12
Jun
Daga BELLO A. BABAJI An baza jami'an tsaro a Birnin Tarayya Abuja a yayin da wasu dandazon jama'a suka fara gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da halin matsin rayuwa da rashin tsaro da ake fama da su a ƙasar a birnin. Hukumomin tsaro sun baza jami'an nasu ne a wurare mabanbanta a cikin birnin musamman inda ake sa ran ɓarkewar zanga-zanga. Daga cikin wuraren akwai Eagle Square da Majalisar Dokoki, wato 'National Assembly' da wasu wuraren da masu zanga-zanga suka taru. Lamarin ya yi daidai da Ranar Dimukraɗiyya a Nijeriya, inda wasu masu zanga-zanga suka fara tattaki daga…
