Babaji

5698 Posts

Lalacewar layin lantarkin Gombe zuwa Damaturu ya jefa Damaturu da Maiduguri cikin duhu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya ce layin T347 da ke yankin Gombe zuwa Damaturu 330kv da ya lalace a ranar Juma'a ya haddasa katsewar wuta a yankunan Maiduguri da Damaturu na jihohin Borno da Yobe. Babban jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Ndidi Mbah a wata sanarwa, ya ce tawagarsu bayan gudanar da bincike sun gano cewa an samu katsewar ne daga tushen layin, wanda hakan yasa ya shafi raba wuta a yankunansa. Saidai, TCN ya ce duk da ƙalubalen, an samu cigaba da raba wuta a wasu yankuna ta tashar…
Read More

An tasa ƙeyar tsohon Fraministan Mali zuwa kurkuku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata kotu a Bamako ta yanke wa tsohon Fraministan, Moussa Mara hukuncin shekara guda a gidan yari bisa samun sa da laifin wallafa rubutu a kafar sadarwa da ke goyon bayan ƴan siyasar da aka tsare da nuna gazawar hukumomin gwamnati. A jiya Litinin yayin hukunci a kotun, wadda ke kula da laifukan da suka shafi yanar gizo ta kuma yi masa dakataccen hukunci na shekara ɗaya da tarar CFA 500,000, wato kimanin Dala 887. Mara, wanda shi ne fraministan ƙasar daga shekerar 2014 zuwa 2015, ya shiga hannun hukuma ne a ranar 1…
Read More

Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu

Shugaban ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara mai shekaru 83, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa domin yin wa’adin mulki na huɗu bayan samun kaso 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen ƙasar. Hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon a ranar Litinin, inda ta ce nasarar Ouattara ta biyo bayan hana manyan abokan takararsa biyu shiga zaɓen. Masana harkokin siyasa na ƙasar sun ce wannan sakamakon ya nuna ƙarfin jam’iyyarsa mai mulki da tasirinsa, duk da cewa wasu ƴan adawa suna kalubalantar tsarin gudanar da zaɓen. Rahotanni sun ce wasu ƙasashen ƙetare da ƙungiyoyin sa ido na…
Read More

Sule Lamiɗo ya yi barazanar zuwa kuto kan hana shi takardar takarar shugabanci a PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi barazanar kai ƙara kotu bayan kasa samun damar sayan fom ɗin takarar kujerar shugaban Jam’iyyar PDP ta ƙasa. Lamiɗo, wanda ya isa ofishin shugaban jam’iyyar na ƙasa da ke Abuja da safiyar Litinin domin sayen fam ɗin, ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira yunƙurin hana shi cimma burinsa na neman kujerar shugabancin jam’iyyar. Da yake magana da ’yan jarida a gaban magoya bayansa, tsohon Ministan Harkokin Waje ya jaddada cewa yana shirye sosai ya tsaya takara a babban taron zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranakun 15…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu na ganawar sirri da sababbin jagororin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin Shugaba Bola Tinubu ke wata ganawar sirri da sababbin jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An fara zaman ne tun da tsakar rana, saidai ba san asalin abinda ake tattaunawa a kai ba, amma majiyoyi sun ce bai rasa nasaba da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen inganta harkokin tsaro musamman duba da yadda fannin ya ke samun sabbin ƙalubale. A kwanan nan Fadar ta fitar da sanarwar cewa garambawul da Shugaba Tinubu ya yi wa fannin tsaro musamman rundunar sojoji, dabar ce ta inganta ƙwarewa da…
Read More

Wata sabuwa: Lamiɗo da Wike sun ƙi amincewa da yarjejeniyar Turaki a matsayin shugaban PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani sabon rikici na neman kunno kai a Babar jam'iyyar adawa ta PDP bayan da aka amince da naɗin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci, Tanimu Turaki (SAN) a matsayin ɗan takarar yarjejeniya na shugabancin jam'iyyar yayin tunkarar babban taronta da za a yi a 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo. Zaɓin, wanda aka yi bayan zaman masu ruwa da tsaki na ƴan PDP na yankin arewa ƙarƙashin jagorancin gwamnoni da jiga-jigan ƴan jam'iyya, ya samu tsaiko ne a yayin da ɓangarorin tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo…
Read More

Masu raba abincin gidajen yari na yunƙurin tsayar da aiki kan bashin biliyan N30

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da bashin da suke bin Gwamnatin Tarayya ke cigaba da hauhawa, ƴan kwangilar raba abinci a gidajen gyaran hali sun koka tare da yin gargaɗi cewa hakan ka iya shafar aikin da haifar da barazanar tsaro. Masu raba abincin sun ce, gwamnati ta riƙe musu jimillar kuɗin ciyarwa da adadinsa ya kai Naira biliyan 30 ciki har da biliyan N7.7 na ragowar kuɗin aikinsu na ƙarshen shekarar 2023 da kuma biliyan N23 na rashin aiwatar da ƙarin kuɗaɗen alawus ga fursunoni daga ɓangaren gwamnatin tarayyar. A watan Agustan 2024 ne Fadar Shugaban Ƙasa…
Read More

Abuja: Lauyan Nnamdi Kanu ya yanki jiki ya faɗi a kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bayan kwana ɗaya da Alƙali Abubakar Umar Sa'id ya ƙi sanya hannu a takardar belinsa, Lauyan Nnamdi Kanu na musamman, wato Aloy Ejimkor, ya yanki jiki ya faɗi a Kurkukun Kuje da ke Birnin Tarayya Abuja. A wani rahoto da Lauyan Ejimkor, Maxwell Opara ya fitar, ya ce ya je wata ziyarar aiki amma bai samu ganin sa ba, sannan majiyoyi sun ce ta yiwu an garzaya da shi asibiti ne a sakamakon faɗuwar. A ranar Litinin aka kama Ejimkor tare da wasu mutane 12 ciki har da ɗan'uwan Kanu, Frins Emmanuel Kanu saboda…
Read More

Jami’ar ABU ta musanta yin aikin makamin nukiliya a ɓoye

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta musanta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa jami’ar tana da hannu wajen haɗa makamin nukiliya a ɓoye ga Nijeriya. Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. Ya ce bidiyon da aka ƙirƙira ta fasahar zamani wato AI, ƙarya ne da ke da nufin ruɗar da jama’a game da shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da Nijeriya ke gudanarwa. Ya ce, bidiyon ya yi ikirarin cewa masana kimiyyar Nijeriya a shekarun 1980…
Read More

Ba na buƙatar sake zama shugaban jami’a, inji Farfesa Abdallah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban (VC) Jami'ar 'National Open University of Nigeria' (NOUN) da ke Abuja, Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake masa ta kafar Soshiyal Mediya na neman ya karɓi tayin zama sabon shugaban Jami'ar 'Northwest University, Kano' ta Jihar Kano, yana mai cewa ba shi da ra'ayin sake karɓar wani muƙamin da ya shafi harkar jagoranci. A wata takarda da ya fita a yau Asabar, Farfesan ya ce da fari bai samun labarin yaɗa kiran da ake masa ba ta kafar sada zumunta sai a kwanan nan, lamarin da ya…
Read More