Babaji

5715 Posts

NNPC ya sayi kowacce litar fetur akan N898 daga matatar Ɗangote

Daga BELLO A BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce, ya sayi fetur daga matatar Ɗangote akan N898 kowacce lita yayin ya fara jidon farko a ranar Lahadi. An ga manyan motocin NNPCL na ɗaukar mai daga matatar wacce ta ke Lekki a jihar Legas a kafafen sada zumunta. A ranar Asabar ne NNPC ya ce zai tura motoci 100 zuwa matatar don ɗibar zango farko na man fetur mallakarta. An ruwaito cewa, NNPCL ya sayi kowacce lita ne akan N760 wanda kakakin kamfanin, Olufemi Soneye ya musa, ya na mai cewa N898 suka sayi kowacce lita guda.
Read More

Gwamnan Katsina ya halarci bikin sallar Gani a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa na daga cikin dubban mutanen da suka halarci bikin sallar gani a garin Daura da ke jihar. Sallar Gani tana ɗaya daga cikin bukukuwan da ake yi a kowacce shekara a ƙasar Daura na zagayowar wannan wata mai tsaki da aka haifi fiyayyayen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Cikin bukukuwan da ake yi akwai hawan Dawaki da Sarkin Daura ya kan jagoranta tare da hakimansa da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a kowacce shekara. A jawabinsa, mai martaba sarkin Daura Faruk Umar Faruk ya gode wa gwamna Raɗɗa kan ƙoƙarin…
Read More

Dujuman Katsina ya taya Musulmi murnar Maulidi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A daidai lokacin da Musulmi ke cigaba da gudunar da murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), shugaban kwamitin majalisar tarayya mai kula da harkokin cikin gida, Hon. Abdullahi Aliyu na taya al'ummar musulmi murna. Hon. Abdullahi Aliyu (Dujuman Katsina) ya ce, ya na kira ga al'ummar musulmi su yi amfani da wannan dama wajen yin addu'o'i na musamman domin samun zaman lafiya ga ƙasa baƙi ɗaya. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa ɗan majalisar kan harkar labarai, Frances Sardauna ya fitar inda Dujuman Katsinar ya yi kira…
Read More

Gwamnan Zamfara ya jajenta wa mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna damuwarsa kan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar da asubahin ranar Lahadi. Aƙalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu bayan jirgin ya ƙwace a rafin Bakin Kasuwa na gundumar Uban Dawaki da ke ƙaramar hukumar. Wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamna Lawal ya bayyana hakan a matsayin abin alhini da kuma tausayawa inda ya umarci Hukumar bada agaji ta gaggawa reshen jihar (ZEMA) ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace game da lamarin. Dauda Lawal ya kuma umarci kwamishinan…
Read More

Babban Hafsan Tsaro ya sauya tsarin atisaye da ƙara kayan aiki ga jami’ai a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya sake tsarin atisayen da aka shirya gudanarwa a Zamfara a ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda. Ya ce, atisayen sun ɗauki salo na kwamandanci inda janarorin kwamandodi za su yi aiki a matsayin kwamandodi na tawaga (component commanders). Ya bayyana cewa, hakan na zuwa ne sakamakon yunƙurin inganta haɗin-gwiwa da kula a tsakanin jami'an tsaro. Daraktan watsa Labarai na rundunar, Janar Tukur Gusau ya ce, shugaban tsaron ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyara wa gwamnan jihar, Dauda Lawal a ranar Juma'a. Janar…
Read More

Zargin almundahana: Kantomomin ƙananan hukumomin Kano sun arce bayan ICPC ta cafke ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hana rashawa da Laifuka masu kama da ita, ICPC ta kama kantoman ƙaramar hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano, Zangina Galadima Zango. ICPC ta kama shi ne kan zargin sauya akalar wasu kuɗaɗe da gwamnatin jihar ta yi ta hannun kantomomi 44 na faɗin jihar. Jin haka ke da wuya, sauran kantomomin ƙananan hukumomin suka arce bayan wani yunƙuri na kamo su da jami'an hukumar suka yi kamar yadda rahotonni suka bayyana. Hakan ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen labarai, cewa an yi garkuwa da kantomomin ne. A kwanakin baya ne aka ruwaito…
Read More

PDP ta dakatar da Sanata Umar Tsauri a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam'iyyar PDP a gundumar Tsauri a ƙaramar hukumar Kurfi da ke Jihar Katsina, ta dakatar da tsohon Sakatarenta na ƙasa, Umar Ibrahim Tsauri. A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun shugaba da sakataren na jam'iyyar, Danjuma Abubakar da Abdullahi Garba suka aika sa zuwa ga shugaban jam'iyyar ta jiha, sun dakatar da Sanata Tsauri ne bisa yi wa jam'iyyar zangon-ƙasa . Haka kuma, jam'iyyar ta zarge shi da maganganu na tayar da husuma ga shugabanninta na ƙasa da kuma nuna halayya da mu'amullar da ka iya haifar da ruɗani a jam'iyyar. Sun ce,…
Read More

Aƙalla mutane 40 sun halaka a hatsarin jirgin ruwa a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Aƙalla sama da mutane 40 ne suka mutu da suka haɗa maza da mata a kogin Gummi da ke ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara. Daraktan Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar (ZEMA), Hon. Hassan Dauran, ya shaida wa manema labarai cewa, jirgin na ɗauke ne da fasinjoji sama da 50 a lokacin da hatsarin ya auku. "Kamar yadda na ke magana a yanzu, kaɗan ne daga cikin su aka ceto da ransu a lokacin, yayin da mafi yawan fasinjojin, galibi mata da ƙananan yara sun hallaka." A zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho, wani…
Read More

Edo 2024: Shettima da Ganduje sun shiga sahun masu nema wa Okpebhol ƙuri’a

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya roƙi al'ummar Jihar Edo su zaɓi ɗan takarar APC, Sanata Monday Okpebhol a zaɓen gwamna da za a yi a ranar Asabar don samun shugabanci mai inganci. Shettima, wanda ya halarci taron rufe yawon neman zaɓen ɗan takarar tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar a Benin babban birnin jihar, ya ce a halin da ake ciki, Edo ta na buƙatar jagora mai basira da iya gina al'umma wanda zai kai ga samun nasarori ga mutanensa. Ya kuma bayyana wa al'ummar jihar cewa, samun jiha mai cike da damanmaki shi ne burinsu…
Read More

Ambaliyar Maiduguri: Adadin ƴan Boko Haram da wasu fursunoni da suka tsere ya kai 4,643

Daga BELLO A. BABAJI Aƙalla fursunoni 6,675 da suka haɗa da manyan ƴan Boko Haram da makasa suka tsere a gidajen yari mabanbanta 13 cikin shekaru biyar a Nijeriya. Rahotonni sun bayyana cewa, kaso 30.4 ne jami'ai suka yi nasarar sake kamowa yayin da aka rasa kama 60.5. Na kwanan nan shi ne wanda ya auku a ranar Talata a jihar Borno, sakamakon ambaliyar Maiduguri inda fursunoni 289 suka tsere bayan rushewar wani ɓangare na ginin gidan yarin birnin. Wani jami'i da aka zanta da shi game da lamarin, ya tabbatar da cewa, wasu kwamandodin Boko Haram da ke tsare…
Read More