Babaji

5698 Posts

Ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, inji Donald Trump

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Juma'a Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce al'ummar addinin Kiristanci suna fuskantar barazana a Nijeriya, lamarin da acewarsa ya sa zai sanya ta a sahun ƙasashen da ake da damuwa akansu. Ya ce, kawo yanzu an halaka dubunnan Kiristoci a ƙasar, wanda yana faruwa ne sakamakon ta'addancin masu tsatstsauran ra'ayin addinin Islama, kamar yadda ya wallafa a wani rubutu a shafinsa na dandalin Truth Social. A cewar jaridar Reuters Daily, Shugaban na Amurka ya sanya Nijeriya, wadda ita ce ke kan gaba wajen samar da albarkatun mai a sahun ƙasashen da…
Read More

Kotu ta umarci a yi sabon zaɓe bayan tsige ɗan Majalisar Wakilai na Zamfara kan koma wa APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige ɗan Majalisar Wakilai, Abubakar Gummi kan sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ɗan majalisar shi ke wakiltar mazaɓar Gummi/Bukkuyum ta tarayya daga Jihar Zamfara. Da yake gabatar da hukunci, Alƙali Obiora Egwuatu ya haramta wa Kakakin Majalisar Wakilan, wato Tajudeen Abbas cigaba da ɗaukar Abubakar Gummi a matsayin mamba a majalisar. Haka kuma, Mai Shari'ar ya umarci hukumar zaɓe, INEC da ta shirya gudanar da sabon zaɓe acikin kwana 30 domin cike gurbinsa. Jam'iyyar PDP da Shugabanta na jihar, Jamilu Jibo-Magayaƙi ne suka shigar da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta dakatar da babban taron PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta hana babbar jam'iyyar adawa ta PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da take shiryawa, wanda ta tsara yi a ranakun 15 da 16 na watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo. Mai Shari'a James Omotosho yayin gabatar da shari'ar ya ce mambobin jam'iyyar uku ne da ke ganin an yi musu rashin adalci suka shigar da ƙarar. Ya ce, hujjar da aka gabatar masa ta nuna cewa PDP ta bijire wa wasu daga cikin dokokin ƙasa, gyaran 1999 da sharuɗɗan hukumar zaɓe (INEC).…
Read More

Natasha ta gayyaci Akpabio taron buɗe muhimman ayyuka a mazaɓarta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alamun sulhu sun fara bayyana a Majalisar Dattawa yayin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya ta gayyaci Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio zuwa wajen ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a mazaɓarta, wanda za a yi a ranar Lahadi, a garin Ihimi na Jihar Kogi. Akpabio ne da kansa ya karanta katin gayyatar musamman a zauren majalisa, ranar Laraba, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito. Za a yi taron ne domin karrama Sanatar, wadda ta cika shekara biyu a Majalisar Dattawan da kuma buɗe ayyukan da aka kammala a mazaɓar Kogi ta Tsakiya. Sanatar ta…
Read More

Tinubu ya umarci sabbin hafsoshin tsaro su jajirce wajen yaƙar ta’addanci da barazanar tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci sababbin hafsoshin tsaron da ya naɗa da su kasance masu samar da sabbin dabaru da jajircewa wajen tinkarar ta’addanci da barazanar tsaro da ke addabar sassan ƙasar. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake karrama hafsoshin tsaron da mukamansu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Alhamis. Ya bayyana yunƙurin a matsayin wata sabuwar aniya da jajircewar gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga ‘yan Nijeriya baki ɗaya. “Yau ba wai bikin ba da mukamai kawai muke yi ba, muna sabunta kudirinmu na tabbatar da…
Read More

An tasa ƙeyar lauya da wasu huɗu zuwa kurkuku kan ɓatanci ga sanatan Bauchi a TikTok

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta umarci a tsare lauya Ahmed Abdulrahman da wasu mutane huɗu a hannun ƴan sanda bisa zargin su da hannu a ayyukan sharri da tatsar kuɗaɗe daga wajen wani sanata. Rahotanni sun bayyana cewa Mai shari'ar Rita Ofili-Ajumogobia ne ta bada umarnin a ranar Alhamis bayan gurfanar da mutanen bisa tuhumar su da aikata laifuka 11 da Sufeto Janar na ƴan sanda ya shigar akansu. Mutanen sune: Daure David, Ishaq Abubakar Muhammed, Abdulrashid Abdullahi Musa, da Nasiru Usman Abubakar. A cewar bayanan masu shari'ar, ana…
Read More

NELFUND ya raba fiye da biliyan N116 ga ɗalibai sama da 600,000 tun farkon ƙaddamar da shirin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Asusun ba da lamunin karatu na ƙasa (NELFUND), ya ce ya raba sama da Naira Biliyan 116.4 ga ɗalibai fiye da 624,000 tun bayan kaddamar da shirin lamunin karatu a ranar 24 ga Mayu, 2024. A cewar rahoton da ya fitar ta shafinsa na X a ranar Talata, NELFUND ya karɓi sama da rajistar ɗalibai 929,000, inda sama da 624,000 daga cikinsu suka amfana da shirin. Rahoton ya nuna cewa an amince da sabbin masu rajista su guda 12,398, adadin da ya kai ƙarin kaso 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da rahoton da…
Read More

Gwamnan Taraba na shirin komawa APC

Mai Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas shawara akan harkokin siyasa Josiah Kente ya bayyana cewa kiran da ake yi wa gwamnan na ya koma jam’iyyar APC zai taimaka matuƙa wajen haɓaka cigaban jihar. Kente ya ce, shigar gwamnan cikin jam’iyyar mai mulki a ƙasa zai buɗe sabbin hanyoyi na haɗin gwiwa da samun tallafin gwamnatin tarayya, sannan ya taimaka wajen inganta ayyukan raya ƙasa a jihar. Ya ƙara da cewa, al’ummar jihar suna sa ran ganin ci-gaba kuma hakan zai fi yiwuwa idan aka samu daidaiton siyasa tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya. Kazalika, ya kiraye masu ruwa da tsaki…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta karrama ƴan jaridar da suka wayar da kan jama’a akan sauya fasalin haraji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Tarayya ta sanar da ƙaddamar da kyautar karramawa ga ƴan jaridar da suka ruwaito ingantaccen rahoton bayanin sauya fasalin haraji da masu wayar da kan al'umma wajen bada bayanai na gaskiya a kai. Shugaban kwamitin gyare-gyaren tsarin kasafi da haraji, Taiwo Oyedele ya sanar da haka a ranar Talata ta kafar X, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu akan ƙudirorin haraji guda huɗu da za su fara aiki daga ranar 1 ga wata Junairun 2026. A cewar sanarwar da ya wallafa, za a bada kyautar ne da nufin inganta harkokin…
Read More

Majalisar Dattawa ta tabbatar sababbin jagororin tsaro

A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sababbin hafsoshin rundunar soji da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a ranar Juma'ar da ta gabata. Majalisar ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS), da Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, sai Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da kuma Air Marshall Kennedy Aneke a matsayin hafsan sojan sama. A yayin tantance su, shugabannin sojan sun amsa wasu tambayoyi daga ƴan majalisar bayan gabatar da kansu da tarihin ayyukan da suka gudanar kafin naɗin nasu. A cewar Shugaban Majalisar…
Read More