12
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla ɗalibai guda 830 ne tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya ɗauki nauyin yaye su bayan kammala karatun NCE daga Community College of Education da ke Kano, a wani yanayi na bunƙasa ilimin malamai da inganta ɗan-adam a jihar. A safiyar ranar Asabar ne aka gabatar wa ɗaliban shaidar kammala karatun nasu, wanda aka gudanar a ɗakin taro na School of Arabic Studies (SAS) a Kano, wanda kuma ya kawo nasarar kammala shirin ɗaukar nauyi karatu da Shekarau ya samar a 2022 a lokacin da yake…
