03
Jul
Daga BUHARI FAGGE Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi gwamnatin tarayya ta koma amfani da fasahar zamani a yaƙin da take yi da mayaƙan Boko Haram da ƴan bindiga. Hakan na ƙunshe cikin ƙudurin da Sanata Ali Ndume ya gabatar don ɗaukar matakin gaggawa kan harin da aka kai a yankin Gwoza da yake wakilta. Bayan doguwar muhawara da aka kwashe sa'o'i ana yi tare da jajentawa kan harin, majalisar ta yarda cewa amfani da fasahar zamani a yaƙin zai kawo ƙarshen masu kai hare-haren ƙunar baƙin wake. BBC Hausa ta ruwaito cewa, Majalisar ta amince a ƙara bayar da muhimmanci…
