Babaji

5715 Posts

NNPC ya ƙara kuɗin litar fetur a Abuja da Legas

Daga BELLO A. BABAJI Gidajen man fetur mallakar kamfanin NNPCL, sun ƙara farashin kowacce lita a jihohin Abuja da Legas. Kafin yanzu, ana sayar da litar ne akan N897 wanda yanzu kuma an mayar da shi zuwa N1,030 a Abuja. A yankin Maitama da ke Abuja, an ruwaito cewa mutane sun yi cincirindo wajen sayan man inda suke ta ƙorafi game da ƙarin. 'News Point Nigeria' ta ruwaito cewa masu sayan man sun ɗauki tsawon lokaci su na jira don a fara sayar da man a yankin Gudu na Abuja inda wani ma'aikaci ya ce ana aikin mayar da na'urar…
Read More

Ɗan-Isan Zazzau ya rasu a hatsarin mota

Daga BELLO A. BABAJI An samu rahoton rasuwar Yariman Masarautar Zazzau kuma Ɗan-Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris bayan aukuwar wani hatsari akan hanyar Abuja-Kaduna da daren nan. Kakakin Masarautar, Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Mamacin, mai shekaru 41, ya rayu ne da mata ɗaya da ƴaƴa biyu. Kafin rasuwarsa, shi ne Mataimakin Sakataren Majalisar Masarautar. A kwanakin baya ne mahaifiyarsa, Hajiya Habiba Shehu Idris, wacce ita ce mahaifiya ga Sarki na yanzu, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ta rasu. Wakilin Blueprint ya ce iyalan mamacin za su sanar da lokacin da za…
Read More

An kori ɗan Osama Bin Laden daga Faransa

Daga BELLO A. BABAJI Hukumomin ƙasar Faransa sun umarci Omar, wanda ɗan sanannen Shugaban ƴan ƙungiyar Al-Ƙa'ida, Osama Bin Laden ne da ya fice daga ƙasar. Omar, mai shekaru 43, an buƙaci ya yi hakan ne ta kafar sada zumunta kamar yadda Ministan Harkokin Cikin gida na ƙasar, Bruno Retailleau ya bayyana. An haifi Omar ne a ƙasar Saudiyya wanda ya kuma taɓa zama a Sudan da Afghanistan. Sun kuma rabu da mahaifin nasa a lokacin da ya ke da shekara 19 a duniya inda daga bisani a shekarar 2016 ya koma yankin Normandy da ke Arewacin Faransa. Saidai, Minista…
Read More

‘Yan sanda sun ceto mutane takwas da ƴan bindiga suka yi yunƙurin sacewa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƴan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin da ƴan bindiga suka yi na sace mutane a ƙananan hukumomin Faskari da Ɗan-Musa. A Ɗan-Musa, ƴan bindigar sun tare mata su biyu a ƙauyen Matarau da ke kan hanyar Ƴan-Tumaki zuwa garin Ɗan-Musa, inda ƴan sandan suka kai wa matan ɗauki tare da yin ɗauki ba daɗi da ƴan bindigar har sai da suka samu nasarar ceto matan. A Faskari kuwa ASP Sadiq Aliyu wanda shi ne Kakakin ƴan sandan jihar, ya ce ƴan bindigar sun tare hanyar ƙauyen Marabar Bangare da Unguwar Kafa a kusa da…
Read More

Dalilin da ya sa ni da Raɗɗa muka nemi Tinubu ya soke kwangilar hanyar Ƙanƙara-Katsina – Ibrahim Masari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Baban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari ya bayyana dalilan da yasa suka shiga suka fita shi da Gwamna Dikko Raɗɗa aka soke aikin sake gina hanyar Ƙanƙara zuwa Katsina daga hannun ɗan kwangila. Kabir Masari ya faɗi haka ne a Katsina a lokacin bikin raba shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar don raba wa al'umma su rage raɗaɗin rayuwa da ake fama da shi. Aikin hanyar mai tsawon kilomita 170 da ta taso daga Marabar Ƙanƙara zuwa Katsina, ta haɗa ƙananan hukumomi bakwai waɗanda yawancin su…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya umarci ƴan sanda su koma ofisoshin ƙananan hukumomin Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Gwamna Siminalayi Fubara da shugabannin siyasa da mabiyansu a Jihar Ribas su ƙaurace wa fitina tare da kiyaye doka. Hakan na zuwa ne sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar wanda ya haddasa tashin-tashina da tashe-tashen bama-bamai a yankunan manyan ofisoshin ƙananan hukumomin jihar saboda ƙin amincewa da sakamakon zaɓen daga wani ɓangare na al'ummar jihar. Shugaba Tinubu ya umarci jami'an ƴan sanda su gaggauta dawo da zaman lafiya da kiyaye doka da oda. Ya nuna muhimmancin kula da kiyaye doka da kuma kare kadarorin…
Read More

‘Yan bindiga sun tare hanyoyin ofisoshin sabbin kantomomin Ribas da yin harbe-harbe

Daga BELLO A. BABAJI An samun harbe-harben bindigogi a ƙananan hukumomi da dama na Ribas bayan da wasu ƴan daba suka yi yunƙurin hana sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a jihar shiga ofisoshinsu. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓen jihar, RSIEC ta yi a ranar Lahadi. Bayan zaɓen ne, Gwamnan jihar, Siminialayi Fubara ya rantsar da kantomomin baki ɗaya na ƙananan hukumomi 23 da ke jihar. A sakamakon haka ne, Sufeton ƴan sanda, ta hannun kakakin ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ya umarci jami'ansu su fice daga duka ofisoshin ƙananan hukumomin…
Read More

Yadda Gwamnatin Tarayya ta raba shinkafa buhu 21,924 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin raba shinkafa buhu 21,924 ga al'ummar jihar Katsina. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne ƙarƙashin kwamitin shugaban ƙasa kan samar da abinci a jihohi Arewa-maso-Yamma, inda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya jagoranta. Ya ce, manufar bada tallafin shinkafar ita ce don ya isa ga mai ƙaramin ƙarfi a kowane mazaɓar gunduma 361 da ke faɗin jihar. Kabir Masari ya ƙara da cewa, raba irin tallafin akai-akai na ɗaya daga cikin shirin gwamnatin tarayya na taimakawa wajen rage halin ƙunci da…
Read More

Na yi wa Tinubu yaƙin neman zaɓe, don haka na yarda da hukuncinsa kan garambawul – Ministar Al’adu

Daga BELLO A. BABAJI Ministar Al'adu, Hannatu Musawa ta ce ba ta damu da shirin garambawul na ministoci da Majalisar Zartarwa (FEC) ke yi ba ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ministar ta faɗi hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels' inda ta ce ta san ta yi wa Tinubu yaƙin neman zaɓe kuma ta yarda da hukuncinsa. Ta ce, ta san shugaban ƙasar ya na da manufa da burin sauya Nijeriya daga halin da take zuwa yanayi mai kyau, ta na mai cewa hakan ba zai samu ba ba tare da mataimaka masu jajircewa ba.…
Read More

Za a yi wa Sarki Salman na Saudiyya gwajin ciwon ƙoda bayan kwantar da shi a asibiti

Daga BELLO A. BABAJI An kwantar da Sarki Salman Bin Abdul'aziz As-Saud a asibiti don duba lafiyarsa game da cutar ƙoda. Kotun Masarautar Saudiyya ta tabbatar da batun cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce, an yi hakan ne la'akari da shawarwari da asibitocin Masarautar ƙasar suka bayar. A watan Mayu na shekarar nan ne Sarkin, mai shekaru 88 kuma ɗan kasuwa daga gabas ta tsakiya mafi fitar da mai ga ƙasashen duniya, aka duba lafiyarsa a ɓangaren ciwon ƙoda. Sarki Salman ya bada dokar ta bada damar gudanar da jagoranci daga magajin mahaifin Sarkin…
Read More