15
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS sai da ta gayyaci shugabanta, Joe Ajaero kafin ta kama shi kasancewar bai amsa ba. Ta bayyana hakan a matsayin ƙarya da kuma salon ruɗar al'umma, ta na mai cewa Ajaero na da tarihin amsa gayyata daga hukumomi. A kwanakin baya ne aka kama Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja akan hanyarsa ta zuwa Burtaniya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci ta TUC. Yayin da DSS ta ke samun suka game da…
