ukarofi

12500 Posts
Daliba ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa huɗu

Daliba ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ɗalibar Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Nijeriya mai shekara 23, Faith Alayande, ta rasu bayan ta faɗo daga saman ginin ɗakunan kwanan ɗalibai mai hawa huɗu a harabar makarantar da ke yankin Victoria Island a Jihar Legas. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 7 ga Agusta 2026. Kakakin rundunar, Abimbola Adebisi, ta ce mai kula da ɗakunan kwanan ɗaliban ce ta sanar da ’yan sanda bayan an gano ɗalibar ba ta cikin hayyacinta a harabar makarantar. A cewar Adebisi, wata ɗaliba da wani…
Read More
Yadda uwargidan Adeleke ta jagoranci zanga-zangar mata akan rikice-rikice a Jihar Osun

Yadda uwargidan Adeleke ta jagoranci zanga-zangar mata akan rikice-rikice a Jihar Osun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar. Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo. Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da…
Read More
Tsaron ƙasa ya fara ne da kula da jin daɗin ‘yan ƙasa  — Sarki Sanusi

Tsaron ƙasa ya fara ne da kula da jin daɗin ‘yan ƙasa  — Sarki Sanusi

Daga RABIU SANUSI a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, CON, ya bayyana cewa tsaron kowace ƙasa yana farawa ne daga kare rayuka, walwala da jin daɗin al’ummarta, yana mai jaddada cewa tsaro bai tsaya kawai kan kare iyakokin ƙasa ba. Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake matsayin uban taron wata gagarumar ƙungiyar ƙa’idar Dokokin Jinƙai ta Duniya da Kwalejin Shari’a ta Jami’ar Northwest Kano suka shirya, inda ya gabatar da babban jawabi mai taken “Jagoranci, Zaman Lafiya da Rawar da Cibiyoyin Gargajiya ke Takawa wajen gina ƙasa.” Mai Martaba ya bayyana cewa bai…
Read More
Adeleke ya zargi Oyetola da matsa wa EFCC ta rufe asusun Jihar Osun

Adeleke ya zargi Oyetola da matsa wa EFCC ta rufe asusun Jihar Osun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola, da kasancewa a bayan matakin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ɗauka na daskarar da asusun gwamnatin jihar. Adeleke ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron Arise Town Hall da aka shirya domin ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta. Gwamnan ya yi zargin cewa Oyetola, wanda a yanzu yake riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Teku, yana amfani da sunan…
Read More
Ƙungiyar kamfen ɗin Mahadi Aliyu za su tafi kotu bisa cire sunan ɗan takarar gwamnan ADC a Zamfara

Ƙungiyar kamfen ɗin Mahadi Aliyu za su tafi kotu bisa cire sunan ɗan takarar gwamnan ADC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kungiyar yaƙin neman zaɓen Mahdi Aliyu Gusau ta ƙi amincewa da ɗora sunan Bilyaminu Shinkafi a shafin yanar gizon hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, a matsayin ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, a Jihar Zamfara. Ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin wata dabarar da ba ta dace ba kuma ta yi alƙawarin ƙalubalantar sa a kotu. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Gusau ranar Juma'a, wadda ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ta sanya wa hannu, ta dage cewa Mahdi Gusau shine halartaccen ɗan takarar gwamna na ADC a…
Read More
Kwamishina ya yabi malaman tsangaya kan goyon bayan Inuwa da Jamilu gwamna a 2027

Kwamishina ya yabi malaman tsangaya kan goyon bayan Inuwa da Jamilu gwamna a 2027

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ƙananan hukumomi na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya yaba wa malaman tsangaya na jihar bisa goyon bayan da suka bayyana wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna a zaɓen 2027. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani babban taro da ƙungiyar malaman tsangaya ta jihar ta gudanar, inda malaman suka bayyana aniyarsu ta mara wa Dakta Jamilu Gwamna baya tare da tabbatar masa da ƙuri’u 150,000 a zaɓen 2027. Ya ce matakin malaman na…
Read More
Osun 2026: INEC ta fara rarraba kayan zaɓe masu muhimmanci

Osun 2026: INEC ta fara rarraba kayan zaɓe masu muhimmanci

Daga USMAN KAROFI Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fara rarraba muhimman kayan zaɓe zuwa ƙananan hukumomi 30 na Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 15 ga Agusta 2026. Kwamishinan INEC mai kula da zaɓen Osun, Kunle Ajayi, ya bayyana cewa ana gudanar da rabon kayan ne daga ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Osogbo, babban birnin jihar. Ajayi ya ce an samu jinkirin rarraba kayan zaɓen ne sakamakon jinkirin isowar sabbin takardun kaɗa ƙuri’a da sauran kayan zaɓe daga Abuja. Ya bayyana cewa an sake buga takardun ne bayan…
Read More
Chadi za ta bai wa ƙasashen Afirka izinin shiga ƙasar babu biza

Chadi za ta bai wa ƙasashen Afirka izinin shiga ƙasar babu biza

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jamhuriyar Chadi ta sanar da cewa daga 1 ga Janairu, 2027, ’yan ƙasa daga dukkan ƙasashen Afirka za su samu damar shiga ƙasar ba tare da neman takardar izinin shiga ƙasa, wato biza, ba. Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙasar na ƙarfafa haɗin kan Afirka da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin ƙasashen nahiyar. Deby ya bayyana cewa cire takunkumin biza zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen Afirka, tare da sauƙaƙa tafiye-tafiye daga wata ƙasa zuwa wata. A cewarsa, wannan manufa ta nuna yadda Chadi ke…
Read More
Bankin Lotus ya shiga tsaka-mai-wuya da hukumar NDPC kan zargin ɗaukar bayanan ɗalibai

Bankin Lotus ya shiga tsaka-mai-wuya da hukumar NDPC kan zargin ɗaukar bayanan ɗalibai

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Bankin Lotus ya shiga tsaka mai wuya bisa fuskantar binciken ƙwararru daga Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC) bisa zargin cewa an yi amfani da bayanan sirri na wasu ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba wajen buɗe musu asusun banki ba tare da ingantaccen tushe na doka ba. Hukumar ta kuma fara bincike kan Jami’ar Legas (UNILAG) da kamfanin Hackerbella Ltd, domin gano irin rawar da kowannensu ya taka wajen tattarawa, amfani da su, bayyana wa wasu ko sarrafa bayanan sirrin ɗaliban da lamarin ya shafa. Shugaban Sashen Shari’a, Tilasta Bin Doka da ƙa’idoji na NDPC, Babatunde…
Read More
Dangote na burin samun Dala biliyan 100 duk shekara nan da 2030

Dangote na burin samun Dala biliyan 100 duk shekara nan da 2030

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, kamfanin zai iya cimma burinsa na samun Dala biliyan 100 a matsayin kuɗaɗen shiga a duk shekara nan da shekarar 2030. Dangote ya ce, cikakken nazari da ƙididdigar cikin gida da mahukuntan kamfanin suka gudanar ya ƙara musu tabbacin wannan buri na samun Dala biliyan 100 a shekara cikin shekaru huɗu masu zuwa abu ne da za a iya cimmawa. Ya bayyana hakan ne yayin da manyan jami’an Goldman Sachs, ɗaya daga cikin fitattun bankunan zuba jari da kamfanonin hidimomin kuɗi na duniya, suka…
Read More