25
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙaddamar da sabuwar na'urar fasahar AI domin inganta ayyukan ma'aikata da kimtsi cikin lokaci yayin da ake tunkarar zaɓen Jihar Anambara da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamba. An yi wa na'urar laƙabi da INEC Training Virtual Assistant' ko kuma 'INECTrainingBot', wanda aka gabatar da ita a jiya Juma’a, wadda za a iya samu ta manhajar Telegram. A cewar hukumar zaɓen, na'urar za ta riƙa bada damar samun baki ɗaya kayayyakin zaɓe ga ma'aikata cikin sa'o'i 24, horo na bada damar tattaunawa da ababen koyo…
