Babaji

5702 Posts

Abinda ya sa jam’iyyun adawa ba za su haɗe ba – Akpabio

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce jam'iyyun adawa ba za su samu haɗin kan da suke nema ba matuƙar za su cigaba da sukar duk abinda ya shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyya mai mulki (APC). Akpabio ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙaddamar da wani sashi na titin jirgin ƙasa a Abuja. Taron ya samu halartar wasu jiga-jigan PDP da suka haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Enugu da Ekiti, wato Ifeanyi Ugwanyi da Ayo Fayose. Shugaban Majalisar Dattawan ya faɗi haka ne bisa la'akari da kalaman Tinubu na Ranar Dimukraɗiyya,…
Read More

Iran ta naɗa sababbin jagororin sojoji bayan harin Isra’ila ya kashe manyan kwamandoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Biyo bayan hare-haren da Isra'ila ta kai wa Iran a ma'ajiyar makaman nukiliyarta ƙasa da sa'o'i 48 da suka gabata, waɗanda suka yi sanadin rasa rayukan manyan jami'an sojojinta, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da maye gurbin waɗanda aka rasa daga cikin manyan hafsoshin. Wata jarida daga Iran ta ruwaito cewa, daga cikin sojojin da suka rasu akwai; Shugaban Rundunar sojojin Iran, Manjo Janar Mohammed Bagheri; Kwamandan jami'an Islamic Revolution Guard, Manjo Janar Hossein Salami; da kuma Laftanal Janar Gholam-Ali Rashid, wato Shugaban Hedikwatar Khatam al-Anbiya. Jim-kaďan bayan haka ne…
Read More

Kaduna: ‘Yan sanda sun kama mutane 13 bisa zargin su da hannu a kisan soja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Kaduna ta kama mutane guda 13 a yankin Kawo dake jihar, inda wasu ƴan ƙwacen waya suka hallaka jami'in sojan ruwa mai suna Laftanal Kwamado, M. Buba. Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya ce bayan aukuwar lamarin ne jami'ai suka gudanar da atisaye a yankin, lamarin da ya yi sanadin kama mutane 13 da wasu muggan makamai. Marigayin, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ɗaliban kwalejin horar da jami'an sojoji ta Jaji, an daɓa masa wuƙa ne a ƙirjinsa, a madakatar ababen hawa da ke kusa da babbar gadar yankin…
Read More

Iran ta jefa wa Isra’ila makaman linzami karo na biyu

Daga BELLO A. BABAJI Baya ga harin Isra'ila akan ma'ajiyar makaman nukiliyar Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar manyan sojoji da masana kimiyya da hallaka mutane da dama. Jakadan Iran ya shaida wa majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa fararen hula sun fi yawa daga cikin waɗanda aka kashe. Ya bayyana hakan ne jim-kaďan bayan Iran ta mayar da martani da makamai masu linzami a babban birnin kasuwancin Isra'ila, wato Tel Aviv, wanda ya raunata aƙalla mutane 34. Isra'ila ta tsokano faɗan ne duba da yadda ƙarfin makaman nukiliyar Iran a Tehran ya ke cigaba da bunƙasa. A tsawon…
Read More

Sojoji sun kama ɗan Chana yana jagorantar safarar makamai ga Boko Haram

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta sanar da kama wani ɗan ƙasar Chana a yayin wani atisayen daƙile ayyukan ta'addanci da jami'an sojoji suka gudanar a Jihar Borno. Duk da cewa ba a bayyana sunansa ba, sojoji sun ce mutumin ya ce yana aikin haƙar ma'adanai ne, wanda a yanzu yana riƙe a hannunsu. Hakan ya faru ne ƙasa da mako ɗaya da kama wasu ƴan Pakistan guda huɗu a shiyyar Arewa maso Gabas, waɗanda ke bada horo ga ƴan ta'adda. Wata majiya daga sojoji ta shaida wa manema labarai cewa,…
Read More

June 12: Shettima ya jinjina wa MKO Abiola bisa gudumawarsa ga dimokraɗiyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce tarihin fafutukar tabbatar da dimokraɗiyya na daya daga cikin tunawa da marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola, wanda ya yi daidai da ranar 12 ga watan Yuni. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a yayin taron bikin murnar cikar dimokraɗiyya a Njeriya shekaru 26 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja. Ya kuma bayyana marigayi Abiola a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya miƙa wuya domin ƴan Nijeriya. Ya ƙara da cewa, sadaukarwar Abiola ta zama…
Read More

June 12: Ku kira ni duk abinda kuka ga dama, zan cigaba da tabbatar da ƴancinku na dimukraɗiyya – Tinubu ga ƴan Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin cigaba da bada kariya ga ƴancin tofa albarkaci baki da dimukraɗiyya ta bai wa ƴan Nijeriya dama akai. A lokacin da ya ke jawabin Ranar Dimukraɗiyya a zauren Majalisar Dokoki a Abuja, ranar Alhamis, Tinubu ya faɗa wa wakilan jami'an tsaro cewa kada su riƙa matsa wa masu sukar gwamnatinsa, waɗanda suke ganin tsare-tsarensa ba su yi musu ba ko kuma suna ɗauke da matsi. Ya ce, a tsarin dimokraɗiyya sai an samu juriya game da suka da zage-zage don haka ko da al'umma za su riƙa kiransa da wasu…
Read More

Na yi kuskuren sukar Jonathan, inji Bello El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i kuma ɗan majalisar wakilai a yanzu, Bello El-Rufa'i ya yi da-na-sanin sukar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Johnathan. Bello, wanda ke wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa ya ce a rashin sani ne ya sa bai san cewa akwai shugabanci ba a zamanin gwamnatin Goodluck. Ya ce, ya gano hakan ne a lokacin da ya ga mahaifinsa ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar domin tattauna bututuwan da suka shafi siyasa. Lamarin da ya sa ya fahimci cewa, haƙiƙancewa da ya ke yi a baya wajen sukar gwamnatin Goodluck kuskure…
Read More

Yanzu-yanzu: Harin da Isra’ila ta kai ma’ajiyar nukiliyar Iran ya halaka manyan sojoji da masana kimiyya

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar Sojojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da hari akan sojojin Iran da ma'ajiyar makaman nukiliyarta dake Babban Birnin ƙasar, Tehran. Akan haka ne Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya gargaɗi Isra'ila da cewa ta tsammaci mummunar sakamako ga abinda ta aikata, wanda ya yi sanadin hallaka da yawa daga cikin kwamandojin sojojinta da manyan masana kimiyya. A wani saƙo ta bidiyo da Fraministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya fitar da safiyar Juma'a, ya ce harin an zartar da shi ne da nufin nakasa albarkatun makaman nukiliyar Iran. Shugaban jami'an sojojin Isra'ila, Eyal Zamir ya ce ƙarfin…
Read More

Tinubu ya yi watsi da haƙiƙanin waɗanda suka cancanta da karrama wasu, inji lauyan ƴancin ɗan adam

Daga BELLO A. BABAJI Masanin shari'a kuma babban lauya a Nijeriya (SAN), Sunusi Musa, ya ƙalubalanci matakan da aka bi wajen bada kyautar karramawa ta ƙasa da aka gudanar a yau Ranar Dimukraɗiyya. Ya ce, an yasar da wasu da suka yi gwagwarmayar kafa mulkin dimokraɗiyya tun daga zaɓen Shugaban Ƙasa da aka soke na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993. A wani saƙo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, Babban Lauyan ya hasato wasu mutane da ya ke ganin ya kamata a ce suna daga cikin waɗanda aka karrama, amma rashin jin sunayensu ya sa ya…
Read More