Babaji

5713 Posts

Ganduje zai cigaba da zama shugaban APC sakamakon yiwuwar ɗage babban zaman Majalisar Zartarwar jam’iyyar zuwa 2025

Daga BELLO A. BABAJI Alamu sun nuna cewa shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ka iya dakatar da taron ƙaddamarwa na babban kwamitin Zartarwa na Ƙasa, NEC zuwa 2025. An samu wasu bayanai daga Sakatariyar APC kan cewa ayyuka da suka yi wa Shugaba Tinubu yawa da rashin kasancewar sa a ƙasa su ne dalilan da suka sa za a ɗage zaman. Wata majiya ta ce, saboda Shugaba Tinubu ba ya ƙasa ya sa aka dage zaman a karon farko wanda aka tsara yin sa tun a watan Satumban da ya gabata. Duk da cewa ba a samu…
Read More

Babu taƙaice zirga-zirga ga matafiya yayin zaɓen ƙananan hukumomi – Gwamnatin Kogi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Kogi ta ce babu dokar taƙaice zirga-zirgar matafiya a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar Asabar. Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar (KOSIEC), Mista Mamman Nnda-Eri ya bayyana hakan wa 'News Agency Nigeria' a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Juma'a. Nnda-Eri ya tabbatar wa matafiya samun gudanar da harkokinsu cikin sauƙi ba tare da musgunawa ba kamar yadda Kwamishinan Labarai, Mista Kingsley Fanwo ya faɗa a cikin wata sanarwa, da ya ke magana kan taƙaice zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 7 na safe zuwa 4 na yamman…
Read More

Obasanjo, Buhari, Sarkin Musulmi da manyan ƙasa sun taya Gowon murnar cika shekaru 90

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya jinjina wa tsohon shugaban mulkin soji, Janar Yakubu Gowon kan cika shekaru 90 a duniya, ya na mai cewa hakan abu ne wanda ya kamata a ce ƙasa ta yi murna a kai. Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja a lokacin lakcar bikin zagayowar ranar haihuwar Gowon a jiya Juma'a inda ya yi godiya ga Ubangiji ganin yadda Ya sa Gowon ya kai shakaru 80 a duniya. Shugaban taron, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya jinjina wa tsohon shugaban ƙasar inda ya ce shi ɗin jigo…
Read More

BANKAƊA: Hisbar Kano ta kama kwamishinan Jigawa da matar aure a kango

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta tabbatar da kama Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara bayan gano shi da aka yi a wani kango tare da wata matar aure. An kama shi ne bayan wani bincike da ake yi kan wasu ƙararraki da aka shigar game da zargin sa da ƙula haramtacciyar alaƙa da matar. Darakta-Janar na hukumar, Dakta Abba Sufi, ya ce an kama kwamishinan ne bayan gudanar da wani bincike na sirri sakamakon ƙara da mijin matar, Nasiru Bulama ya shigar kan zargin mutumin da yin lalata da matarsa mai…
Read More

Nijeriya ta ƙarfafa alaƙarta ta kasuwanci da ƙasar Sweden

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Nijeriya ta ƙula yarjejeniyar cimma matsaya ta MoU tsakanin ta da kamfanin telekom, Ericsson kan samar da sabis mai ƙarfin 5G. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar ƴan Nijeriya inda aka ƙula yarjejeniyar wadda an yi ta ne don a sanya Nijeriya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi amfani da 5G wajen harkokin ingantayya na fasahar zamani. An gabatar da taron ne a yankin Arewacin Stockholm da ke Sweden wanda ya zama fage na ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu. Ciki wata takarda da mai taimaka wa shugaban…
Read More

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya ya jajenta wa Nijeriya kan fashewar tankar mai a Jigawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja Wakilin Babban Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman ga kula da Yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana baƙin cikinsa game da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa. Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnati da al'ummar Nijeriya baki ɗaya. Fashewar, wadda ta auku cikin mummunan yanayi, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama,…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da tsarin ƙin karɓar tsabar kuɗi a hanyar Abuja-Keffi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ƙaddamar da tsarin ƙin karɓar tsabar kuɗi (cashless tolling system) a babbar hanyar Abuja zuwa Keffi. Ministan Ayyuka, Sanata Umaho ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya ke ƙaddamar da naɗa kwamitin aikin da kuma ninka hanyar Keffi zuwa Akwanga zuwa Makurdi. Ya ce tsarin, wani shiri ne ƙarƙashin shirin samar da ci-gaba a manyan titina don samar da sufuri mai sauƙi da inganci acikin al'umma. Ministan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya tare da fatan kwamitin…
Read More

Shettima ya buƙaci ƴan kasuwa su yi amfani da damar kasuwancin zamani don bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga manyan ƴan kasuwa da su ya amfani da damammaki wajen zuba hannun-jari a ɓangarorin daban-daban don bunƙasa harkar tattali a Nijeriya. Ya ce akwai buƙatar a sanya hannu a ƙananan masana'antu, noma, harkar tattali na zamani, ingantayya da makamantansu. Wata takarda daga Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harakokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha, ta ce harkar zuba hannun-jari na ƙasashen waje da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tsara, ya samu ƙaruwa a ranar Alhamis bayan da ƴan kasuwa da dama daga ƙasar Sweden suka ƙudiri aniyar zuba…
Read More

Yadda shari’a ta zama wasan kwaikwayo bayan rashin sanin inda wanda aka tsare ya ke

DAGA BELLO A. BABAJI An samu wani abin mamaki a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da aka nemi babban ma'aikacin kamfanin Binance Holding Limited, Tigran Gambaryan ba a gan shi ba bayan an tsare shi na zaman dakon shari'a wadda aka shirya yi a yau Juma'a. Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Shari'a Emeka Nwite na kotun ya ayyana ranar 18 ga watan Oktoba don gurfanar da kamfanin da ma'aikacin kan badaƙalar wasu kuɗaɗe da hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta shigar. A lokacin da aka shirya tsaf don sauraren ƙarar ne, sai aka…
Read More

Kiwon Kaji: Gidauniyar BATN ta tallafa wa mata 200 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gidauniyar 'British American Tobacco Nigeria Foundation', BATN tare da haɗin-gwiwar Ma'aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya da Ma'aikatar Noma da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Zamfara, sun bai wa mata 200 da jariran kajin turawa don inganta shirin kiwon kaji a jihar. A lokacin da ya ke magana a wajen ƙaddamar da rabon kajin a Gusau, babban Manajan BATN, Oludare Odusanya ya ce, gidauniyar ta zaɓo mata 200 ne daga dukkan ƙananan hukumomi 14 dake jihar don su ci gajiyar tallafin. Ya ce kowacce mace za ta karɓi kaji guda 20, buhun abincinsu na…
Read More