ukarofi

12500 Posts
Sanata Yar’adua ya yi na’am da komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC a Katsina

Sanata Yar’adua ya yi na’am da komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana farin cikinsa game da sauya shekar da tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa ya yi daga jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC. A wata sanarwara da ya fitar, Sanatan ya bayyana dawowar Dr. Mustapha a matsayin babban karin ƙarfi ga jam’iyyar APC da kuma alamar ƙaruwar amincewar al’umma ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa. A cewarsa, "Na sami labarin dawowar babban ɗan’uwana, Dr. Mustapha Inuwa, zuwa jam’iyyar APC da…
Read More
Hukumar DSS na shirin ɓullo da sabbin dabaru na shawo kan matsalar tsaro a Arewa maso Yamma

Hukumar DSS na shirin ɓullo da sabbin dabaru na shawo kan matsalar tsaro a Arewa maso Yamma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Daracktocin hukumar tsaro na farin kaya na Arewa maso Yamma da ya ƙunshi jihohi 7 sun fara gudanar da taro a Katsina domin ƙara haɗin kai da ɓullo da shirin sabbin dabarun shawo kan matsalar tsaro a yankin. A jawabin sa Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa matsalar tsaro da yadda ake tunkarar matsalar a jihohin Arewa maso Yamma yakamata ya zama bai ɗaya domin haka ya yaba wa hukumar DSS da sauka shirya wannan taro mai taken haɗa kai don yaƙar ta'addanci(United against Terror). Gwamnan ya yaba wa da haɗin kai…
Read More
Ranar matasa ta duniya: Mahdi ta yi kira da a ƙarfafa matasa domin gina ƙasa

Ranar matasa ta duniya: Mahdi ta yi kira da a ƙarfafa matasa domin gina ƙasa

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata mai fafutukar kare muradun matasa, Halima Ahmed Mahdi, ta yi kira ga gwamnatoci, iyaye, al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa matasa tare da samar musu da damammaki domin su taka rawar gani wajen ci gaban ƙasa. Mahdi ta yi wannan kiran ne a cikin saƙonta na bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026, inda ta bayyana matasa a matsayin wani muhimmin ɓangare na al’umma da ke da kuzari, buri da kuma damar jagorantar ci gaba. Ta ce matasa da dama na neman ilimi da koyon sana’o’i, yayin da wasu ke…
Read More
AGILE ta yaye ɗalibai ‘yan mata 1,868 a fannin ilimi a Zamfara

AGILE ta yaye ɗalibai ‘yan mata 1,868 a fannin ilimi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jimillar 'yan mata da matasa mata 1,868 sun kammala karatunsu daga rukunin farko na shirin ilimi na AGILE, Subcomponent 2.2C. An gudanar da bikin kammala karatun ne a Otal din Falala da ke Gusau yau Alhamis. Da take gabatar da jawabin maraba, mai kula da ayyukan AGILE na Zamfara Hajiya Sa'adatu Abdu Gusau, ta bayyana taron a matsayin damammaki da mata suka samu. "An gudanar da shirin na tsawon watanni 10 a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar," in ji ta. Ta bayyana cewa shirin ya haɗa ilimin karatu da lissafi tare da dabarun rayuwa,…
Read More
NVMA ta yaba wa Gwamna Lawal kan aiwatar da ƙarin albashin CONMESS ga likitocin dabbobi a Zamfara

NVMA ta yaba wa Gwamna Lawal kan aiwatar da ƙarin albashin CONMESS ga likitocin dabbobi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya, NVMA, reshen Jihar Zamfara ta yaba wa Gwamna Dr. Dauda Lawal saboda amincewa da aiwatar da sabon tsarin albashin likitanci mai haɗaka, CONMESS, ga likitocin dabbobi a jihar. Shugaban ƙungiyar, Dr. Mukhtar Salihu Anka, PhD, ya sanar da hakan ga 'yan jarida a Gusau yau Alhamis. Dr. Anka ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmi ga aikin likitocin dabbobi a Zamfara, yana mai jaddada matakin da wata jajircewar gwamnati ga walwalar ma'aikata, ƙwarewa da kuma ci gaban fannin dabbobi. A cewarsa, aiwatar da sabon tsarin albashin ya magance damuwar da…
Read More
Kishin garinmu Daƙayyawa ne ya sa na rubuta littafin ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’ – Na’ima Sulaiman

Kishin garinmu Daƙayyawa ne ya sa na rubuta littafin ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’ – Na’ima Sulaiman

"Na fi yin rubutu akan abubuwan da marubutanmu ba su fiye yin rubutu akai ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  (Ci gaba daga makon jiya) Marubuciya Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ba ɓoyayyiya ba ce a tsakanin matasan marubutan Hausa a Jihar Jigawa. Ta fito ne daga ƙaramar Hukumar Kaugama. Tana da gogewa a harshen Larabci da Hausa, inda yanzu haka take karatun digirinta na biyu a Jami'ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa. Marubuciya ce da ta bambanta da sauran marubutan adabi, saboda ita ta fi mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa na tarihi ko al'adu. Akasari rubuce-rubucen da ta yi sun…
Read More
Yadda garin Lokoja ya zama babban birnin Nijeriya kafin Legas da Abuja

Yadda garin Lokoja ya zama babban birnin Nijeriya kafin Legas da Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Blueprint Manhaja na ci gaba da kawo wa masu karatu shafinsa na tarihi domin waiwayar muhimman abubuwan da suka taka rawa wajen gina tarihin Nijeriya, musamman waɗanda ba kasafai ake ba su kulawar da ta dace ba. A wannan makon, mun duba tarihin garin Lokoja, birnin da ya kasance cibiyar mulkin Turawan Birtaniya a farkon mulkin mallaka. Duk da cewa Legas ce aka fi sani a matsayin tsohon babban birnin Nijeriya, tarihi ya nuna cewa kafin hakan, Lokoja ce ta kasance cibiyar gudanar da harkokin gwamnatin Turawa a yankin da daga bisani ya zama Nijeriya. Ta…
Read More
Illar ƙazantar wurin kiwo ga lafiyar dabbobi

Illar ƙazantar wurin kiwo ga lafiyar dabbobi

Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D Gabatarwa: Tsaftar muhalli na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar dabbobi da haɓaka yawan amfanin kiwo. ƙazantar wurin kiwo na haifar da taruwar ƙwayoyin cuta da ƙwari da gurɓataccen ruwa, waɗanda ke haddasa cututtuka da rage ƙarfin dabbobi da ingancinsu. Duk lokacin da aka bar wurin kiwo da ƙazanta ba tare da kula ba to tabbas waɗannan matsalolin ne za su faru.  1. Yaɗuwar cututtukan ƙwayoyin cuta Taruwar kashin dabbobi da fitsari na samar da muhalli mai kyau ga ƙwayoyin cuta irin su Salmonella, Escherichia coli (E. coli) da Clostridium. Waɗannan ƙwayoyin cuta…
Read More
Gwamnatin Kebbi za ta kula da iyalan ‘yan sanda da suka rasu bakin daga

Gwamnatin Kebbi za ta kula da iyalan ‘yan sanda da suka rasu bakin daga

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamnatin jihar Kebbi ta jaddada ƙudirin ta na kulawa da iyalan 'yan sanda da suka rasu a bakin daga yayin artabu da 'yan ta'adda a ƙaramar hukumar mulki ta Sakaba. Ya yi wannan bayanin ne jiya a fadar gwamnatin jihar yayin da ya ke karɓar baƙuncin wata tawaga daga ofishin Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya Mista Olatunji Disu ƙarƙashin jagorancin mataimakin Sufeto Janar Umar Dada don jajentawa gwamnati da kuma al'ummar jihar Kebbi. Gwamna Malam Nasir Idris ya jajentawa rundunar 'yan sanda tare da bayyana cewa rayuwar su ba ta tafi a banza ba…
Read More
Gwamnatin Kebbi ta raba wa makarantun gaba da sakandare motoci

Gwamnatin Kebbi ta raba wa makarantun gaba da sakandare motoci

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamna Malam Nasir Idris ya raba wa makarantun gaba da sakandare mallakar jihar Kebbi guda bakwai da ke faɗin jihar manyan motoci ƙirar Bas-bas. Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da motocin a gidan Gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi ranar Laraba ɗin nan, gwamna Nasir Idris ya ce wannan ya biyo bayan la'akari da akwai buƙatar motoci musamman ga ɗalibai don ƙara saukaka musu zirga-zirga daga makarantu zuwa wajen kwana musamman waɗanda ke zama a cikin gari da ke da nisa da makarantu. Ya ce yana fata hukumomin makarantun za su riƙe motocin tare…
Read More