09
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga masu zuba jari daga ƙasar Saudiyya da su yi amfani da ɗimbin damar kasuwanci da ke Nijeriya, yana mai tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya ta samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali. Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe baje kolin zuba jari da yawon buɗe ido na Nijeriya da Saudiyya na kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja. Kamfanin Al-Yaro International Limited ne ya shirya taron tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yan Nijeriya…
