ukarofi

12500 Posts
Musa Funtua ya ƙaddamar da ƙungiyar Gwagware Continuity a Katsina

Musa Funtua ya ƙaddamar da ƙungiyar Gwagware Continuity a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina,Hon Musa Adamu Funtua,ya ƙaddamar da ƙungiyar a garin Funtua sa mai suna Gwagware Continuity dan samun nasarar zaɓen 2027. Hon Musa Adamu ya bayyana mutanen da suka samar da ƙungiyar a matsayin mutane masu mutunci da kima ga al'ummar Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya, dan haka babu ko shakka akwai gagarimar nasara a wannan tafiya ta samun nasara ga 'yan takarar jamiyyar APC tunda sama har ƙasa, nji Hon Musa Adamu Funtua. Kwamishinan mai riƙe da sarautar Ɗan Kafin Katsina,ya kuma tabbatar da cewa,daga yau wannan ƙungiyar babu…
Read More
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Katsina United ya mutu

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Katsina United ya mutu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ozah Chinedu ɗan wasan ƙwallon kafa na ƙungiyar Katsina United ya rasu a yayin da yake buga wasan sada zumunta tsakanin ƙungiyar sa da ta Niger Tornadoes a filing wasa na Muhammadu Dikko a Katsina. Dan wasan wanda tsohon ɗan wasan Kano Pillars ne kafin zuwan sa Katsina United ya gamu da ajalinsa a yayin da ana tsaka da wasa inda aka ga ya faɗi ƙasa. Sanarwa daga sashin hulɗa da jama'a ƙungiyar Katsina United ta bayyana cewar an yi gaggawar kai shi asibitin ƙwararru na K_Dara a Katsina amma daga baya ya rasu. Mutuwar…
Read More
Zuwa ga masu shirin aure (I)

Zuwa ga masu shirin aure (I)

A yau zan yi wasiƙa ne a kan zaɓin ma'aurata, domin shi ne babban abin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya a halin yanzu. Wanda kuma hakan ke jawo yawan mace-macen aure, domin ana auren ne kawai barkatai ba tare da sanin wa ya kamata a aura ba. Babban hadafin da ya ke sanya mu zaɓar wanda zamu rayuwa da shi ko wacce zamu rayu da ita a matsayin rayuwar aure shi ne samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan zaman rayuwar tare ya kasance…
Read More
Mutum 1,932 aka kashe cikin wata uku a Arewa maso Gabas – Majalisar Dinkin Duniya

Mutum 1,932 aka kashe cikin wata uku a Arewa maso Gabas – Majalisar Dinkin Duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Daidaita Ayyukan Agaji (OCHA) ta bayyana cewa aƙalla mutum 1,932 ne suka rasa rayukansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2026, sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Rahoton, wanda ya fito a ƙarƙashin Binciken Hanyar Isar da Agaji na Farkon Shekarar 2026, ya nuna cewa rashin tsaro, hare-hare kan ma'aikatan agaji da kayayyakinsu, cikas na hukumomi da kuma matsanancin yanayin muhalli ne suka fi kawo tsaiko ga ayyukan jinƙai a yankin. Rahoton ya samo bayanansa ne daga ƙungiyar Aiki Kan Hanyar Isar da…
Read More
Malam Ibrahim Shekarau: Goga ka san hanya

Malam Ibrahim Shekarau: Goga ka san hanya

Daga BIKISU YUSUF ALI Me ya sa wasu ke ganin gogaggen ɗan siyasa ne ya dace da Majalisar Dattawa? Nazari ta fuskar Malam Ibrahim Shekarau Majalisar Dattawa ce babbar Majalisar Dokoki ta Nijeriya mai wakiltar mazabun sanatoci 109. Babbar aikinta ita ce kirƙirar dokoki, sa ido kan ayyukan gwamnati, wakiltar muradun al'umma da kuma tantance wasu muƙaman gwamnati kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada. Saboda muhimmancin wannan majalisa, masu nazarin siyasa sukan yi la'akari da gogewa ta ilimi da tarihin shugabanci lokacin nazarin cancantar 'yan takara.Haka ana bukatar mai baki da kishi da iya magana cikin mutane da…
Read More
Rarara annoba ne ga Kano da Arewa?

Rarara annoba ne ga Kano da Arewa?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ A baya, ban taba bata lokaci don yin rubutu game da Rarara ba, amma a wannan lokaci ya zama wajibi ga duk mai kishin Arewa da Musulmi ya yi Allah wadai da irin halayya da wakokin Rarara. Komai kiyayyarka da Rarara dole ka sallama wajen yarda da cewa hakika Allah ya ba shi ni'ima ta basirar waka. Ita kuma waka, ko su mawaka, Allah ya sanar da mu cikin suratul Shu'ara cewa kashi biyu ne: Q22:226 "Kuma mawãƙa, halakakku ne ke bin su. Shin, ba ku ga cewa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin…
Read More
Abokan Mujaddadi allo da tawada

Abokan Mujaddadi allo da tawada

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Har Shehu Usmanu Danfodiyo ya koma ga Allah a shekaru 63 bai samu zarafin yin hajji ba don sadaukar da kansa kakaf ga koyarwa. Kama daga ƙofar gidansa, masallaci har duk inda ya nufa a cikin jama’arsa. Hatta kaninsa Sheikh Abdullahi Gwandu ya yi yunƙurin tafiya aikin hajji amma kanawa su ka dakatar da shi don ya koya mu su addini. Gaba ɗaya rayuwar Shehu Mujaddadi a hidimar karatu, karantarwa da wayar da kan al’umma ne kan dokokin addinin Musulunci na ƙarfafa gaskiya da amana da tarbiyya. Wannan ya sa ba a samun ko rabin sa’a…
Read More
Nazari kan matsalolin noma a daminar bana

Nazari kan matsalolin noma a daminar bana

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Wani rahoto da jaridar Manhaja Blueprint ta wallafa game da matsalolin da manoma ke fuskanta a daminar bana, dangane da ƙalubalen noma da tsadar abinci ya ja hankalina sosai, musamman ganin cewa jama'a da dama na sa ran ganin an samu sauƙin farashin kayan abinci a kasuwanni, saboda yanayin da ake ciki na damina, yayin da manoma a wasu sassan arewacin ƙasar nan suka fara fitar da kayan gona zuwa kasuwanni.  Rahoton ya naaalto Babban Sakataren ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), Femi Oke, yana bayyana cewa, har kawo yanzu ana cigaba da samun hauhawar farashin kayayyakin…
Read More
Lakurawa sun kashe soja da ‘yan sa kai biyu a Kebbi

Lakurawa sun kashe soja da ‘yan sa kai biyu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga ƙaramar hukumar Dandi sun bayyana cewa wani soja da 'yan sa kai biyu sun rasa ran su a wani artabu tsakanin su da lakurawa jiya a ƙauyen Tashar Jiba da ke kan hanyar Kamba zuwa Kangiwa. Wani mazauni garin Kamba Malam Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa bayan samun labarin lakurawa sun kai hari a ƙauyen ne sai sojojin da 'yan sa kai da ke aiki a wannan yankin suka isa inda suka fafata da su wanda a nan ne aka ce an yi wa jami'an kwanton ɓauna aka harbe su. Ya ce duk…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da shirin horas da malamai 250 a Gusau

Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da shirin horas da malamai 250 a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara a yau Litinin ta ƙaddamar da shirin juyin juya hali na malamai na matsayin duniya (GSTTP), wani babban shiri na gina ƙarfi da za a horas da malamai 250, jami’an tabbatar da ingancin, da kuma masu gudanar da harkokin ilimi a faɗin jihar. Kwamishinan ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha, Hon. Abdulmalik Gajam, wanda Babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Maryam Yahaya Shantali, ta wakilta ta ƙaddamar da horon a kwalejin fasaha da kimiyya ta Zamfara, ZACAS, da ke Gusau. Ta bayyana horon a matsayin mataki mai muhimmanci a tafiyar haɗin gwiwa wajen sauya ilimi…
Read More