ukarofi

12500 Posts
An buƙaci gwamnatin Gombe ta bai wa matasa masu sa-kai fifiko wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro

An buƙaci gwamnatin Gombe ta bai wa matasa masu sa-kai fifiko wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ƙungiyar BREACH Initiative for Leadership Development ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da ta bai wa matasan da suka yi aiki a ƙungiyoyin sa-kai masu sanya kayan aiki na musamman fifiko a duk lokacin da za a ɗauki sabbin jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro. Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a yayin gasar fareti da aka gudanar a Gombe domin bikin ranar matasa ta duniya ta shekarar 2026. Da yake jawabi a wajen taron, tsohon daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) a Jihar Gombe, Ado Solomon, ya ce mambobin…
Read More
Annobar karuwanci a ƙasar Hausa

Annobar karuwanci a ƙasar Hausa

(Ci gaba daga makon jiya) Daga MUKHTAR YAKUBU  "Shekara ta takwas kenen ina sana'ar karuwanci amma ba abinda na amfana da shi," in ji wata karuwa Da yake ba wannan ne ya fi damu na na sani ba, nan take sai na katse ta da tambayarta, duk tsawon shekarunta da take wannan sa'ar, wacce riba ta taɓa samu kuma wacce wahala ta taɓa fuskanta, kuma ko tana tunanin barin sana'ar nan gaba idan ta samu kudi ko mijin aure?  Sai ta ce, "Ni dai yanzu ina jin ina cikin shekaruna na takwas kenen a cikin wannan sana'ar ta karuwanci, kuma…
Read More
Gyaran farce bisa tsari: Karamar hanya da ke kare lafiyar ƙafa

Gyaran farce bisa tsari: Karamar hanya da ke kare lafiyar ƙafa

Daga AISHA ASAS Akwai wasu abubuwa da muke yi a kullum waɗanda muke ɗauka ba su da wani tasiri mai yawa a rayuwa. Daga cikinsu akwai yadda muke kula da farcen ƙafa. Ga mutane da dama, gyaran farce wani ɓangare ne na tsafta kawai ko kuma gyaran kwalliya, amma masana lafiya sun nuna cewa yadda mutum yake yanke farcensa na iya taimaka masa wajen kauce wa matsalolin da kan jawo ciwo da wahalar jinya. Kafa na ɗaukar nauyin jiki gaba ɗaya, kuma duk wata matsala da ta shafe ta na iya shafar tafiyar mutum da sauran harkokinsa na yau da…
Read More
Zamfara AGILE ta gudanar da horarwa na kwanaki biyu

Zamfara AGILE ta gudanar da horarwa na kwanaki biyu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Shirin inganta Ilimin 'yan matan Zamfara AGILE, ya fara horo na kwana biyu yau Talata, a Taula Apartment da ke Gusau ga 'yan kwangila, ma'aikatan gini, injiniyoyi da kuma masu ba da shawara kan kula da muhalli. Bitar ta mayar da hankali kan aiwatar da shirye shiryen gudanar da muhalli da zamantakewa, ESMPs, a fadin wuraren aikin AGILE a jihar. Da yake buɗe taron bitar, mataimakin mai gudanar da ayyukan hukumar ta AGILE a Zamfara, Dr. Salisu Dalhatu ya ce manufar ita ce a wayar da kan mahalarta bitar game da haɗurran muhalli da ke…
Read More
Katsina United ta sake tabbatar da mutuwar ɗan wasanta da aka ce ya farfaɗo a ɗakin ajiyar gawarwaki

Katsina United ta sake tabbatar da mutuwar ɗan wasanta da aka ce ya farfaɗo a ɗakin ajiyar gawarwaki

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United da masu sha’awar ƙwallo a jihar Katsina sun shiga jimami bayan da ƙungiyar ta sanar cewa sabon ɗan wasanta, Ozoh Chinedu, wanda a baya ya taka leda a Kano Pillars, ya rasu. Rahotanni sun ce Chinedu ya rasu a safiyar Talata, 11 ga Agusta, 2026, bayan samun matsalar lafiya yayin wasan sada zumunta da Katsina United ta yi da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina. A cikin wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na Katsina United ya fitar, an bayyana cewa an ba ɗan…
Read More
Sufeto-Janar na ‘ yan sanda ya yi ta’aziyya ga iyalan ‘yan sanda da ‘yan ta’adda suka kashe a Kebbi

Sufeto-Janar na ‘ yan sanda ya yi ta’aziyya ga iyalan ‘yan sanda da ‘yan ta’adda suka kashe a Kebbi

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu ya yi ta'aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al'ummar Jihar Kebbi dangane da rasuwar 'yan sanda 10 a fagen fama. Sufeto-Janar Disu ya turo wata tawaga mai karfi ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin Sufeto-Janar mai kula da dabarun yaƙi, DIG Umar Shehu Nadada, zuwa Birnin Kebbi domin gabatar da juyayinsa akan lamarin. A sa'ilin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati, DIG Nadada ya shaida masa cewar, ya zo Kebbi ne bisa umurnin IG Disu dangane da lamarin da…
Read More
Sojoji sun daƙile harin ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun daƙile harin ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar sojin Najeriya ta 17 dake Katsina ta fatattaki wasu 'yan bindiga masu tarin yawa bayan da suka yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Charanci da ke jihar Katsina. Rundunar ta samu nasarar daƙile harin ne bayan ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:20 na safe a ranar Talata da ta gabata, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun taru a kusa da ƙauyen Kaɗɗanya da ke yankin. Zagazola Makama mai sharhi kan tsaro ya bayyana cewa wani rahoton tsaro ya ce sojojin da…
Read More
Ɗan wasan Katsina United da aka sanar da mutuwarsa ya farfado a mutuware

Ɗan wasan Katsina United da aka sanar da mutuwarsa ya farfado a mutuware

Daga UMAR GARBA a Katsina Tun da farko an kai ɗan wasan Katsina United, Chinedu Ozor, sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na babbar asibitin Katsina bayan da aka sanar da mutuwarsa a jiya Talata, bayan ɗan wasan ya faɗi a yayin da yake taka wasan share fagen shiga kakar wasa ta firimiyar Najeriya (NPFL) a ranar Talata. Rahotanni sun ce Ozor ya ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin wasan Katsina United da Niger Tornadoes, inda nan da nan aka garzaya da shi asibiti da ke kusa, sai dai likita ya tabbatar da mutuwarsa tun a lokacin.…
Read More
Masoyin Aliyu Wadada ya raba wa mata injin niƙa a Lafia

Masoyin Aliyu Wadada ya raba wa mata injin niƙa a Lafia

Daga JOHN D. WADA a Lafia Wani matashin ɗan siyasa Abbas Zanwa wanda masoyi ne kuma wakilin yaƙin neman takarar mai neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa na 2027 a Jam'iyyar APC wato Sanata Ahmad Aliyu Wadada daga gundumar Zanwa da ke ƙaramar hukumar Lafia ta Jihar Nasarawa ya raba wa mata injinan niƙa guda 10, domin taimaka musu wajen samun sana’o’in dogaro da kai. Abbas ya bayyana cewa tallafin ya shafi mata ne musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke ƙarƙashin gundumar Zanwa inda yace burinsa shi ne ganin mata sun rungumi sana’o’in dogaro da kai domin rage musu…
Read More
’Yan wasan ƙwallon ƙafa ta Katsina Academy sun tafi Belarus

’Yan wasan ƙwallon ƙafa ta Katsina Academy sun tafi Belarus

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ’Yan wasa takwas daga kwalejin ƙwallon ƙafa na Jihar Katsina sun bar Najeriya zuwa ƙasar Belarus, domin halartar horo a ƙungiyar FC Torpedo Zhodino da ke Minsk. An zaɓi ’yan wasan ne a gasar Malam Dikko Raɗɗa Scouting Tournament da ta gudana a Katsina. Shugaban kwalejin, Ahmed Mohammed, ya ce Gwamna Dikko Raɗɗa ya shirya gasar ne domin gano tare da bunƙasa ƙwararrun matasan ’yan wasan ƙwallon ƙafa daga ƙananan hukumomi 34 na jihar. Ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin ’yan wasan su samu kwangilar ƙwararru da FC Torpedo Zhodino-Belaz bayan kammala horon. Ya…
Read More