Babaji

5713 Posts

Yadda ƴan kasuwa suka shigo da fetur lita miliyan 123 don rage nauyi ga Ɗangote

Daga BELLO A. BABAJI Aƙalla gungun maɗaukai huɗu ne ɗauke da man fetur suka iso tashoshin jiragen ruwan Nijeriya daga ranar 18 zuwa 20 ga watan Oktoba. Cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen ruwa (NPA) ta fitar, ta ce aƙalla man da aka yi dakon su zuwa ƙasar sun kai kusan lita miliyan 123.4 don faɗaɗa harkar raba fetur a Nijeriya. Rahotonni sun bayyana cewa, dilolin sun yi hakan ne don rage nauyin samar da fetur ga matatar Ɗangote, inda suka ce adadin da ta ke samarwa ya yi kaɗan ga duka sassan Nijeriya. Sun yi zargin…
Read More

DSS ta tsige Adegboyega a matsayin babban jami’in tsaron Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Ƙasa (SSS), Tosin Ajayi, ya tsige Adegboyega Fasasi daga muƙamin babban jami'in tsaro (CSO) ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Wata majiya ta ce an cire Fasasi ne daga muƙamin inda aka maye gurbinsa da Rasheed Atanda Lawal, wanda mataimakin darakta ne da ke ɗaukar horo a Cibiyar Nazarin Harkar Tsaro ta Ƙasa. Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, an cire Fasasi ne daga matsayinsa da amincewar Shugaba Tinubu sakamakon wata buƙata da aka nema ta tura shi ɗaukar horo a ƙarƙashin tsangayar koyon salon iya aiki. Rahotonni sun bayyana cewa, ana…
Read More

NELFUND ta bai wa ɗaliban Nijeriya lamunin Naira biliyan 11

Daga BELLO A. BABAJI Asusun bayar da lamunin ilimi na ƙasa, NELFUND ya ce, zuwa yanzu ya raba rancen kimanin Naira biliyan 11 ga ɗalibai domin tallafa wa ilimi a ƙasar. Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya faɗi hakan a yayin wata hira da Gidan Talabijin na Arise inda ya bayyana ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin an samu sauƙi a harkar Ilmi. Sawyerr ya ce ba za a buƙaci waɗanda suka ci gajiyar lamunin su biya bashin ba, har sai bayan sun kammala bautar ƙasa da shekaru biyu ko kuma sun samu aikin yi. Sannan, tsarin biyan lamunin zai…
Read More

Gwamnatin Katsina ta bada tallafin N50m ga Jigawa kan iftila’in tankar mai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe ya miƙa saƙon ta'aziya da jaje ga al'umma da gwamnatin Jihar Jigawa bisa mummunar iftila'in gobarar motar man fetur da ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dama. Mataimakin gwamnan ya kuma sanar da bada tallafin kudi Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar don rage raɗaɗi ga iyalan mutanen da suka mutu da waɗanda suka jikkata . Da ya ke jawabi bayan ya karɓar tallafin kuɗin, gwamnan Jigawa, Alhaji Umar Namadi ya yi godiya ga gwamnatin Katsina bisa turo tawaga ta musamman domin yin jaje tare da bada…
Read More

NERC za ta binciki matsalar ɗaukewar rumbun lantarki a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ta ce ta na shirin gudanar da bincike game matsalar ɗaukewar lantarki da ake samu a ƴan kwanakin nan daga rumbun lantarkin Nijeriya. Ta ce dalilin yin hakan shine don gano ainihin musabbabin abin da ke haifar da faruwar lamarin akai-akai. NERC ta bayyana hakan ne ta shafinta na X a ranar Asabar inda ta ce za a yi hakan ne don samar da mafita ta dindindin game da al'amarin. Hukumar ta kuma ce za ta sanar da rana da lokaci da za a yi zama game batun…
Read More

An kama ɗan shekara 18 bisa zargin sace ɗan maƙota a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan Jihar Sakkwato ta kama wani matashi mai suna Abba Aliyu kan zargin sa da laifin yin garkuwa da wani ɗan ƙaramin yaro. Kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa'i, ya ce sun samu ƙara ne daga wani Ibrahim Shehu a ranar 16 ga watan Oktoba kan cewa ɗansa da mai kimanin shekaru biyu ya ɓata tun a ranar 13 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 6 na yamma. An yi ta ƙoƙarin gano inda yaron ya ke, amma hakan bai sa an yi nasara ba har sai da wanda ya yi garkuwa da shi ya…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya dawo Nijeriya bayan kammala hutun aiki

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya bayan shafe makonni ya hutunsa na shekara. Mai taimaka masa, Dada Olusegun ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya iso Nijeriya, inda ya ke masa maraba da dawowa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar. Tinubu ya iso Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe ne da ke Abuja da dare bayan ƙarewar lokacin hutun.
Read More

NOA ta ƙaddamar da ayyukan bunƙasa aƙidun ƙasa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Farouk Joɓe, ya koka kan yadda kishin ƙasa yayi rauni a tsakanin ƴan Nijeriya. Ya nuna takaicinsa ga yadda ƴan ƙasa suka yi watsi da tarihinsu da kishin ƙasa wanda hakan ya jefa mutane da dama cikin halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa. Mataimakin gwamnan, wanda shi ne babban baƙo wajen taron da Hukumar Gyaran Aƙida ta Ƙasa (NOA) ta shirya a Katsina, ya ce Nijeriya na da arziƙin ƙasa da yawan al'umma wanda ita kanta al'ummar arziƙi ce. A nasa jawabin, Shugaban NOA, Mista Lanre Issa_onilu wanda ya samu…
Read More

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda huɗu da ƙwato makamai

Daga BELLO A. BABAJI A yayin wasu atisaye da jami'an sojojin Nijeriya suka gudanar, sun yi nasarar kama wata mata mai safarar makamai da kuma tarwatsa ƴan ta'adda inda suka ƙwato muggan makamai. A lokacin da suka kai farmaki, jami'an sun kuma yi nasarar kashe wasu manyan ƴan ta'adda tare da kama wasu sanannu daga cikin su. A ranar 17 ga watan Oktoba ne jami'an suka kama wata mata da takwarata a tashar mota ta Barikin Ladi da ke Jihar Filato da laifin safarar makamai ga ƴan ta'adda a Jihar Zamfara. Hakan ya sa jami'an suka yi nasarar kama wani…
Read More

An naɗa ɗan ƙabilar Igbo na farko a matsayin limamin babban masallacin Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar gudanarwa ta babban Masallaci na Ƙasa da ke Abuja (National Mosque), ta naɗa Farfesa Iliyasu Usman a matsayin ɗaya daga cikin limaman masallacin. Lamarin da ya sa ya zamo mutum na farko daga ƙabilar Igbo da ya samu matsayin limanci a masallacin. Farfesan Larabcin zai zama mataimaki ga Farfesa Ibrahim Maƙari da kuma Farfesa Muhammad Kabir da kuma limami na huɗu, wato Sheikh Ahmad Onilewura. Al'umma da dama musamman ƴan ƙungiyar musulman Kudu-maso-Gabas (SEMON) sun yi murnar samun labarin inda ƙungiyar ta yaba masa kan ƙoƙarin da ya ke yi ta fuskar shugabanci da hidimta…
Read More