Babaji

5698 Posts

‘Babu yunƙurin juyin mulki’: Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar da sabon saƙo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da rahotannin da ke zargin yunƙurin juyin mulki ga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tana mai jaddada biyayyar jami'an sojoji ga gwamnatin. Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare a wata hira da gidan talabijin na TVC ya ce babu wani abu mai kama da haka a ko'ina a faɗin ƙasar. Ya ce, gwamnatin ta yanzu tana goyon bayan matsayar rundunar sojoji, wadda ta musanta samun wani abu mai kama da haka a ƙasar. Ya kuma ce, rundunar sojojin tana cigaba da zama mai aikin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu daga cikin waɗanda aka yi wa afuwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Laraba aka cire sunan matar nan da aka yanke wa hukunci bayan samun ta da laifin halaka mijinta, wato Maryam Sanda daga sahun waɗanda suka samu yafiyar shugaban ƙasa, bayan da Shugaba Bola Tinubu ya amince da gyararren jaddawalin waɗanda aka yi wa afuwa da aka miƙa da fari domin aiwatarwa. Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa kisan mijinta Bilyaminu Bello, an sanya sunanta ne acikin waɗanda aka yafewa da fari, lamarin da ya haddasa cecekuce acikin al'umma. Saidai, cire ta da aka yi a yanzu ya…
Read More

‘Yan ta’adda sun yi barazanar tarwatsa Majalisar Dokoki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Wakilai ta yi ikirarin samun barazana daga ƴan ta'adda cewa za su tarwatsa Majalisar Dokoki a Birnin Tarayya Abuja. Shugaban Kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilan, Garba Muhammad ya sanar da haka a yayi taron ji ta bakin al'umma da aka yi a jiya Talata a Abuja. An shirya taron ne domin nazari akan ƙudirin samar da sashin tsaro a majalisar, wanda ya zayyano cancanta da sharuɗɗan hidima na jami'in tabbatar da doka da oda da tsaro, wato 'sergeant-at-arms'. Garba Muhammad ya bayyana cewa majalisar tana fuskantar ƙalubalen tsaro musamman ganin yadda…
Read More

Sojoji sun kai samame gidan tsohon ministan Buhari kan hannu a juyin mulki, sun kama ɗan uwansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu dakarun tsaron Nijeriya a Abuja, sun mamaye gidan tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, bisa zargin sa hannu a yunƙurin juyin mulkin da ake bincike akansa ƙarƙashin Hukumar Leƙen Asirin Soji ta DIA. A cewar jaridar SaharaReporters kamar yadda IntelRegion ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da atisayen ne a gidan Sylva da ke unguwar Maitama a birnin. Majiyoyin sun ce, wata tawagar sojoji ne ta kai samamen sakamakon samun wani bayani na sirri da ke nuna tsohon ministan yana da hannu a lamarin…
Read More

Wasu sassan Abuja za su ci gaba da kasancewa cikin duhu, inji TCN

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya sanar da cewa za a samu tsaiko yayin raba wuta a wasu yankunan birnin tarayya Abuja har na tsawon makonni biyu. Kakakin kamfanin, Ndidi Mbah ya sanar da haka a wata takarda ranar Litinin. A cewar TCN, tsaikon zai samu ne sakamakon aikin gina titina da ake yi, wanda zai faru tun daga yau Talata, 28 ga watan Oktoba zuwa Nuwamba 16. Ya ce, a yayin haka za a rasa wuta a layin Gwagwalada-Kukwaba-Apo mai nauyin kilovolt 132, wato ninki biyu na layin lantarki. Don…
Read More

Gwamnatin Trump ta hana Farfesa Wole Soyinka shiga Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump, ta soke bizar fitaccen marubuci kuma mai lambar yabo ta 'Nobel', wato Farfesa Wole Soyinka daga shiga ƙasar. Rahotanni sun bayyana cewa, an sanar da Soyinka cewa izinin shigar sa ƙasar ya ƙare ne bisa sabuwar dokar da gwamnatin Trump ta sanya wadda ta shafi wasu daga cikin fitattun mutane a duniya. Farfesa Soyinka, wanda ya shahara wajen kare ƴancin al'umma da ƙoƙarin riƙo da gaskiya, ya daɗe yana da alaƙa da ƙasar Amurka, inda ya yi aiki a da dama daga cikin jami’o’in ƙasar. Matakin ya…
Read More

Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sababbin jagororin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dattawa, inda ya nemi da ta tabbatar da naɗin sababbin shugabannin rundunonin tsaro da ya yi a kwanan nan. Takardar ta ƙunshi sunayen manyan hafsoshin da aka zaɓa domin jagorantar rundunonin soji, ƴan sanda da sauran ɓangarorin hukumomin tsaro na ƙasa. A ƴan kwanakin nan ne Tinubu ya yi wa ofisoshin jagororin tsaron garambawul ciki har da tsige Janar Christopher Musa Gwabin a babban hafsan tsaro da maye gurbinsa da Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne shugaban sojojin ƙasa gabanin haka. A cewar mai taimaka…
Read More

Sowore da lauyan Nnamdi Kanu sun shaƙi iskar ƴanci daga kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan gwagwarmayar fafutukar kare haƙƙin ɗan-adam, Omoyele Sowore tare da lauyan Nnamdi Kanu, sun samu ƴanci a yammacin jiya Litinin bayan shafe kwanaki huɗu a gidan yarin Kuje da ke Birnin Tarayya Abuja. Sowore ya bayyana haka ne ta shafinsa na X inda ya ce, ya samu fitowa daga kurkukun bayan tsare shi ba bisa doka ba na tsawon kwanaki huɗu. A makon da ya gabata aka tsare shi bayan ya halarci zaman shari'a a Kotub Majestare da ke Kuje. An ga yadda Sowore da masu goyon bayansa…
Read More

NAHCON ta buƙaci Gwamnatin Gombe ta ba hukumar alhazan jihar kuɗi gabanin ƙurewar lokaci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) na yankin Arewa ta Gabas, Alhaji Abba Jato, ya roƙi Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe da ya fitar da kuɗaɗen lamuran hajji ga hukumar jigilar alhazan jihar domin bata damar biya gabanin wa'adin 21 ga watan Disamba da aka bayar ya ƙare. Hukumomin Saudiyya sun sanar da ranar 21 ga Disambar 2025 a matsayin lokacin ƙarewar wa'adin da aka ɗiba wa hukumomin alhazai na su biya kuɗaɗen ayyukan hajjin 2026. Alhaji Abba Jato ya yi kiran ne a jiya Litinin yayin ziyarar ta musamman ga gwamnan, a…
Read More

Cibiyar Africa CEO Club ta ƙulla yarjejeniyar bunƙasa jagorancin kasuwanci da sana’o’i a Afrika

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar jagororin kasuwanci da masana'antu ta Afirka, wato Africa CEO Club (ACC), ta ƙulla yarjejeniya a tsakanin masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban da nufin ciyar da harkokinsu a Nahiyar Afirka. Shugabar ACC, Fatoumatta Gaye ta sanar da haka a yayi taron manema labarai da aka gudanar a Afreximbank Africa Trade Center da ke Birnin Tarayya Abuja, ranar Litinin. Ta ce, hakan abu ne da zai ƙara kusanto da jagorori masana'antu kusa duba da manufar ƙungiyar ta faɗaɗa hanyoyin zuba jari da inganta ƙananan ƴan kasuwa da kasuwancin Afirka ta yadda za su…
Read More