ukarofi

12498 Posts
Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu – Rauf Aregbesola

Ban taɓa cin amanar matata ba tun bayan aurenmu – Rauf Aregbesola

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa tun bayan da ya auri matarsa, Sherifat, bai taɓa yin wata alaƙar soyayya ko ta kusanci da wata mace ba. Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar ADC a wani gangamin yaƙin neman zaɓe da aka gudanar a ƙaramar Hukumar Ejigbo ta Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga Agusta, 2026. Tsohon gwamnan, wanda ya yi jawabin ne da harshen Yarbanci, ya ce tsoron Allah da kuma alƙawarin…
Read More
Tinubu ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da muryarsu wajen yaƙi da ta’addanci

Tinubu ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da muryarsu wajen yaƙi da ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga malaman addini a Nijeriya, Afirka da sauran sassan duniya da su ci gaba da anfani da muryoyinsu kan yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma amfani da addini wajen kashe-kashe da tashin hankali. Tinubu ya ce babu wata ibada ta gaskiya da za ta samu ci gaba ta hanyar zubar da jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Shugaban ƙasar ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Kano, a cikin saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata…
Read More
A Ringim shekaru 50 al’umma na fama da matsalolin lafiya — Garba Dabi

A Ringim shekaru 50 al’umma na fama da matsalolin lafiya — Garba Dabi

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, Hon. Badamasi Garba Dabi, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun shafe kusan shekaru 50 suna fama da matsaloli a fannin kiwon lafiya, kafin zuwansa shugabancin ƙaramar hukumar. Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa da ke Sakatariyar ƙaramar Hukumar Ringim, Hon. Badamasi Garba Dabi ya ce tun bayan da Allah (A.W.T) Ya ɗora masa nauyin jagorantar al’ummar yankin, ya mayar da hankali wajen sauraron koke-kokensu da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar su. Ya ce daga cikin muhimman fannoni da ya ba…
Read More
Kano ta zama cibiyar nazarin NIPSS kan tattalin arziƙi da kasuwanci

Kano ta zama cibiyar nazarin NIPSS kan tattalin arziƙi da kasuwanci

Daga RABIU SANUSI a Kano Jihar Kano ta zama cibiyar wani muhimmin bincike da Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun ƙasa ta Nijeriya (NIPSS) ke gudanarwa, domin tantance irin gudunmawar da jihar ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, samar da ayyukan yi da haɓaka harkokin kasuwanci. Tawagar NIPSS, wadda ta ƙunshi mahalarta Babban Darasin Gudanarwa na 48, Rukuni na ɗaya, ta fara ziyarar nazari ta tsawon mako guda a Kano, inda za ta tattauna da gwamnati, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki. Shugaban tawagar, mai ritaya Birgediya Janar Jimo, MNI, ya bayyana cewa binciken ya mayar da hankali…
Read More
Nijeriya ta kashe tiriliyan N3.14 wajen biyan bashin cikin gida a zangon farko na 2026 – DMO

Nijeriya ta kashe tiriliyan N3.14 wajen biyan bashin cikin gida a zangon farko na 2026 – DMO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin Kula da Basussukan ƙasa (DMO) ta ce Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira tiriliyan 3.14 wajen biyan bashin da ta biyo na cikin gida a zangon farko na shekarar 2026. Jaridar Tribune ta rawaito cewa wannan na ƙunshe a cikin rahoton da DMO ta fitar kan basukan da ake bin gwamnatin Nijeriya a cikin gida, inda ya baiyana cewa cikin kudin, an kashe Naira tiriliyan 2.97 wajen biyan kudin ruwa na bashin, yayin da aka biya Naira biliyan 169.68 a matsayin wani bangare na gundarin bashin. A watan Janairu, gwamnati ta kashe Naira biliyan…
Read More
Yadda na samu rancen biliyan N2.5 domin zuba jari a harkar noma — Buni

Yadda na samu rancen biliyan N2.5 domin zuba jari a harkar noma — Buni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana yadda ya samu rancen Naira biliyan 2.5 daga Bankin Noma na ƙasa (BoA) da Bankin Masana’antu (BoI) jim kaɗan bayan hawansa mulki a shekarar 2019, domin zuba jari a harkar noma da bunƙasa tattalin arzikin jihar. Buni ya ce ya samu Naira biliyan biyu daga Bankin Masana’antu, yayin da ya samu ƙarin Naira miliyan 500 ta wani shirin shiga tsakani na Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda Bankin Noma ya jagoranta. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Gidan Gwamnatin Jihar Yobe da…
Read More
’Yan bindiga sun kai hari Alƙaleri, sun jikkata mutane, sun kwashe shanu

’Yan bindiga sun kai hari Alƙaleri, sun jikkata mutane, sun kwashe shanu

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi Mazauna yankin Fego da Ruga Maikasuwa da ke ƙasar Gwana a ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi, sun nemi taimakon gwamnatin jihar da hukumomin tsaro bayan ’yan bindiga sun kai musu hari a tsakiyar daren Asabar zuwa wayewar Lahadi. Sheikh Yusuf Bello Gafaka, wani malami daga ƙasar Gwana, ya shaida wa wakilinmu a Bauchi cewa ’yan bindigar sun sake kai hari yankin ne kamar yadda suka yi a watannin baya, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankin yin hijira zuwa Jihar Gombe da wasu garuruwa domin tsira da rayukansu. Ya ce bayan ɗaukar tsauraran…
Read More
Kaunar ƙasa ce ta sa na shirya juyin mulki kan Tinubu – Kanar Ma’aji

Kaunar ƙasa ce ta sa na shirya juyin mulki kan Tinubu – Kanar Ma’aji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kanar Mohammed Ma’aji na Rundunar Sojin Nijeriya, wanda ake zargi da jagorantar wani shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar juyin mulki, ya bayyana cewa abin da ya sa aka shirya shirin ba wata buƙata ta neman mulki ba ce, sai dai abin da ya kira kishin ƙasa da damuwa kan tabarbarewar tsaro da tattalin arzikin ƙasar. An gano shirin ne a watan Satumba na 2025 kafin a aiwatar da shi, lamarin da ya haifar da kama da binciken jami’an soja masu ci da waɗanda suka yi ritaya, da kuma wasu…
Read More
Daliba ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa huɗu

Daliba ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ɗalibar Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Nijeriya mai shekara 23, Faith Alayande, ta rasu bayan ta faɗo daga saman ginin ɗakunan kwanan ɗalibai mai hawa huɗu a harabar makarantar da ke yankin Victoria Island a Jihar Legas. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 7 ga Agusta 2026. Kakakin rundunar, Abimbola Adebisi, ta ce mai kula da ɗakunan kwanan ɗaliban ce ta sanar da ’yan sanda bayan an gano ɗalibar ba ta cikin hayyacinta a harabar makarantar. A cewar Adebisi, wata ɗaliba da wani…
Read More
Yadda uwargidan Adeleke ta jagoranci zanga-zangar mata akan rikice-rikice a Jihar Osun

Yadda uwargidan Adeleke ta jagoranci zanga-zangar mata akan rikice-rikice a Jihar Osun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar. Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo. Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da…
Read More