Babaji

5715 Posts

Yadda kwamitin gudanarwa na PDP ya fifita ɓangaren Wike kan na gwamnoni a Jihar Ribas

Daga BELLO A BABAJI Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙarfafa matsayinsa a rikicin shugabancin jam'iyyar PDP bayan da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya tabbatar da tawagarta mambobinta a jihar Ribas. Baya ga nasarar haka ga ƴan ɓangaren Wike, sun kuma dakatar da zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa saboda gujewa sauya hukuncin wanda da farko an shirya yin sa ne a ranar 26 ga watan Satumba inda daga bisani aka mayar da shi ranar 24 ga watan Oktoba. Kwamitin gudanarwar ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam'iyyar, Umar Damagum ya yi hukuncin a yayin wani zama a hedikwatar PDP da ke Flazar…
Read More

Ambaliyar Borno: Halin da muka tsinci kanmu a ciki – Mazauna Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI Wasu daga cikin wanɗanda suka tsira daga ambaliya mafi muni da aka yi a tsawon shekaru 30 a Maidugurin Jihar Borno sun bayyana yadda suka tsira daga iftila'in. Mamakon ruwan sama wanda aka fara a ranar Litinin da dare ya yi sanadiyar batsewar tafkin Alua wanda ya fasa wani yanki tare da haifar da ambaliya acikin garin na Maiduguri inda ya ɗaiɗaita gidaje, makarantu da asibitoci a birnin. Sai dai, yayin da dama daga cikin mutanen yankunan suka tsira, akwai iyalai masu yawa da suka watse sakamakon ambaliyar. Wani mai suna Abubakar Tijjani da lamarin ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ware Litinin a matsayin ranar hutu don bikin Maulidi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin lokacin hutu ga ma'aikata don bikin zagayowar ranar Maulidin haihuwar Annabi Muhammad (SAW). Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya faɗi hakan a madadin Gwamnatin Tarayya inda ya ce, ya na taya al'ummar musulmi na gida da waje murnar bikin. Cikin wata takarda da Sakatariyar Ma'aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar, ta ce, Tunji-Ojo ya yi kira ga al'ummar Musulmi da ƴan Nijeriya baki ɗaya su kasance masu haƙuri da sadaukarwa. Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani…
Read More

Ronaldo ya zama mafi shahara a kafar sada zumunta bayan samun mabiya biliyan ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan samun jimillar mabiya biliyan ɗaya a shafukansa na sada zumunta. Ganin haka ya sa Ronaldo yi yi godiya ga magoya bayansa tare da jinjina mu su kan soyayyar da suke nuna masa a lokacin da ya ke haskawa a fagen ƙwallo. Ronaldo, wanda a halin yanzu ɗan wasa ne na ƙungiyar AL Nassr ta ƙasar Saudiyya, ya bayyana a shafinsa na X cewa hakan ya samu ne sakamakon soyayyar da shi da magoya bayan nasa ke wa tamola. Ɗan wasan yana da…
Read More

PDP ta dakatar da Dino Melaye kan ayyukan zagon-ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kogi, ta dakatar da ɗaya daga cikin manyan ƴaƴanta, Dino Melaye kan zarginsa da ayyukan zagon-ƙasa. Dino, wanda tsohon Sanata ne, an dakatar da shi ne daga Gunduma ta ɗaya ta Ayetoro Gbede bayan ƙin amsa gayyatar da aka yi masa. Jagoran Gundumar na jam'iyyar ya ce an dakatar da shi ne sakamakon yin ayyukan da suka shafi zagon-ƙasa da kuma zarginsa da rashin yin biyayya. Haka nan, an yi hukuncin ne yayin nazari game da rahoton kwamitin ladabdtarwa na jam'iyyar wanda aka wakilta ya yi bincike akan zargin da ake ma…
Read More

Al’umma sun fara koma wa gidajensu yayin da ake samun sassauci a ambaliyar Maiduguri – NEMA

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar bada agaji ta gaggawa, NEMA ta ce ambaliyar Maiduguri ta soma janyewa yayin da mutane suka fara koma wa gidajensu. Darakta-Janar ta hukumar, Zubaida Umar a lokacin da ta ke bada bayanai game da yanayin al'amarin, ta bayyana cewa, ambaliyar ita ce mafi muni a tarihin Nijeriya kamar yadda ya ke a wata takarda da ta fitar. Ta ce, kawo yanzu akwai sauran ayyukan da basu kammala ba inda za su cigaba da kula da bada bayanai game da halin da ake ciki. Ta kuma ce, gwamnatin jihar ta samar da sansani guda takwas ga…
Read More

Gwamnatin Katsina za ta ƙara ɗaukar jami’an tsaro na gida aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A zaman da ta yi karo na tara, majalisar zartarwa ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da kashe Naira 1.5b wajen ɗaukar sabbin jami'an tsaro na cikin gida a jihar. Kwamishinan tsaro na jihar, Dakta Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar. Ya ce, za a yi amfani da kuɗin ne wajen horas da jami'an tsaron tare da sama musu kayan da za su gudanar da ayyukan tsaro a ƙananan hukumomi goma da ƴan ta'adda ke yin ta'addanci. Ɗanmusa ya bayyana sunayen ƙananan hukumomin waɗanda suka…
Read More

Gwamnatin Katsina ta fara gina gidaje 350 ga ƴan gudun hijira a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin jihar Katsina da haɗin-gwiwar gwamnatin tarayya, ta fara gina gidaje guda 350 a wasu ƙananan hukumomin da ƴan ta'adda suka ɗaiɗaita. Ƙananan hukumomin sun haɗa da Ɗanmusa, Batsari, Ɗandume da kuma Faskari. Mai taimaka wa gwamnan na musamman kan lamuran ƴan gudun hijira, Alhaji Sa'idu Ibrahim Koguna Jibiya ya bayyana wa manema labarai hakan a Katsina. Ya ce, tuni gwamnatin Katsina ta biya nata kason yayin da ta ma gwamnatin tarayya na na ƙoƙarin biyan nata domin aikin ginin ya cigaba don a kammala akan lokaci. Alhaji Sa'idu Ibrahim ya ce, gwamnatin Katsina tana…
Read More

Yadda Isra’ila ke cigaba da cin karenta ba babbaka a yaƙinta da Palestine

Daga BELLO A. BABAJI Bayan shafe tsawon kwanaki 342 ƙasar Isra'ila na buɗe wuta wa makofciyarta ta Palastine, sojojin Isra'ila ƙarƙashin jagorancin shugabannin siyasa da na soji tare da taimakon Amurka, na cigaba da kisan kiyashi da rushe gine-gine da ɗaiɗaita al'ummar Palestine a wani yunƙuri na ramuwar gayya. Cikin wata takarda da Jakadan Palestine, Abdullah Abu Shawesh ya fitar, ya ce haɗin-gwiwa tsakanin Isra'ila da Amurka akan mutanen Palestine na ɗaya daga cikin mummunan yanayi da aka taɓa shiga a tarihi kamar yadda ƙididdiga ta nuna. Ya ce, ƙasashen da a duniya suke ikirarin sun fi kowa ƙoƙarin kare…
Read More

Tinubu ya gana da Sarki Charles na uku a Fadar Bakinham da ke birnin Landan

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga sarkin Ingila, Sarki Charles na uku a Fadar Bakinham da ke birnin Landan don gudanar da ganawa ta kai-da-kai a wani mataki da ke nuni da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da ƙasar Ingila. A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samo, wannan ita ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu tun bayan haɗuwarsu a wajen taron canjin yanayi karo na 28 da aka yi a bara a ƙasar Dubai. Ganawar ta yanzu ta biyo bayan amsa gayyatar da sarkin na Ingila ya yi ma sa. Shugabannin sun tattauna…
Read More