09
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar ya bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a shekarar 2025, idan aka kwatanta da kashi 3.38 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2024. Hakan na ƙunshe ne cikin Rahoton Shekara na 2025 da bankin ya wallafa, inda ya danganta wannan ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki a muhimman fannoni, tare da sake fasalin tsarin ƙididdigar tattalin arzikin ƙasar domin haɗa sabbin sassan da suka fara taka rawa. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 15.15 cikin…
