13
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya amince da samar da sabuwar gunduma da ta ƙunshi ƙauyuka guda takwas a Ƙaramar Hukumar Dandi da ke jihar. Haka kuma, gwamnan ya amince da samar da sabon jagorancin ƙauye a Ƙaramar Hukumar Augie a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa gwamnatin gargajiya da inganta shugabanci daga tushe a jihar. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomin da Sarauta, Alhaji Garba Umar Dutsinmari ne ya sanar da haka a wata takarda a Birnin Kebbi, ranar Alhamis. A cewar kwamishinan, an kafa sabuwar Gundumar Buma ne daga Gundumar Dolekaina ta Ƙaramar Hukumar…
