nuna damuwa akan sace kimanin ɗalibai 82 tsakanin 13 da 15 ga Mayu a Oyo…
Read More

An kusa kammala aikin kafa ‘yan sandan jihohi a dokance, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce an samu gagarumin cigaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin. Shugaban ma'aikatan fadar, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, wadda ta haɗa manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisun dokoki kan batun kafa ’yan sandan jihohi. Gbajabiamila ya ce an fara nazari da tattaunawa kan yadda za a kafa rundunar tun watanni uku zuwa huɗu da suka gabata…
Read More

‘Yan sanda sun kama wanda ya ƙirƙiri muryar Tinubu ta bogi bayan makonni

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda ta ce ta cafke wani Ifechukwu Dennis, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya ƙirƙiri murya ta fasahar AI da aka baza a kafafen sada zumunta da sunan cewa ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ce. Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a ranar Alhamis ta kafar X. A cewar Onanuga, jami'an 'yan sanda na musamman ne suka kama wanda ake zargin akan wata ɗauka ta murya da ta haddasa gagarumar cece-kuce a kafafen yaɗa labarai. "Tawagar IGP ta 'crack' ta kama Ifechukwu Dennis wanda ya samar da muryar…
Read More

Ekiti: Yadda mataimakiyar shugaban ƙaramar hukuma ta yi ƙaryar garkuwa da ita, an tura ta kurkuku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti, Grace Ogunleye ta shiga matsalar shari'a bayan an tsare ta a gidan gyaran hali na Ado-Ekiti bisa zarge-zargen kitsa makirci da garkuwa da kanta. Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Grace ne a Babbar Kotun Shari’a da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar tare da wasu mutane guda uku a ranar Laraba bayan binciken 'yan sanda akan al'amarin. Kotun ta umarci da a tsare mataimakiyar ciyaman ɗin da sauran mutanen a gidan yari har zuwa lokacin da za a sake tayar da batun nasu a gabanta.…
Read More

Ƙudirin samar da hukumar daƙile zazzaɓin cizon sauro ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta yi wa ƙudirin dokar neman kafa hukumar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro karatu na uku, lamarin da ke nuna ta kammala aikin tantance shi a hukumance. Za a samar da hukumar ne da nufin kula da bayar da kariya, kulawa da kuma kawo ƙarshen cutar, wadda ake kira da "Malaria" a Nijeriya musamman ganin yadda mutane da dama ke rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da ita a ƙasar. Sanata Ned Nwoko (Delta ta Arewa) ne ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin, wanda ya tsallake karatu na uku bayan nazari da kuma…
Read More

An jibge jami’an tsaro a Aso Rock yayin zanga-zangar su Sowore kan garkuwar makarantun Oyo da Borno

A yau Alhamis ne aka ƙara yawan jami’an tsaro a hanyoyin da ke yankin Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock a Abuja yayin da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan-adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya sanar da shirin jagorantar zanga-zanga zuwa fadar. Rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda masu yaƙi da tarzoma sun kewaye manyan ƙofofin Aso Rock, yayin da aka takaita shiga wurin ga masu katin shaidar aiki na Fadar Shugaban Ƙasa kawai. Sowore ya ce, shi da magoya bayansa za su gudanar da gangami daga Eagle Square zuwa Aso Rock domin…
Read More

Bayan tattaunawar fansar miliyan N150, ‘yan cocin EKWA biyar sun rasu a hannun ‘yan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane biyar na cocin EKWA a garin Omugo da ke Gundumar Oro Ago a Ƙaramar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara da aka yi awon-gaba da su sun rasu a hannun 'yan bindiga. Rahotanni sun bayyana cewa, ministan cocin Reberen Timothy Omole ne ya faɗi hakan a wani saƙon WhatsApp ga mambobin cocin, sannan ya kuma tabbatar wa manema labarai a yammacin ranar Laraba. Daga cikin wadansuka rasu akwiya matar faston, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole. Marigayiyar tana ɗaya daga cikin 'yan cocin guda takwas da aka sace yayin harkokinsu na ranar Lahadi, 22 ga watan…
Read More