ukarofi

12500 Posts
Karramawar Blueprint ta ƙara mana ƙaimin taka-tsantsan da kuɗin al’umma – Gwamna Namadi

Karramawar Blueprint ta ƙara mana ƙaimin taka-tsantsan da kuɗin al’umma – Gwamna Namadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karɓi lambar yabo ta Blueprint Newspapers ta shekarar 2025 kan kula da kuɗaɗen gwamnati da sauye-sauyen harkar noma, yana mai cewa karramawar za ta ƙara wa gwamnatinsa ƙwarin gwiwar yin taka-tsantsan da ci gaba da yin amfani da albarkatun jama’a cikin tsanaki da bunƙasa harkar noma. Gwamnan Namadi ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa mai kwanan watan 5 ga Agusta, 2026, wacce Babban Sakataren Ofishinsa na Musamman, Adamu M. Garun-Gabas, ya sanya wa hannu, a matsayin martani ga wasiƙun da Blueprint Newspapers Limited ta aiko masa…
Read More
Zaɓen Osun: Sufeto Janar ya tura DIG Ishyaku domin jagorantar tsaro

Zaɓen Osun: Sufeto Janar ya tura DIG Ishyaku domin jagorantar tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Disu, ya tura Muƙaddashin Babban Sufeto Janar, DIG Ishyaku Mohammed, zuwa Jihar Osun, domin jagorantar daidaita ayyukan tsaro yayin zaɓen gwamnan njihar da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (FPRO), CSP Anietie Iniedu, ya fitar a Abuja, ya ce tura babban jami’in na daga cikin matakan da rundunar ta ɗauka domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya, tsaro da sahihanci a faɗin jihar. Ya ce, DIG Ishyaku Mohammed…
Read More
Na haihu a hanyar tsere wa ’yan bindiga, inji ‘yar gudun hijira a Sakkwato

Na haihu a hanyar tsere wa ’yan bindiga, inji ‘yar gudun hijira a Sakkwato

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD  Wata mata da ’yan bindiga suka tilasta wa barin gidanta a ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato, ta bayyana irin mummunan halin da ta shiga, inda ta ce ta haifi jaririnta a kan hanya yayin da take tserewa daga hare-haren ’yan bindiga da suka mamaye garinsu tare da ƙona gidaje. Matar ta bayyana haka ne cikin harshen Hausa yayin wata tattaunawa da Iconic FM, inda ta ce hare-haren sun lalata dukiyoyin iyalansu, har ta kai ga ba ta da isasshen kayan da za ta yi amfani da su wajen ɗaukar jaririn da ta haifa. A cewarta,…
Read More
Akwai buƙatar tuntuɓar manoma a shirin ba da tallafin taki na gwamnatin Kano— Maikuɗi Kadawa

Akwai buƙatar tuntuɓar manoma a shirin ba da tallafin taki na gwamnatin Kano— Maikuɗi Kadawa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An shawarci gwamnatin Kano da sauran gwamnatoci har zuwa matakin tarayya da su riƙa tuntuɓar manoma na haƙiƙa kafin su raba tallafin noma, musamman takin zamani da sauran kayan aikin gona kamar taraktoci da makamantansu. An bayyana cewa akwai buƙatar gwamnatoci su riƙa tuntuɓar ƙungiyoyin manoma na gaskiya waɗanda aka tabbatar da cewa manoma ne, domin samun nasarar duk wani shiri na tallafin noma da kuma cimma manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziki, samar da abinci da ci gaban jihohi da Nijeriya baki ɗaya. Wannan shawara ta fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar Masu Sayar…
Read More
Muna taimaka wa masu Umrah wajen samun ƙarin arziƙi — Baba Gambo

Muna taimaka wa masu Umrah wajen samun ƙarin arziƙi — Baba Gambo

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban UBJ Group, Uzairu Baba Gambo ESK, ya bayyana cewa an kafa kamfanin ne domin taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Nijeriya, musamman masu gudanar da harkokin Makka da Umrah. Uzairu Baba ya ce kamfanin na daga cikin masu gudanar da harkokin da suka samu amincewar hukumomin da abin ya shafa wajen taimaka wa maniyyata da masu Umrah wajen samun kayayyakin da suke buƙata a Makka, Madina da sauran wurare a ƙasar Saudiyya, da kuma a Nijeriya. Ya ce mutanen da suka yi hulɗa da kamfanin na iya samun riba mai yawa tare da samun…
Read More
Yadda Boko Haram da ISWAP ke yaƙar juna kan neman iko a Tafkin Chadi

Yadda Boko Haram da ISWAP ke yaƙar juna kan neman iko a Tafkin Chadi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rikicin da ya daɗe tsakanin ƙungiyar ISWAP da Boko Haram na ci gaba da sauya yanayin tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya. ƙungiyoyin biyu na fafatawa mai zafi domin mallakar yankuna, samun tasiri da albarkatu. Sabon artabu da aka ruwaito a ranar Juma’a, 7 ga Agusta, ya sake jawo hankali kan mummunan rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, bayan rahotannin cewa mayaƙan ISWAP sun kai wani samame kan Bok Haram a yankin Bula Murge, cikin ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno, inda aka ce an kashe wasu manyan kwamandojin Boko Haram.…
Read More
2027: Tinubu, Atiku, Obi za su biya miliyan N150 kowanne kan allunan talla a Kuros Riba

2027: Tinubu, Atiku, Obi za su biya miliyan N150 kowanne kan allunan talla a Kuros Riba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan takarar shugaban ƙasa da suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su biya kuɗin Naira miliyan 150 kowanne domin kafa allunan tallan kamfen a Jihar Kuros Riba gabanin babban zaɓen 2027. Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamu ta Jihar Kuros Riba (CRISSAA) ce ta bayyana sabon tsarin kuɗin tallan siyasa na waje da za a biya a jihar. Daraktan-Janar na hukumar, Ubong Sam, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da Majalisar Shawarar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a Calabar, inda ya yi bayanin sabon tsarin kuɗaɗen. A…
Read More
Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in Kano biyu

Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in Kano biyu

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin ƙarin albashi ga ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano. An ɗauko sabon tsarin ne daga tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a jami’o’in tarayya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin. Amincewar ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta…
Read More
Sojojin Nijeriya sun ce sun ceto fasinjoji 33 da aka sace a Zamfara

Sojojin Nijeriya sun ce sun ceto fasinjoji 33 da aka sace a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar sojin Najeirya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun ceto mutum 33 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, bayan samun sahihan bayanai kan sace fasinjojin da ke tafiya ta yankin Magazu. Sanarwar da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ta ce sojojin tare da 'yan sanda a Tsafe sun samu bayanin lamarin ne da yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026. Nan take dakarun suka nufi wurin da lamarin ya faru, inda suka ci karo da maharan suna tafiya…
Read More
An rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna

An rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya, NERC, ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric, sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa. NERC ta ce matakin ya fara aiki daga ranar 10 ga Agustan 2026, bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta shekarar 2023. Hukumar ta ce kamfanin ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, lamarin da ya sa jimillar bashin da ke kansa ya kai kusan naira biliyan 456.5. NERC ta…
Read More