ukarofi

12500 Posts
Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu a Katsina

Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon babban sakatare kuma raya karkaran Katsina, Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya a Katsina. Ɗanmalam Karofi wanda aka fi sani da ADK shi ke kula da ƙananan hukumomin jihar a lokacin Marigayi Umaru Musa Yar'adua na gwamnan jihar. Marigayi ADK za a riƙa tunawa da shi wajen jajircewa na ganin shugabannin ƙananan hukumomi dole su gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da mulkin ƙananan hukumomin jihar. Haka kuma an bayyana Karofi a matsayin mai gaskiya da jajircewa wajen ganin shugabannin ƙananan hukumomi sun sarrafa kason kuɗaɗen su…
Read More
Gambo Sawaba: Matar da ta biya kuɗin ‘yancin matan Arewa da jikinta

Gambo Sawaba: Matar da ta biya kuɗin ‘yancin matan Arewa da jikinta

"Tun tana ƙaramar idan ana zaluntar wani yaro, takan shiga tsakani tana faɗin ta ɗauki faɗan a kanta" Daga AISHA ASAS A duk lokacin da ake magana kan gwagwarmayar mata a Arewacin Najeriya, akan ambaci sunaye da dama. Amma akwai suna guda da ya tsaya daban, saboda ba a gina shi da mulki ko arziki ba, sai da sadaukarwa, ƙalubale da kuma jajircewar da ba ta san ja da baya ba. Wannan suna shi ne na Hajiya Gambo Sawaba. A wani zamani da aka ɗauki siyasa a matsayin fagen maza, kuma aka ɗora wa mata nauyin zama masu sauraro kawai,…
Read More
Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron zuba jari na Kanada-Afirka

Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron zuba jari na Kanada-Afirka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnoni da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa za su wakilci Nijeriya a taron ƙoli na Kanada-Afirka kan hanyoyin zamani na tattalin arziki da za a gudanar a Toronto kamar yadda sanarwar ta fito daga mai magana da yawun gwaman Sulaiman Bala Idris. Taron zuba jari na farko na irin sa zai gudana ne daga ranar 10 zuwa 15 ga Agusta, 2026, a birnin Toronto na ƙasar Kanada. A cikin wasiƙar gayyatar da fadar shugaban ƙasa ta aika wa gwamna Lawal, an bayyana cewa kasancewarsa cikin manyan mahalarta taron zai taimaka wajen ƙarfafa…
Read More
Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyar ADC zuwa APC a Katsina

Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyar ADC zuwa APC a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Madugun adawa a Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da dubban magoya bayansa sun fice daga ADC sun koma APC. Mustapha Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina dama can ɗan jam'iyar APC amma tun da jam'iyar ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takara gwamna, da Dikko Raɗɗa ya kada shi ya bar jam'iyar. Bayan wani lokaci sai madugun adawar ya koma jam'iyar PDP nan ma ya fice bayan ya sami saɓani da Sanata Yakubu Lado Danmarke. Daga nan ya koma ADC inda ya zama jagorar jam'iyar a Jihar kafin shigar shi APC. Sauyin ya jawo…
Read More
An yi kira ga ‘yan siyasa a Katsina su guji cin mutuncin juna a yaƙin neman zaɓe

An yi kira ga ‘yan siyasa a Katsina su guji cin mutuncin juna a yaƙin neman zaɓe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An yi kira ga 'yan siyasa a Jihar Katsina da su guji cin mutuncin junan su gabanin fara yaƙin neman zaɓe na 2027. Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua,Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira a Katsina a wata hira da manema labarai. Kwamred Suleiman ya nuna damuwarsa a yadda kwanaki kaɗan masu zuwa za a fara fita yaƙin neman zabe amma har an fara fitowa kafafen sadarwa ana musayar yawu wanda haka ka iya kawo rigingimu a tsakin su. Yakamata 'yan siyasa su san cewa duk wannan yunƙuri da suke yi kan neman kujerar mulki, domin…
Read More
Ya jefa ’ya’yansa biyu daga bene mai hawa uku a Aba

Ya jefa ’ya’yansa biyu daga bene mai hawa uku a Aba

Wasu yara biyu sun jikkata bayan da mahaifinsu ya jefa su daga saman wani bene mai hawa uku a unguwar Umuobe da ke kusa da Babban Garin Aba, a Jihar Abia. Rahotanni sun ce mutumin, mai kimanin shekara 40 a duniya, ya aikata hakan ne saboda wani dalili da har yanzu ba a bayyana ba. Bayan jefa yaran, shi ma ya yi tsalle daga saman wannan bene, bayan da ake zargin ya yi barazanar cutar da matarsa. Ko da yake yaran sun tsallake rijiya da baya, sun samu raunuka daban-daban sakamakon faɗuwar. Mazauna yankin, da suka fito bayan jin kukan…
Read More
An kama mai aski bisa zargin amfani da gashin mutane don yin tsafi

An kama mai aski bisa zargin amfani da gashin mutane don yin tsafi

An kama wani mai aski mai suna Emeka a garin Umuahia, babban birnin Jihar Abia, bayan da jami'an Rundunar 'Yan Sandan Jihar Abia suka gano wata tukunya da ke cike da gashin mutane a cikin ɗakinsa. Rahotanni sun ce Emeka ya yi suna a Umuahia saboda ƙwarewarsa wajen aski, sai dai an cafke shi ne a ranar Talata bayan maƙwabcinsa, Johnson Ikenga, ya kai ƙorafi ga 'yan sanda yana zargin mai askin da yi masa barazana. A yayin da jami'an 'yan sanda suka kai samame gidan wanda ake zargin domin bincike, sun gano wata tukunya mai ɗauke da gashin mutane…
Read More
Ya damfari jagoran ’yan bindiga miliyan N95 da sunan sayo masa makamai a Katsina

Ya damfari jagoran ’yan bindiga miliyan N95 da sunan sayo masa makamai a Katsina

Wani mutum da ake zargin yana safarar makamai ya ɓace ɓat bayan karɓar Naira miliyan 95 daga hannun wani fitaccen jagoran ’yan bindiga a Jihar Katsina, da sunan zai saya masa manyan makamai. Rahotanni sun ce zargin ya fito ne daga ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Musawa/Matazu, Abdullahi Aliyu, wanda aka fi sani da Janar, yayin wata hira da ya yi da NTA Hausa. A cewarsa, mutumin ya karɓi kuɗin ne daga wani shugaban ’yan bindiga da ke aiki a ƙaramar hukumar Matazu, bayan ya yi masa alƙawarin samar masa da manyan makamai. Sai dai bayan karɓar kuɗin, ana…
Read More
PTDF ta buƙaci ’yan jarida su riƙa bayar da sahihan rahotanni kan fannin mai da gas

PTDF ta buƙaci ’yan jarida su riƙa bayar da sahihan rahotanni kan fannin mai da gas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Asusun Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ya buƙaci 'yan jarida su riƙa wallafa sahihan rahotanni masu cike da gaskiya kan harkokin mai da iskar gas a Nijeriya, yayin da ya kammala wani shirin horaswa da aka gudanar a Legas domin ƙara wa ƙwararrun kafafen yaɗa labarai ilimi kan yadda ake ba da rahoto a wannan muhimmin fanni. Shirin horaswar ya samu halartar kusan 'yan jarida 50 da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, inda aka koya musu dabarun fahimtar fannoni na fasaha da manufofin da suka shafi masana'antar mai da iskar gas, tare da…
Read More
Ku yi amfani da ɗimbin damar kasuwancin Nijeriya – Shettima ga Saudiyya

Ku yi amfani da ɗimbin damar kasuwancin Nijeriya – Shettima ga Saudiyya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga masu zuba jari daga ƙasar Saudiyya da su yi amfani da ɗimbin damar kasuwanci da ke Nijeriya, yana mai tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya ta samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali. Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe baje kolin zuba jari da yawon buɗe ido na Nijeriya da Saudiyya na kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja. Kamfanin Al-Yaro International Limited ne ya shirya taron tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yan Nijeriya…
Read More